LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE
“Na soma tunani sosai game da inda na nufa a rayuwa”
SHEKARAR HAIHUWA: 1941
ƘASAR HAIHUWA: OSTARELIYA
TARIHI: MASHAYIN GIYA DA TABA
RAYUWATA A DĀ:
Na girma a Warialda, wani ƙaramin gari a jihar New South Wales. Warialda gari ne da ake noman hatsi da kayan lambu dabam-dabam kuma ana kiwon tumaki da shanu ma a wurin. Garin akwai tsabta kuma ba a cika aikata laifi.
Ni ne ɗan fari cikin yara 10, kuma sa’ad da na kai ɗan shekara 13, na soma aikin kuɗi don in tallafa wa iyalinmu. Na yi aiki a gona da yake ban yi makaranta sosai ba. Sa’ad da na kai shekara ɗan 15, na soma horon dawaki.
Yin aiki a gona abu ne da na ji daɗin yi amma kuma yana da nasa ƙalubale. Nakan zauna in ji ɗumin wuta da dare kuma in kalli wata da taurari yayin da nake jin daɗin iska da ke busawa daga itatuwa. A lokacin, zuciyata takan gaya mini cewa akwai Wanda ya halicci dukan waɗannan abubuwa masu ban al’ajabi. A wani ɓangaren kuma, mazauna wurin suna da wasu banzan halaye da za su iya shafan mutum. Sun saba yin ashar kuma ana yawan samun sigari a wurin. Ba da daɗewa ba yin ashar da kuma shan sigari sun zama jinina.
Da na kai ɗan shekara 18, na ƙaura zuwa Sydney. Na yi yunƙurin shiga soja amma an ƙi a ɗauke ni domin ban yi makaranta ba. Na sami aiki kuma na zauna a birnin Sydney har tsawon shekara ɗaya. A wannan lokacin ne na haɗu da Shaidun Jehobah. Na halarci taronsu sa’ad da suka gayyace ni kuma nan da nan na gane cewa koyarwarsu gaskiya ne.
Amma, ba da daɗewa ba bayan haka, na yanke shawarar komawa ƙauye. Sai na koma Goondiwindi a jihar Queensland. Na sami aiki kuma na yi aure, amma abin baƙin ciki, na soma shaye-shaye.
Mun haifi ’ya’ya biyu. Bayan haihuwar ’ya’yanmu, na soma tunani sosai game da inda na nufa a rayuwa. Na tuna abin da na ji a taron Shaidun Jehobah da na taɓa halarta a ƙasar Sydney, sai na ƙudura cewa zan ɗauki mataki a kai.
Na tarar da wata tsohuwar mujallar Hasumiyar Tsaro, wadda ke ɗauke da adireshin ofishin reshen Shaidun Jehobah da ke ƙasar Ostareliya. Na aika wasiƙa cewa ina bukatar taimako. Da suka sami wasiƙar sai suka aika wani Mashaidi mai kirki ya zo ya ziyarce ni. Ba da daɗewa ba ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:
Yayin da nake nazarin Littafi Mai Tsarki, na gano cewa ina bukatar in yi canji sosai a rayuwata. Wata ayar Littafi Mai Tsarki da ta taɓa ni sosai ita ce 2 Korintiyawa 7:1. Wannan ayar ta ƙarfafa mu mu “tsarkake kanmu daga dukan ƙazamtar jiki.”
Na ƙudura cewa zan daina shan taba da kuma yin maye. Bai kasance mini da sauƙi in yi waɗannan gyare-gyare ba, domin waɗannan halayen sun zama min jaraba da daɗewa. Amma na riga na ƙudura cewa zan yi rayuwa da za ta faranta wa Allah rai. Abin da ya taimake ni shi ne bin ƙa’idar wata aya da ke littafin Romawa da ta ce: “Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sake ta wurin sabunta hankalinku ɗungum.” (Romawa 12:2, Littafi Mai Tsarki) Na fahimci cewa idan ina son in canja halayena, wajibi ne in canja tunanina kuma in kasance da ra’ayin Allah. Da taimakon Allah, na daina shan taba da kuma yin maye.
“Na fahimci cewa idan ina son in canja halayena, wajibi ne in canja tunanina”
Amma halin da ya kasance mini da wuya sosai in daina shi ne yin ashar. Na san gargaɗin da ke littafin Afisawa 4:29: “Kada kowane ruɓaɓɓen zance shi fita daga cikin bakinku.” Duk da haka, ban iya daina yin ashar nan da nan ba. Amma yin bimbini a kan kalmomin da ke Ishaya 40:26 ya taimaka mini. Game da sararin samaniya, wannan ayar ta ce: “Ku tada idanunku sama, ku duba ko wanene ya halicci waɗannan, wanda ya kawo rundunansu bisa ga lissafinsu: yana kiransu duka da sunansu; bisa ga girman ikonsa, domin shi mai-ƙarfi ne cikin iko, ba wanda ba shi ko ɗaya.” Na yi tunani cewa idan Allah yana da ikon halittar sararin samaniya, tabbas zai iya ba ni ƙarfin yin waɗannan canji don in faranta masa rai. Da addu’a da kuma himma, na daina yin ashar.
YADDA NA AMFANA:
A matsayin mai kula da dabobbi, ban cika yin magana da mutane ba domin mutane kaɗan ne kawai suke zuwa gonar da nake aiki. Amma koyarwa da ake tanadarwa a taron Shaidun Jehobah ta taimaka mini in iya yin magana da mutane a hankali kuma ba tare da yin ashar ba. Ƙari ga wasu abubuwa da na koya, na koyi yin magana da mutane game da bisharar Mulkin Allah.—Matta 6:9, 10; 24:14.
Na yi shekaru da yawa ina hidima a matsayin dattijo a ikilisiyarmu. Gata ne a gare ni in yi iya ƙoƙarina wajen taimaka wa ’yan’uwana masu bi. Amma albarka mafi kyau da na samu ita ce bauta wa Jehobah tare da matata da kuma yaranmu.
Ina godiya ga Jehobah, wanda ya ilimantar da ni, ko da yake ban yi makaranta ba. (Ishaya 54:13) Na gaskata da kalmomin da ke Misalai 10:22, cewa: “Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata.” Ni da iyalina muna ɗokin ƙara koyan abubuwa game da Jehobah da kuma bauta masa har abada.