Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 12/15 p. 16
  • Ka Tuna?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Tuna?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • “Wane ne Fa Bawan nan Mai-Aminci, Mai-Hikima?”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • ‘Ka Faɗa Mana, Yaushe Waɗannan Abubuwa Za Su Zama?’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Wani ‘Bawa’ Da Yake Da Aminci Da Kuma Hikima
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • “Sukan Bi Ɗan Ragon Inda Ya Tafi Duka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 12/15 p. 16

Ka Tuna?

Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

A wane lokaci ne Yesu “ya yi wa’azi ga ruhohin da ke cikin maɗaura”? (1 Bit. 3:19)

Kamar dai bayan Yesu ya tashi daga mutuwa ne ya gaya wa miyagun ruhohi game da hukuncin da za a yi musu.—6/15, shafi na 23.

A wane lokaci ne Yesu zai ware tumaki daga awaki? (Mat. 25:32)

Yesu zai yi hakan a lokacin ƙunci mai girma, bayan an halaka addinan ƙarya.—7/15, shafi na 6.

A wane lokaci ne miyagun da aka ambata a kwatancin alkama da ciyayi za su yi kuka da kuma ciza haƙoransu? (Mat. 13:36, 41, 42)

Za su yi hakan a lokacin ƙunci mai girma, sa’ad da suka ankara cewa lallai za a halaka su.—7/15, shafi na 13.

A wane lokaci ne furucin Yesu game da bawa mai aminci, mai hikima ya cika? (Mat. 24:45-47)

Bai soma cika a ranar Fentakos na shekara ta 33 a zamaninmu ba, amma bayan shekara ta 1914. A shekara ta 1919 ce aka naɗa bawan bisa iyalin gidansa, kuma sun haɗa da dukan Kiristoci da suke amfana daga koyarwar Allah.—7/15, shafuffuka na 21-23.

A wane lokaci ne Yesu zai sanya bawan bisa dukan mallakarsa?

Hakan zai faru a nan gaba, sa’ad da aka ba bawa mai aminci ladarsa a sama, a lokacin ƙunci mai girma.—7/15, shafi na 25.

Shin Allah yana “tara”? (A. M. 10:34)

Allah ba ya ɗaukan mutum da muhimmanci fiye da ɗan’uwansa saboda bambancin launin fata ko ƙasa ko matsayi ko kuma wani dalili dabam.—7/1, shafi na 11.

Ban da ikon Allah, mene ne ya taimaki Shaidu 230 su tsira daga tafiya mai nisa da suka yi daga sansanin Sachsenhausen?

Ko da yake sun yi kasala saboda rashin abinci da kuma ciwo, amma sun ci gaba da ƙarfafa juna.—8/15, shafi na 18.

Me ya sa yadda Isra’ilawa suka ƙetare Kogin Urdun kuma suka shiga Ƙasar Alkawari abin ƙarfafa ne a gare mu?

Ko da yake ruwan kogin ya cika sosai, amma Jehobah ya sa kogin ya daina gudu domin mutanen su iya ƙetarewa. Babu shakka, hakan ya ƙarfafa bangaskiyarsu da dogararsu ga Jehobah, kuma zai iya ƙarfafa mu ma a yau.—9/15, shafi na 16.

Me ya sa Jehobah ya tsani batsa?

Jehobah ya san cewa batsa za ta iya ɓata rayuwar mutum gaba ɗaya. Yana ƙaunar mu kuma yana so ya kāre mu daga abin da zai iya ɓata mu da aurenmu da kuma iyalinmu.—9/1, shafi na 6.

Ta yaya annabcin Mikah 5:5 game da makiyaya da shugabannai yake cika a yau?

Mun fahimci cewa dattawan ikilisiya da suke ƙarfafa bayin Allah kuma suke shirya su don harin da za a kawo musu a nan gaba ne ‘makiyaya bakwai da shugabannai takwas’ da aka ambata a littafin Mikah 5:5.—11/15, shafi na 20.

Me ya sa ya kamata mu riƙa gafarta wa mutane?

Dalili mafi muhimmanci da ya sa ya kamata mu riƙa gafarta wa mutane shi ne don Allah yana gafarta mana. Wani dalili kuma shi ne don za mu iya roƙan wasu su gafarta mana.—11/1, shafi na 13.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba