Allah Zai Iya Ƙarfafa ka
“Shi wanda yake yi ma masu-tawali’u ta’aziya, wato Allah, ya yi mana ta’aziya.”—2 KORINTIYAWA 7:6.
ABIN DA KE SA WASU SHAKKA: Sa’ad da wasu suke bukatar ƙarfafa da taimako, ba sa roƙon Allah ya taimake su domin suna ganin yin hakan son kai ne. Wata mata mai suna Raquel ta ce: “Idan na yi tunani a kan ɗimbin mutanen da ke duniya da kuma matsaloli masu wuya da suke fuskanta, sai in ga kamar nawa matsalar ba wani abu ba ne, kuma hakan na sa in yi jinkirin roƙon Allah ya taimake ni.”
ABIN DA KALMAR ALLAH TA CE: Allah ya riga ya ɗauki wani babban matakin taimaka wa mutane da kuma ƙarfafa su. Kowane ɗan Adam ya gāji zunubi, wanda ke hana mu bin mizanan Allah sau da kafa. Amma, Allah “ya ƙaunace mu, ya aike Ɗansa [Yesu Kristi] kuma ya biya hakin zunubanmu.” (1 Yohanna 4:10) Ta wajen mutuwar fansa da Yesu ya yi, Allah ya ba mu damar samun gafara da lamiri mai kyau da kuma begen rai na har abada a cikin sabuwar duniya, inda salama za ta kasance.a Amma shin wannan fansar kyauta ce ga ’yan Adam gaba ɗaya, ko kuma tabbaci ne cewa Allah ya damu da kai?
Ka yi la’akari da misalin manzo Bulus. Hadayar Yesu ta ratsa zuciyarsa sosai har ya rubuta cewa: ‘Ina rayuwa cikin bangaskiya, bangaskiya wanda ta ke cikin ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, ya ba da kansa kuma domina.’ (Galatiyawa 2:20) Yesu ya mutu tun kafin Bulus ya zama Kirista. Duk da haka, Bulus ya ɗauki hadayar Yesu a matsayin kyauta da Allah ya yi masa.
Mutuwar fansa ta Yesu kyauta ce da Allah ya yi maka. Wannan kyautar tabbaci ne cewa kana da tamani sosai a gaban Allah, kuma za ta iya sa ka sami “ta’aziya madawwamiya” da kuma “nagarin bege.” Hakan zai ‘ƙarfafa ka cikin kowane kyakkyawan aiki da zance.’—2 Tasalonikawa 2:16, 17.
Yanzu an yi kusan shekaru 2,000 da Yesu ya sadaukar da ransa. Shin, me ya nuna cewa Allah yana so ya ƙulla dangantaka da kai a yau?
a Don ka daɗa koya game da hadayar Yesu, ka duba babi na 5 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.