Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 9/1 pp. 14-15
  • Na Yi Yaƙi da Rashin Adalci da Kuma Mugunta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Na Yi Yaƙi da Rashin Adalci da Kuma Mugunta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • “Ina Son Fada Sosai”
    Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • Taimakon Mutane Iri-Iri a Netherlands
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Dā Ni Mugu Ne da Kuma Mai Son Yin Fada
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 9/1 pp. 14-15

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Na Yi Yaƙi da Rashin Adalci da Kuma Mugunta

Antoine Touma ne ya ba da labarin

  • SHEKARAR HAIHUWA: 1960

  • ƘASAR HAIHUWA: LABANAN

  • TARIHI: ƘWARARREN ƊAN DAMBEN KUNG FU

RAYUWATA A DĀ:

Na yi girma a birnin Rmaysh, kusa da iyakar ƙasar Isra’ila da Labanan, a lokacin da ake yaƙin basasa. Har yanzu ina tune da tashin bama-bamai da mutane da suka rasa ƙafafunsu da kuma hannayensu sanadin yaƙin. Rayuwa ta yi wuya kuma aikata laifi da mugunta suka zama gama-gari.

Iyalinmu ’yan Cocin Maronite ne, wato ɗaya daga cikin coci-cocin da Cocin Katolika na Gabas ya yaye. Mu 12 ne a iyalinmu, kuma mahaifina ya yi ƙoƙari sosai wajen ciyar da mu, amma mahaifiyarmu ta tabbata cewa mun je coci. A kwana a tashi, na lura cewa babu wani bambanci tsakanin mabiya coci da sauran mutane domin dukansu sun kasa taimakon marasa ƙarfi.

Na soma sha’awar damben kung fu a lokacin da nake tsakanin shekara 13 zuwa 19. An horar da ni sosai kuma na ƙware a yin naushi da yin harbi da ƙafa da kuma yin amfani da wasu kayayyakin faɗa. Na gaya wa kaina cewa, ‘Na san ba zan iya hana yaƙin ba, amma zan yi ƙoƙari in hana mutane yin mugunta.’ A duk lokacin da na ga mutane biyu suna faɗa, nakan sa baki nan da nan. Ni mai saurin fushi ne, saboda haka, ƙaramin abu ne yake ɓata mini rai. Mazauna kudancin Labanan suna tsoro na, domin ina yaƙar rashin adalci da kuma mugunta da kaina.

A shekara ta 1980, na shiga wata ƙungiyar ’yan damben kung fu a birnin Beirut. Ko da yake ana ruwan bama-bamai da kuma makaman roka kowace rana, ban fasa zuwa wurin da nake koyan dambe ba. A duk rayuwata, abin da na sa a gaba shi ne cin abinci da kwanciya da kuma yin kwaikwayon Bruce Lee, wani ɗan ƙasar Caina da aka haife shi a Amirka wanda ƙwararren ɗan fim ne da kuma damben kung fu. Na bar suma kamar nasa kuma na kwaikwayi salon tafiyarsa da kuma yadda yake ihu sa’ad da yake damben kung fu. Ƙari ga haka, ba na dariya.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Burina shi ne in zama ƙwararren ɗan damben kung fu a ƙasar Caina. Wata rana da yamma sa’ad da nake horar da kaina don zuwa Caina, sai na ji an ƙwanƙwasa mini kofa. Ashe wani abokina ne tare da wasu Shaidun Jehobah guda biyu. Sun tarar da ni sanye da baƙin tufafin dambe kuma na jiku sharaf da zufa. A tattaunawarmu na gaya musu cewa, “Ban san kome a Littafi Mai Tsarki ba.” Ban san cewa daga wannan lokacin rayuwata za ta ɗauki wani salo dabam ba.

Shaidun sun nuna mini a Littafi Mai Tsarki dalilin da ya sa ’yan Adam ba za su iya kawo ƙarshen rashin adalci da mugunta ba. Sun bayyana cewa Shaiɗan Iblis ne ainihin sanadin matsalolin nan. (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Irin zaman lafiya da gaba gaɗin da Shaidun suke da shi ya burge ni. Sanin cewa Allah yana da suna ya ratsa zuciyata sosai. (Zabura 83:18) Sun nuna mini littafin 1 Timotawus 4:8, wanda ya ce: “Wasa jiki tana da amfaninta kaɗan: amma ibada tana da amfani ga dukan abu, da shi ke tana da alkawari ga rai na yanzu, da na mai-zuwa.” Kalmomin nan sun yi tasiri a rayuwata sosai.

Abin baƙin ciki fa, ban sake ganin Shaidun ba domin iyalina sun hana su dawowa. Duk da haka, na ƙuduri niyyar soma nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma daina damben kung fu. ’Yan’uwana maza ba su ji daɗin wannan matakin da na ɗauka ba, amma a zuciyata, na ƙudurta cewa zan nemi Shaidun Jehobah don su soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.

Na ci gaba da neman Shaidun amma ban gan su ba. A kwana a tashi, sai farat ɗaya mahaifina ya rasu kuma wasu masifu suka faɗo wa iyalina. Na yi baƙin ciki sosai. Zuwa lokacin, ina aiki da kamfanin gine-gine sai wani abokin aikina mai suna Adel ya tare ni wata rana kuma ya tambaye ni dalilin da ya sa nake baƙin ciki haka. Ya yi mini bayani a kan begen tashin matattu daga Littafi Mai Tsarki. Wannan Mashaidi mai kirki ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni cikin haƙuri, har tsawon wata tara.

Yayin da nazarin yake ci gaba, na gane cewa ina bukata in canja halina. Hakan bai yi mini sauƙi ba. Ni mutumi ne mai saurin fushi, kuma abu kaɗan yana tayar mini da hankali. Amma Littafi Mai Tsarki ya koya mini yadda zan riƙa kame kaina maimakon yin fushi. Alal misali, Matta 5:44 yana ɗauke da shawarar Yesu cewa: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a.” Kuma Romawa 12:19 ya ce: “Kada ku ɗauka wa kanku fansa, . . . gama an rubuta, Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.” A hankali waɗannan nassosin da kuma wasu sun taimaka mini in kame kaina.

YADDA NA AMFANA:

A farko dai, iyalina sun yi hamayya da ni saboda matakin da na ɗauka na yin nazari da Shaidun Jehobah, amma a yanzu haka, suna daraja Shaidu sosai. Ƙanina yana bauta wa Jehobah, kuma har mutuwar mahaifiyarmu, ta kāre imaninmu a gaban mutane.

Ƙari ga haka, na auri mace mai kirki da kuma aminci mai suna Anita, wadda muke fita wa’azi tare a kowane lokaci a matsayin majagaba na kullum. Tun shekara ta 2000, Ni da Anita mun ƙaura zuwa birnin Eskilstuna a Sweden don mu koyar da Littafi Mai Tsarki ga Larabawa.

Har yanzu, ina tausaya ma waɗanda wulaƙantawa. Amma sanin ainihin sanadinsa da kuma sanin cewa ba da daɗewa ba Allah zai kawar da shi, yana ba ni farin ciki da kuma kwanciyar rai.—Zabura 37:29.

Ni da matata muna jin daɗin wa’azi sosai da kuma koyar da mutane game da Jehobah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba