Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 8/15 p. 9
  • Jehobah Yana ‘Ɗaukan Nauwayata Kowace Rana’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana ‘Ɗaukan Nauwayata Kowace Rana’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 8/15 p. 9

Jehobah Yana ‘Ɗaukan Nauwayata Kowace Rana’

Maretha du Raan

Na ga tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunata kuma yana taimaka mini duk da rashin lafiyata da ke da wuyar jimrewa. Kuma fiye da shekara 20 da suka shige, na yi farin cikin bauta wa Jehobah a matsayin majagaba.

An haife ni a shekara ta 1956 da ciwon kashin baya da ake kira spina bifida. Hakan ya sa ina tafiya da kyar kuma na samu wasu matsaloli masu tsanani a sakamako.

Wasu ma’aurata Shaidun Jehobah da suke wa’azi a ƙasashen waje sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da iyayena tun ba a haife ni ba. Sa’ad da nake ƙarama, masu shela ƙalilan ne kawai suke zama a birnin Usakos, Namibiya. Hakazalika, muna yin taron ikilisiya a matsayin iyali. Sa’ad da nake ’yar shekara 7, sai aka yi mini fiɗa don na iya yin fitsari. Na kamu da ciwon farfaɗiya sa’ad da nake ’yar shekara 14. Ban iya sauƙe karatu a makarantar sakandare ba domin ba ta kusa da gida kuma ina bukatar taimakon iyayena.

Akasin haka, na duƙufa cewa zan kyautata dangantaka ta da Jehobah. A lokacin, babu littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da yawa a yaren Afrikaans. Saboda haka, na koyi karanta Turanci don na samu yin nazarin littattafai da yawa. Na zama mai shela kuma na yi baftisma sa’ad da nake ’yar shekara 19. Bayan na yi baftisma, na yi rashin lafiya iri-iri har na tsawon shekara huɗu. Bugu da ƙari, tsoron maƙwabtana ya hana ni yin ƙwazo a hidima.

Sa’ad da na ba shekara 20 baya, sai muka ƙaura daga ƙasar Namibiya zuwa Afrika ta Kudu kuma wannan ne lokaci na farko da na halarci taro a Majami’ar Mulki. Hakan ya sa ni farin ciki sosai. Amma, sai aka sake yi mini fiɗa don na iya yin kashi.

Daga baya, wani mai kula da da’ira ya ziyarce mu kuma ya yi jawabi game da hidimar majagaba. Jawabin ya ratsa zuciyata sosai. Ko da yake na san cewa ba ni da ƙoshin lafiya, amma Jehobah ya kāre ni a dukan shekarun da suka shige. Sai na ce ina so na zama majagaba, amma dattawan ikilisiyarmu ba su yarda ba saboda rashin lafiyata.

Duk da haka, na duƙufa cewa zan yi iya ƙoƙarina a wa’azi. Mahaifiyata da kuma wasu ’yan’uwa sun taimake ni na samu sa’o’in da ake bukata daga majagaba har na tsawon wata shida. Hakan ya sa dattawan su san cewa zan iya yin hidimar majagaba duk da rashin lafiyata. Sai na sake saka takarda kuma a wannan karon aka amince da ita. Na zama majagaba na kullum a ranar 1 ga Satumba, 1988.

Ina shaida taimakon Jehobah a kai a kai a matsayin majagaba. Yin hidimar majagaba ta taimaka mini na mai da hankali ga dangantakata da Jehobah ba ga rashin lafiyata ba. Na yi matuƙar farin ciki don taimaka wa mutane su keɓe kansu ga Jehobah kuma su yi baftisma.

Har yanzu ba ni da ƙoshin lafiya. Amma, Jehobah yana ‘ɗaukan nawayata kowace rana.’ (Zab. 68:19) Jehobah ya taimaka mini na jimre da yanayina kuma ya sa na ji daɗin rayuwata!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba