Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Waɗanne dalilai ne suka sa Yahudawa na ƙarni na farko suka yi ɗokin zuwan Almasihu?
A zamanin Yohanna Mai Baftisma, jama’a “suna cikin sauraro, mutane duka kuwa suna zato a cikin zukatansu a kan Yohanna, ko wataƙila shi Kristi ne.” (Luk 3:15) Me ya sa Yahudawa suke zato cewa za a haifi Almasihu a lokacin? Akwai dalilai da yawa.
Bayan an haifi Yesu, mala’ikan Jehobah ya bayyana ga makiyaya da suke kiwon tumakinsu a filin Bai’talami. (1) Mala’ikan ya ce: “Yau cikin birnin Dauda an haifa maku Mai-ceto, shi ne Kristi Ubangiji.” (Luk 2:8-11) Bayan haka, sai wasu ‘taron rundunar sama suka kasance tare da mala’ikan, suna yabon Allah, suna cewa,a Alhamdu ga Allah a cikin mafi ɗaukaka, a duniya kuma salama wurin mutanen da ya ke murna da su sarai.’—Luk 2:13, 14.
Babu shakka, wannan sanarwar ta shafi waɗannan makiyaya masu tawali’u sosai. Nan da nan, sai suka je Bai’talami kuma sa’ad da suka ga Yusufu da Maryamu tare da jaririn, wato Yesu, sai suka “ba da labarin batun da aka faɗa musu a kan wannan yaro.” A sakamako, ‘dukan waɗanda suka ji suka yi al’ajabi da al’amuran da aka faɗa masu ta bakin makiyaya.’ (Luk 2:17, 18) Furucin nan “dukan waɗanda suka ji” ya nuna cewa ba Yusufu da Maryamu kaɗai makiyayan suka gaya wa zancen ba. Sa’ad da makiyayan suka koma gida, sun ci gaba da “girmama Allah, suna yabonsa saboda dukan al’amuran da suka ji da suka gani, kamar yadda aka faɗa masu.” (Luk 2:20) Hakika, waɗannan makiyayan ba su ɓoye wannan albishirin ba!
Sa’ad da Maryamu ta kawo ɗanta na fari zuwa haikalin Urushalima kamar yadda Doka ta ce, annabiya Hannatu ta ‘ba da godiya ga Allah, ta yi zancensa kuma ga dukan waɗanda su ke sauraron fansar Urushalima.’ (2) (Luk 2:36-38; Fit. 13:12) Hakan ya sa labarin haihuwar Almasihu ya ci gaba da bazuwa ko’ina.
Daga baya, “waɗansu shehuna daga gabas suka zo Urushalima, suka ce, Ina shi ke wanda an haife shi Sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas, mun zo kuwa domin mu yi masa sujada.” (Mat. 2:1, 2) ‘Sa’ad da Hirudus sarki ya ji wannan, hankalinsa ya tashi, da na dukan Urushalima tare da shi. Sai da ya tattara dukan manyan malamai da marubutan jama’a, kana ya tambaye su wurin da za a haifi Kristi.’ (3) (Mat. 2:3, 4) Hakika, mutane da yawa sun sami labari cewa: An haifi mutumin da zai zama Almasihu!b
Littafin Luka 3:15 da muka yi ƙaulinsa ɗazun ya nuna cewa wasu Yahudawa sun yi tsammani cewa Yohanna Mai Baftisma ne Kristi. Amma, Yohanna ya sa sun daina irin wannan tunanin sa’ad da ya ce: “Shi wanda ke zuwa bayana ya fi ni iko, ko takalmansa ban isa in ɗauke su ba: shi za ya yi maku baftisma da Ruhu Mai-tsarki da wuta kuma.” (Mat. 3:11) Babu shakka, kalaman da Yohanna ya yi cikin tawali’u sun sa Yahudawa sun ta zuba ido don su ga zuwan Almasihu.
Shin Yahudawa a ƙarni na farko sun yi amfani da annabcin bakwai bakwai cikin bakwai da ke littafin Daniyel 9:24-27 don su lissafta lokacin da Almasihu zai bayyana? Ko da yake hakan zai iya yiwu, amma ba mu da tabbaci. A zamanin Yesu, mutane suna da ra’ayi dabam-dabam game da yadda bakwai bakwai cikin bakwai ɗin zai cika, amma babu ko ɗaya cikinsu da ya yi daidai da yadda muka fahimci annabcin a yau.c
Akwai wani addini da ake kiran Essenes wanda mutane da yawa suka ce mabiyansa Yahudawa ne da suke zama a cikin hamada. Waɗannan mutanen sun ce Almasihu biyu za su bayyana kusan ƙarshen shekaru 490. Amma ba mu san ko sun yi lissafinsu da annabcin Daniyel ba. Ko da sun yi amfani da shi, da ƙyar sauran Yahudawa za su gaskata da ra’ayinsu tun da suna zaune a ware daga sauran mutane.
A ƙarni na biyu a zamaninmu, wasu Yahudawa sun gaskata cewa bakwai bakwai cikin bakwai ɗin ya soma a shekara ta 607 kafin zamaninmu, sa’ad da aka halaka haikali na farko kuma ta zo ƙarshe a shekara ta 70 a zamaninmu sa’ad da aka halaka ta biyun. Wasu kuma sun yi zato cewa annabcin ya cika a zamanin Makabawa a ƙarni na biyu kafin zamaninmu.
Da a ce manzannin da kuma sauran Kiristoci na ƙarni na farko sun fahimci annabcin bakwai bakwai cikin bakwai sosai, da sun ambata shi don tabbatar wa mutane cewa Yesu Kristi ne Almasihu kuma ya zo a lokacin da aka annabta. Amma babu wurin da aka nuna cewa Kiristoci na farko sun ambata hakan.
Akwai wani abu kuma mai muhimmanci. Marubutan Linjilar Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna suna yawan nuna cewa wasu annabce-annabcen da ke Nassosin Ibrananci sun cika a kan Yesu Kristi. (Mat. 1:22, 23; 2:13-15; 4:13-16) Amma, babu kowanne cikinsu da ya rubuta cewa annabcin bakwai bakwai cikin bakwai game da Yesu Kristi ne.
A taƙaice: Ba mu sani ba ko lallai mutane a zamanin Yesu sun fahimci annabcin bakwai bakwai cikin bakwai. Amma, Linjila ta ba da wasu dalilai masu kyau da suka nuna cewa Yahudawa sun jira zuwan Almasihu.
a Littafi Mai Tsarki bai ce mala’ikun sun rera waƙa sa’ad da aka haifi Yesu ba.
b Za mu iya yin wannan tambayar, Ta yaya waɗannan shehunan suka san cewa akwai alaƙa tsakanin fitowar ‘tauraron’ a Gabas da haihuwar “Sarkin Yahudawa”? Shin sun sami labari ne cewa an haifi Yesu sa’ad da suke wucewa ta ƙasar Isra’ila?
c Don sanin yadda muka fahimci annabcin bakwai bakwai cikin bakwai a yau, ka duba littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa, shafuffuka na 197-199.