KA KUSACI ALLAH
“Al’amura Nasa da Ba Su Ganuwa, . . . a Sarari Ake Ganinsu”
Ka gaskata da Allah kuwa? Idan amsarka e ce, za ka iya tabbatar ma wani cewa Allah ya wanzu? Gaskiyar ita ce, akwai abubuwa kewaye da mu da suke tabbatar mana cewa akwai Mahalicci mai hikima da iko da kuma ƙauna. Mene ne waɗannan abubuwan, kuma za mu iya ɗaukan su da muhimmanci sosai kuwa? Bari mu bincika abin da manzo Bulus ya faɗa a cikin wasiƙarsa ga Kiristoci da ke Roma don mu sami amsar wannan tambayar.
Bulus ya ce: ‘Gama tun halittar duniya al’amuran [Allah] da ba su ganuwa, watau ikonsa madawwami da allahntakarsa, a sarari a ke ganinsu; ta wurin abubuwa da an halitta ana gane su; har kuwa su rasa hujja.’ (Romawa 1:20) Mahaliccinmu ya ba da tabbaci cewa ya wanzu ta wajen abubuwan da ya halitta, kamar yadda Bulus ya bayyana. Bari mu tattauna furucin nan da Bulus ya yi da kyau.
Bulus ya ce ana iya ganin halayen Allah “tun halittar duniya.” A nan, kalmar Helenanci da aka fassara “duniya” ba ta nufin doron ƙasa, amma tana nufin ’yan Adam ne.a Saboda haka, Bulus yana nufi cewa tun halittar ’yan Adam, mutane suna iya ganin halayen Mahaliccinmu ta wajen kallon abubuwan da ya halitta.
Muna ganin waɗannan abubuwan da suke ba mu tabbaci a ko’ina. Ba a ɓoye suke ba, amma “a sarari ake ganinsu.” Halittu manya da ƙanana suna nuna a fili cewa akwai Mahalicci kuma yana da halaye masu kyau. Abubuwan al’ajabi da Allah ya halitta suna nuna cewa Shi mai hikima ne, ko ba haka ba? Hakika, taurari da ke samaniya da kuma igiyar ruwa a teku suna nuna cewa Mahaliccinmu mai iko ne. Abinci kala-kala masu daɗi da kuma fitowa da faɗuwar rana suna nuna mana cewa Allah yana ƙaunar ’yan Adam sosai.—Zabura 104:24; Ishaya 40:26.
Ana ganin waɗannan abubuwan a fili sosai kuwa? Hakika, a bayyane suke sarai, saboda haka, waɗanda ba su gan waɗannan abubuwan ba kuma suka ƙi gaskata da Allah ba su da “hujja.” Wani masani ya ba da kwatanci da zai bayyana hakan. Ya ce: “A ce wani direba ya yi watsi da wata alamar da ke nuna masa cewa ya bi hagu. Sai ɗan sanda ya tsayar da shi don ya ci masa tara. Direban kuma ya ce bai ga alamar ba. Amma ɗan sandan ya ce sai ya biya tarar, don alamar tana fili kuma direban yana gani da kyau. Ban da haka ma, hakkin direban ne ya riƙa lura da alamun da ke kan hanya.” Haka yake da alamu ko abubuwan da suke tabbatar mana cewa akwai Allah. Waɗannan “alamun” a fili suke. Tun da mu halittu ne masu tunani, muna da ilimin gane waɗannan alamun. Duk wanda ya ce bai gan waɗannan abubuwan ba bai da hujja.
Mahaliccinmu ya ba da tabbaci cewa ya wanzu ta wajen abubuwan da ya halitta
Hakika, halittun Allah suna koya mana abubuwa da yawa game da Mahaliccinmu. Amma akwai littafin da ke bayyana mana abubuwa game da Allah fiye da halittu, kuma wannan littafi shi ne Littafi Mai Tsarki. A cikinsa, za mu iya samun amsar wannan tambaya mai muhimmanci: Mene ne Allah ya nufa wa duniya da kuma mutane da ke cikin ta? Sanin amsar wannan tambayar zai taimaka maka ka kusaci Allah, wanda “al’amura nasa da ba su ganuwa . . . a sarari ake ganinsu” a ko’ina.
Karatun Littafi Mai Tsarki na watan Oktoba
a Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa “duniya” tana da alhakin zunubi kuma tana bukatar mai ceto. Wannan ya nuna cewa kalmar nan a wannan ayar tana nufin mutane ne, ba doron ƙasa ba.—Yohanna 1:29; 4:42; 12:47.