Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 4/15 p. 32
  • Ka Sani?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sani?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Me Za Mu Koya Daga Tufafin Firistoci?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 4/15 p. 32

KA SANI?

A zamanin dā, mutane sukan yayyaga tufafinsu. Mene ne manufar hakan?

LITTAFI MAI TSARKI ya ambata misalai da yawa na mutanen da suka yayyaga tufafinsu. Hakan zai iya sa mutane a zamaninmu mamaki, amma Yahudawa suna yin hakan ne domin su nuna cewa suna baƙin ciki ko makoki ko kuma ɓacin rai.

Alal misali, Reuben “ya tsatsage tufafinsa” sa’ad da ya lura cewa ’yan’uwansa sun riga sun sayar da Yusufu duk da ƙoƙarin da ya yi don ya cece shi. Sa’ad da Yakubu mahaifinsu kuma ya yi tsammani cewa namomin daji sun cinye Yusufu, sai “ya tsatsage tufafinsa.” (Far. 37:18-35) Ayuba “ya tsagi rigatasa” sa’ad da aka gaya masa cewa dukan ’ya’yansa sun rasu. (Ayu. 1:18-20) Wani ɗan aike ya zo wurin Eli Babban Firist da “tufafinsa a tsatsage” don ya gaya masa cewa an ci Isra’ilawa a yaƙi kuma an kashe ’ya’yansa biyu, bugu da ƙari, an kwace sunduƙin alkawari. (1 Sam. 4:12-17) Sa’ad da aka karanta wa Josiah Dokokin Jehobah kuma ya fahimci cewa sun yi kuskure, sai “ya yage tufafinsa.”—2 Sar. 22:8-13.

Sa’ad da ake neman a yanka wa Yesu hukunci, Kayafa Babban Firist ya “kekkece tufafinsa,” sa’ad da ya ce Yesu ya yi saɓo. (Mat. 26:59-66) Dokokin da limaman addinan Yahudawa suka kafa sun ce duk mutumin da ya ji an yi saɓo da sunan Allah ya yayyaga tufafinsa. Wani kuma da aka kafa bayan an halaka haikalin Urushalima ta ce “duk mutumin da ya ji an yi saɓo da Sunan Allah ba ya bukatar ya yayyaga tufafinsa, domin idan kowa ya ci gaba da yin hakan, dukan tufafi za su zama tsummokara.”

Idan mutum ya yayyaga tufafinsa, amma baƙin cikin da yake yi na munafunci ne, Jehobah ba ya ɗaukan hakan da muhimmanci. Saboda haka, Jehobah ya gaya wa bayinsa cewa, ‘ku tsaga zukatanku ba tufafinku ba, ku juyo wurina.’—Joel 2:13.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba