Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 9/15 p. 22
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu​—⁠Satumba 2014

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu​—⁠Satumba 2014
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • “Masu Neman Sanin Jehobah Ba Za Su Rasa Abu Mai Kyau Ba”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Jehobah—“Mai-ceto” Ne A Zamanin Da Aka Rubuta Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • ‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Dogara Ga Ruhun Allah Sa’ad Da Kake Fuskantar Canji A Yanayin Rayuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 9/15 p. 22

AMSOSHIN TAMBAYOYIN MASU KARATU

Shin abin da Dauda ya faɗa a Zabura 37:25 da kuma furucin Yesu da ke Matta 6:33 suna nufin cewa Jehobah ba zai bari Kirista ya yi rashin isashen abinci ba ne?

Dauda ya rubuta cewa bai “taɓa gani an yar da mai-adalci ba, ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu.” Ya yi wannan maganar bisa abubuwan da ya shaida a rayuwarsa. Yana da tabbaci cewa Allah yana kula da bayinsa a kullum. (Zab. 37:25) Amma, furucin Dauda ba ya nufin cewa babu bawan Allah da ya taɓa rashin abin biyan bukata ko kuma babu wanda zai taɓa yin hakan.

Akwai lokatan da Dauda da kansa ya fuskanci mawuyacin hali. Misali ɗaya shi ne a lokacin da yake tsere wa sarki Saul. Abincin Dauda ya ƙare kuma hakan ya sa ya roƙi gurasa don shi da mutanensa su ci. (1 Sam. 21:1-6) Saboda haka, a wannan lokacin Dauda ya yi ‘roƙon abinci.’ Duk da haka, a wannan mawuyacin halin, Dauda ya tabbata cewa Jehobah bai yashe shi ba. Hakika, babu wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa Dauda ya yi roƙon abinci don ya rayu.

A littafin Matta 6:33, Yesu ya ba da tabbaci cewa Allah zai biya bukatun bayinsa masu aminci idan suka saka al’amuran Mulkin farko a rayuwarsu. Yesu ya ce: “Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa [sun haɗa da abinci da abin sha da kuma tufafi] za a ƙara maku su.” Amma Yesu ya ce ‘’yan’uwansa’ za su fuskanci rashin abinci saboda tsanantawa da za su fuskanta. (Mat. 25:35, 37, 40) Hakan ya taɓa faruwa da manzo Bulus. A wasu lokatai ya taɓa rashin abinci da kuma ruwan sha.—2 Kor. 11:27.

Jehobah ya gaya mana cewa za a tsananta mana a hanyoyi dabam-dabam. Zai iya bari mu fuskanci yanayi na ƙarancin abinci don ya ba da amsa ga zargin da Shaiɗan ya yi. (Ayu. 2:3-5) Alal misali, wasu ’yan’uwanmu Kirista kamar waɗanda aka saka a sansanin Nazi sun fuskanci wani yanayi mai wuya saboda tsanantawa. Wata muguwar dabara da aka yi amfani da ita don a sa ’yan’uwanmu su yi rashin aminci ita ce hana su abinci. Shaidu masu aminci sun yi biyayya ga Jehobah kuma bai yashe su ba. Ya bari sun fuskanci tsanantawa, kamar yadda yake barin dukan Kiristoci su fuskanci matsaloli dabam-dabam. Amma, muna da tabbaci cewa Jehobah yana taimaka wa dukan bayinsa da suke shan wuya saboda sunansa su jimre. (1 Kor. 10:13) Kada mu manta da abin da aka rubuta a Filibiyawa 1:29 cewa: “A gare ku an bayar sabili da Kristi, ba ba da gaskiya gare shi kaɗai ba, amma shan wahala kuma dominsa.”

Jehobah ya yi alkawari cewa zai kasance tare da bayinsa. Alal misali, an rubuta a littafin Ishaya cewa: ‘Ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ku.’ (Isha. 54:17, Littafi Mai Tsarki) Wannan alkawarin da kuma wasu irinsa sun tabbatar mana cewa Allah zai kāre bayinsa a matsayin rukuni. Amma kowane Kirista zai iya fuskantar gwaji, har ma ya kai ga mutuwa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba