KA KUSACI ALLAH
“Duba, Sabonta Dukan Abu Nake Yi”
Shin kana so kai da iyalinka ku samu ƙoshin lafiya kuma ku rayu har abada? Shin kana marmarin zama a cikin duniyar da azaba da wahala da kuma mutuwa sun zama labari? Zama a irin wannan duniyar ba mafarki ba ne domin ba da daɗewa ba, Jehobah zai kawo sabuwar duniya da ya yi alkawarinta, inda adalci zai kasance. Ka lura da yadda zai cika wannan alkawarin a Ru’ya ta Yohanna 21:3-5.—Karanta.
“[Allah] zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Hawayen mene ne zai share? Ba hawayen da muke yi saboda farin ciki ko kuma wanda ke kāre idanunmu ba. Alkawarin da Allah ya yi ya shafi hawayen da muke yi saboda wahala da kuma baƙin ciki. Allah zai share wannan hawayen ta wajen kawar da waɗannan matsalolin.
“Mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Mutuwa ce ta fi sa mutane baƙin ciki a duniya a yau. Jehobah zai ’yantar da ’yan Adam daga hannun mutuwa. Yaya zai yi hakan? Ta wajen kawar da ainihin sanadiyyar mutuwa, wato zunubin da muka gāda daga Adamu. (Romawa 5:12) Jehobah zai sa ’yan Adam masu yi masa biyayya su zama kamilai ta wajen hadayar fansa ta Yesu.a Sa’an nan zai “kawar” da maƙiyi na ƙarshe, wato mutuwa. (1 Korintiyawa 15:26) ’Yan Adam masu aminci za su yi rayuwa har abada cikin ƙoshin lafiya, kamar yadda Allah ya nufa.
“Ba kuwa za a ƙara [shan] . . . azaba ba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Wace irin azaba ce Allah zai kawar? Kowace irin azaba da mutane suke sha domin zunubi da ajizanci, da ya sa miliyoyin mutane ba sa jin daɗin rayuwa.
Ba da daɗewa ba, za a kawar da kuka da mutuwa da azaba. Amma, kana iya tunani cewa, ‘A ina ne hakan zai faru?’ ‘A sama ne za a yi irin wannan rayuwa da Allah ya yi alkawarinta?’ A’a. Ga dalilai biyu da suka sa muka faɗa haka. Na farko, an soma wannan alkawarin da furucin nan ‘mazaunin Allah yana wurin mutane,’ kuma a duniya ne mutane suke zama. (Ru’ya ta Yohanna 21:3) Na biyu, da yake an ambata cewa “mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba” a duniyar, hakan yana nufin cewa ana mutuwa a duniyar a dā. Mutuwa ba ta taɓa kasancewa a sama ba, amma an daɗe ana mutuwa a duniya. Saboda haka, abin da Allah ya faɗa game da ingantacciyar rayuwa zai faru a nan duniya ne.
Allah zai share dukan hawaye da ake yi saboda wahala da kuma baƙin ciki
Jehobah yana so mu gaskata da alkawarin da ya yi game da sabuwar duniya, inda za a yi adalci. Bayan da ya faɗi albarka da za a samu, sai ya ba da tabbaci cewa alkawarinsa zai cika. Ya ce: “Duba, sabonta dukan abu nake yi.” Sai ya daɗa cewa: “Waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya.” (Ru’ya ta Yohanna 21:5) Ka ƙara koyan yadda kai da iyalinka da kuma abokanka za ku kasance cikin waɗanda za su ga lokacin da Allah zai cika alkawarinsa.
a Don ka ƙara koya game da hadayar fansa ta Kristi, ka duba babi na 5 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa.