Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 11/15 p. 15
  • Bauta wa Allah Ta Zama Masa Magani!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bauta wa Allah Ta Zama Masa Magani!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 11/15 p. 15

Bauta wa Allah Ta Zama Masa Magani!

Sa’ad da wasu majagaba biyu suka shiga wani gida a ƙasar Kenya don su yi wa’azi, sun yi mamakin ganin wani ƙaramin mutum mai suna Onesmus yana kwance a kan gado. Mutumin yana da ƙaramin kafaɗa da guntayen hannaye. Sa’ad da majagaban suka gaya masa alkawarin da Allah ya yi cewa “gurgu za ya yi ta tsalle kamar barewa,” sai ya yi murmushi.—Isha. 35:6.

An gaya wa majagaban cewa an haifi Onesmus wanda yanzu ya kusan shekara 40 da wani irin ciwon ƙashi da ake kira, osteogenesis imperfecta. Ƙasusuwansa ba su da ƙarfi ko kaɗan kuma idan an ɗan taɓa su za su karye. Tun da wannan ciwon ba shi da magani, Onesmus zai riƙa amfani da keken guragu a koyaushe kuma ba zai riƙa jin daɗin jikinsa ba.

Onesmus ya yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Amma, mahaifiyarsa ba ta yarda ya riƙa halartar taro ba, domin tana ganin hakan zai sa ciwonsa ya daɗa tsanani. A sakamako, ’yan’uwa suna ɗaukan jawaban da ake yi a taro a faifai don Onesmus ya saurara a gida. Bayan an yi nazari da shi na tsawon wata biyar, sai ya yanke shawara cewa zai halarci taro, ko da mene ne zai faru.

Shin halartar taro ya sa yanayin Onesmus ya daɗa tsanani kuwa? Ko kaɗan. Ya ce: “Ciwon da nake yi yana raguwa sa’ad da ake taro.” Ya kuma ce begen da yake da shi yana sa ya ji daɗin jikinsa. Mahaifiyarsa ta lura da yadda yanayin ɗanta ya canja kuma hakan ya sa ta farin ciki sosai har ta yarda a yi nazari da ita ma. Ta ce: “Bauta wa Allah ya zama wa ɗana magani.”

Ba da daɗewa ba, Onesmus ya zama mai shelar da bai yi baftisma ba. Daga baya, sai ya yi baftisma kuma ya zama bawa mai hidima. Ko da yake ba ya iya amfani da ƙafafunsa da kuma hannunsa ɗaya, amma yana da marmarin yin iya ƙoƙarinsa a hidimar Jehobah. Yana so ya yi hidimar majagaba na ɗan lokaci, amma ya yi jinkirin yin hakan. Me ya sa? Domin ya san cewa zai dangana ga wani da zai riƙa tura kekensa sa’ad da za su wa’azi. Sa’ad da ya gaya wa ’yan’uwa Kirista matsalarsa, sai suka ce za su tallafa masa. ’Yan’uwan sun taimaka masa ya yi hidimar majagaba na ɗan lokaci.

Onesmus yana so ya zama majagaba na kullum amma har ila, ya damu da yadda zai riƙa samun mutumin da zai tura shi a kekensa. Mene ne ya taimaka masa? Ya karanta nassin yini wata rana kuma hakan ya ƙarfafa shi. Littafin Zabura 34:8 ne wanda ya ce: “Ku ɗanɗana, ku duba, Ubangiji nagari ne.” Bayan ya yi bimbini a kan wannan nassin, sai ya yanke shawara cewa zai zama majagaba na kullum. Yanzu yana wa’azi kwana huɗu a mako kuma yana da mutane da yawa da yake nazari da su. Waɗannan mutanen da yake nazari da su suna samun ci gaba sosai. Onesmus ya je Makarantar Koyar da Majagaba a shekara ta 2010. Ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya ga cewa ɗaya cikin ’yan’uwan da suka fara yi masa wa’azi ne malamin makarantar!

Ko da yake iyayen Onesmus sun rasu yanzu, amma ’yan’uwa a cikin ikilisiya suna biyan bukatunsa. Yana farin ciki domin dukan albarkar da yake morewa kuma yana ɗokin ganin ranar da babu mutumin da zai ce, “Ina ciwo!”—Isha. 33:24.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba