Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 9/1 p. 9
  • Ka Sani?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sani?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Makamantan Littattafai
  • Taimaka wa ’Yan’uwan Kristi da Aminci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Mai Sāka wa Dukan Waɗanda Suke Bauta Masa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 9/1 p. 9

KA SANI?

Kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki, mene ne kalmar nan bāba take nufi?

A wasu lokuta, ana amfani da kalmar nan bāba don a kwatanta namijin da aka yi masa dandake. A dā, an yi wa wasu maza dandake don sun yi wani laifi ko bayan an ci su a yaki ko kuma sa’ad da suka zama bayi. Ana amfani da mazan da aka yi musu dandake wajen gadin matan sarki ko kuma wani attajiri. Alal misali, bāba Hegai da Sha’ashgaz sun yi aiki ne a matsayin masu gadin matan Sarki Ahasurus ko kuma Xerxes na Ɗaya.—Esther 2:3, 14.

Amma ba dukan waɗanda Littafi Mai Tsarki ya kira su bāba ne aka yi musu dandake ba. Wasu masana sun ce kalmar tana da manufa da yawa, tana iya nufin wani babban ma’aikaci a fadar sarki. Watakila abin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce da Ebed-melech, abokin aikin Irmiya bāba kuma ya ce da wani Bahabashe wanda Filibus ya yi ma wa’azi ma hakan. Ebed-melech babban ma’aikacin sarki ne don yana da ’yancin zuwa wurin Sarki Zedekiya. (Irmiya 38:7, 8) Kuma an kwatanta Bahabashen a matsayin ma’ajin sarauniya da ya je “Urushalima . . . garin yin sujada.”—Ayyukan Manzanni 8:27.

Me ya sa makiyaya a zamanin dā suke ware tumaki daga awaki?

Sa’ad da Yesu yake kwatanta hukuncin da za a yi a nan gaba, ya ce: ‘Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukaka tasa . . . zai kuma ware mutane dabam-dabam, kamar yadda makiyayi ke ware tumaki da awaki.’ (Matta 25:​31, 32, Littafi Mai Tsarki) Me ya sa makiyaya suke ware tumaki daga awaki?

Ana yawan yin kiwon awaki da tumaki tare da rana. Amma daddare, ana shinge su saboda namomin daji ko ɓarayi ko kuma sanyi. (Farawa 30:​32, 33; 31:​38-40) Ana ware tumaki daga awaki domin kada awakin su ji wa tunkiya ko kuma ’ya’yansu rauni. Littafin nan All Things in the Bible ya ce: “Makiyaya suna kuma ware tumaki daga awaki sa’ad da suke tatse nono da yanke gashinsu da kuma sa’ad da suka haihu.” Saboda haka, kwatancin Yesu sananne ne ga masu sauraronsa da ke zama a wuraren da ake kiwo kamar a kasar Isra’la ta dā.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba