KA SANI?
Wane ’yanci ne manzo Bulus ya samu domin ya zama ɗan kasar Roma?
Zama ɗan kasar Roma yana ba mutum ’yanci da kuma zarafi da yawa a kowane wuri da ya shiga a cikin daular. Duk mutumin da ke da ’yancin zama ɗan kasar Roma yana karkashin dokar kasar ne ba na biranen da ke kasar ba. Sa’ad da aka tuhume shi da aikata laifi, za a iya shari’anta shi a birnin, amma yana da ’yancin ɗaukaka kara zuwa babban kotun kasar. Idan kuma an yanke masa hukuncin kisa, zai iya ɗaukaka karar zuwa wajen sarkin kasar.
Irin wannan ’yancin ne ya sa wani ɗan siyasa a karni na farko kafin haihuwar Yesu, mai suna Cicero ya ce: “Kama ɗan kasar Roma laifi ne; yi masa duka mugunta ne; kashe shi kuma ɗaya ne da wani ya kashe mahaifinsa ko mahaifiyarsa ko kuma wani danginsa.”
Manzo Bulus ya yi wa’azi sosai a Daular Roma. Ya yi amfani da ’yancinsa na ɗan kasar Roma a hanyoyi uku: (1) Ya gaya wa alkalan Filibi cewa sun taka ’yancinsa ta wajen yi masa duka. (2) Sa’ad da yake Urushalima, ya faɗi cewa shi ɗan kasar Roma ne domin kada a doke shi. (3) Ya ɗaukaka kararsa zuwa gaban Kaisar, wanda shi ne sarkin Roma, domin ya yanke hukuncin da kansa.—Ayyukan Manzanni 16:37-39; 22:25-28; 25:10-12.
Ta yaya ake biyan makiyaya a zamanin dā?
Yakubu uban iyali ya yi kiwon garken kawunsa Laban shekara 20. Yakubu ya fara yi wa Laban aiki na shekara 14 domin ya ba shi ’ya’yansa biyu ya aura, bayan haka, sai ya yi aiki na shekara 6 domin ya sami tumaki. (Farawa 30:25-33) Littafin nan Biblical Archaeology Review ya ce: “Marubuta a zamanin dā da kuma waɗanda suka karanta Littafi Mai Tsarki sun san da irin wannan yarjejeniyar, kamar wanda Yakubu da Laban suka yi.”
Duwatsun da aka rubuta kwangila a zamanin dā da aka tono a birnin Nuzi da Larsa da kuma wasu wurare a kasar Iraki sun nuna irin wannan yarjejeniyar. A irin wannan kwangilar, ana rarraba tumaki kowace shekara. Makiyaya suna karɓan rikon tumaki kuma ana rubuta adadinsu da shekarunsu da kuma jinsinsu. Bayan shekara guda, mai tumakin yana karɓan ulu da madara da kindirmo da kuma kananan tumaki da dai sauransu. Duk karin da aka samu na makiyayin ne.
Karuwar da aka samu ya dangana ga adadin tunkiyar da aka ba makiyayin. Ana sa rai cewa tunkiya ɗari za su haifi ’ya’ya 80. Makiyayin zai biya idan wani tunkiya ko rago ya ɓace. Saboda haka, yana bukata ya kula da dabbar da yake kiwo.