ABIN DA KE SHAFIN FARKO | AKWAI WANDA ZAI IYA SANIN GOBE?
Wasu Sun Cika, Da Yawa Ba Su Cika Ba
Za ka so ka san yadda rayuwarka za ta kasance a nan gaba? Mutane da yawa za su so su san hakan. Mutane da dama sukan faɗi abubuwan da suke ganin za su faru a nan gaba, amma sakamakon yakan bambanta. Ka yi la’akari da waɗannan misalan:
’YAN KIMIYYA suna amfani da na’urori na zamani kuma suna kashe kuɗi mai yawa don su san yadda abubuwa za su kasance a nan gaba. Alal misali, yadda gurɓatawar yanayi za ta shafi duniya da kuma lokacin da za a yi ruwan sama a wasu wurare.
ƘWARARRARUN MANAZARTA suna faɗin yadda suke ganin kasuwanci da siyasa za su kasance nan gaba bayan sun bincika abin da ke faruwa. Wani attajiri mai suna Warren Buffett, wanda ɗaya ne cikin masu arzikin duniya, gwani ne a hangen abin da gobe zai kawo a sha’anin kasuwanci. Hakan ne ya sa aka soma kiransa gogan kasuwanci. Wani manazarci kuma mai suna Nate Silver ya bincika bayanan da aka adana don ya san dukan abubuwan da za su faru a Amirka.
WASU RUBUCE-RUBUCE NA DĀ sun zama annabci ga wasu mutane. Wasu suna ganin kamar abubuwan da Michel de Notredame (Nostradamus), wanda ya wanzu a ƙarni na 16, ya rubuta suna cika a yau. Wasu kuma sun ce za a yi bala’i a ranar 21 ga Disamba, 2012, wadda ita ce rana ta ƙarshe a kalandar mutanen Maya.
SHUGABANNAN ADDINAI sukan annabta aukuwar munanan abubuwa a faɗin duniya don su gargaɗi mutane kuma su sami mabiya da yawa. Harold Camping, wani mai annabcin bala’i tare da mabiyansa sun yi shela cewa duniya za ta halaka a shekara ta 2011. Ga shi kuwa duniya tana nan har wa yau.
HATSABIBAI suna da’awa cewa suna da baiwar sanin abin da zai faru gobe. Edgar Cayce da Jeane Dixon sun yi annabci a kan wasu abubuwa da za su faru a ƙarni na 20, kuma hakan ya faru. Amma, akwai abubuwa da yawa da suka faɗa da ba su faru ba. Alal misali, Dixon ya annabta cewa Yaƙin Duniya na Uku zai ɓarke a shekara ta 1958. Cayce kuma ya annabta cewa birnin New York a Amirka zai lume cikin teku a tsakanin shekara ta 1974 da 1976.
Shin akwai yadda za a iya sanin gobe kuwa? Wannan tambaya ce mai muhimmanci. Idan za ka iya sanin abubuwan da za su faru nan gaba, hakan zai shafi salon rayuwarka da kuma zaɓin da kake yi a yanzu.