Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 9/1 p. 3
  • Munanan Abubuwa Sun Yawaita!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Munanan Abubuwa Sun Yawaita!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Don Me Masifu Suke Faɗa wa Mutanen Kirki?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Allah ne Ya Sa Muke Shan Wahala?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Wane ne Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Sashe na 1—Allah Yana Kula Da Mu Kuwa Da Gaske?
    Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 9/1 p. 3

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | DON ME MASIFU SUKE FAƊA WA MUTANEN KIRKI?

Munanan Abubuwa Sun Yawaita!

Smitaa ’yar shekara 35 ce da aka san ta da halin kula da mutane, kuma tana da zama a birnin Dhaka a Bangladesh. An san ta a matsayin mace mai ƙwazo da fara’a da kuma son koya wa mutane abubuwa game da Allah. Hakika, iyalinta da kuma abokanta sun yi baƙin ciki sosai sa’ad da ta kamu da wata mummunar cuta kuma ta rasu cikin mako ɗaya.

James da matarsa, ’yan shekara 30 da wani abu, mutanen kirki ne ma kamar Smita. Wata rana, sun kai wa abokansu ziyara a yankin West Coast a Amirka. Amma abin baƙin ciki, ba a sake ganin su ba don sun rasu a wani mummunan hatsari. Hakan ya bar danginsu da abokansu da kuma abokan aikinsu cikin baƙin ciki da kuma kewa.

Ba sai ka je wani wuri dabam kafin ka ga cewa mugunta da wahala sun yawaita a yau ba. Sojoji da farar-hula suna mutuwa a yaƙi. Mutanen da ba su san hawa ko sauka ba suna shan wahala sakamakon aikata laifi da mugunta. Munanan hatsari da cututtuka suna auko wa mutane kome shekarunsu ko kuma matsayinsu. Bala’o’i suna halaka garuruwa babu zaɓi. Wariyar fata da kuma rashin adalci sun zama ruwan dare. Mai yiwuwa ka taɓa fuskantar wasu cikin waɗannan matsalolin.

Saboda haka, mutane sukan yi tambayoyi kamar su:

  • Don me mummunan abu ke faɗa wa mutanen kirki?

  • Allah ne ke da alhakin irin waɗannan abubuwa?

  • Bala’o’i suna faruwa ne haka kawai ko kuma ’yan Adam ne ke jawowa?

  • Shin Karmab ce ke haifar da munanan abubuwa?

  • Idan akwai Allah da ke da iko duka, don me ba ya kāre mutanen kirki daga munanan abubuwa?

  • Zai yiwu mu rabu da mugunta da kuma wahala kuwa?

Kafin mu amsa tambayoyin nan, bari mu ba da amsar tambayar nan: Me ya sa munanan abubuwa suke faruwa, kuma wane mataki ne Allah zai ɗauka?

a An canja sunaye a wannan talifin.

b Kalmar nan Karma wata koyarwar addinin Hindu da kuma Buddha ce, cewa abin da ke faruwa da mutum yanzu sakamakon irin rayuwar da ya yi kafin a sake haifarsa ne.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba