Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 6/15 pp. 22-23
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Shin Aljanu Suna Wanzuwa da Gaske?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Su Waye ne ko Kuma Mene ne Ake Nufi da Mala’iku?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 6/15 pp. 22-23

AMSOSHIN TAMBAYOYIN MASU KARATU

Su waye ne “’ya’yan Allah” da aka ambata a Farawa 6:2, 4 da suka rayu kafin Rigyawa?

Tabbas, wannan furucin yana nufin mala’iku ’ya’yan Allah. Amma, mene ne ya nuna hakan?

Littafin Farawa 6:2 ya ce: “Sai ’ya’yan Allah suka ga ’yan mata na mutane kyawawa ne; suka ɗauko wa kansu mata dukan waɗanda suka zaɓa.”

A Ibrananci, an yi amfani da furucin nan “’ya’yan Allah” a cikin littafin Farawa 6:2, 4 da Ayuba 1:6; 2:1; 38:7 da kuma Zabura 89:6. Mene ne waɗannan nassosin suka nuna game da “’ya’yan Allah”?

“’Ya’yan Allah” da aka ambata a littafin Ayuba 1:6 suna nufin halittu na ruhu da suka taru a gaban Allah, har da Shaiɗan da ya fito “yawace-yawace cikin duniya.” (Ayu. 1:7; 2:1, 2) Hakazalika, littafin Ayuba 38:4-7 ya ce “’ya’yan Allah” sun “yi sowa don farinciki” sa’ad da Allah ya ‘sanya dutsen ƙusurwar’ duniya. Babu shakka, waɗannan mala’iku ne domin ba a halicci ’yan Adam ba a lokacin. Haka nan ma, “’ya’yan Allah” da aka ambata a littafin Zabura 89:6 suna nufin mala’iku, ba mutane ba.

Saboda haka, su wane ne “’ya’yan Allah” da aka ambata a littafin Farawa 6:2, 4? Bisa ga abin da ke cikin nassosin da aka ambata ɗazu, tabbas ne cewa suna nufin mala’iku da suka sauko duniya.

Wasu ba sa son su amince cewa mala’iku suna iya yin sha’awar jima’i. Kalaman Yesu a Matta 22:30 sun nuna cewa ba a yin aure da kuma jima’i a sama. Amma, akwai lokuta da mala’iku suka ɗauki siffar ’yan Adam kuma suka ci da sha tare da mutane. (Far. 18:1-8; 19:1-3) Saboda haka, gaskiya ne cewa mala’iku za su iya saduwa da mata sa’ad da suka ɗauki siffar mutane.

Littafi Mai Tsarki ya ba da dalilai na amincewa da hakan. Littafin Yahuda, ayoyi 6 da 7 sun kwatanta zunubin ’yan Saduma da suka biɗi sha’awar jiki da na ‘mala’iku waɗanda ba su riƙe matsayi nasu ba.’ Nasabar da ke tsakanin waɗannan mala’ikun da kuma ’yan Saduma shi ne sun “ba da kansu ga fasikanci, suka biɗi kwaɗayi ba irin na tabi’a ba.” Makamancin wannan nassin shi ne 1 Bitrus 3:19, 20, da ya ambata mala’iku masu tawaye sa’ad da yake magana game da “zamanin Nuhu.” (2 Bit. 2:4, 5) Abin da mala’iku masu tawaye suka yi a zamanin Nuhu yana kamar zunubin Saduma da Gwamarata.

A taƙaice, za mu amince da hakan idan muka fahimci cewa “’ya’yan Allah” da aka ambata a Farawa 6:2, 4 suna nufin mala’iku da suka ɗauki siffar mutane kuma suka yi lalata da mata.

Mene ne Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce Yesu “ya yi wa’azi ga ruhohin da ke cikin maɗaura”?—1 Bit. 3:19.

Manzo Bitrus ya nuna cewa waɗannan ruhohin sun yi “kangara a dā, lokacin da haƙurin Allah yana jinkiri a zamanin Nuhu.” (1 Bit. 3:20) A bayyane yake cewa Bitrus yana magana game da mala’iku da suka yi tawaye tare da Shaiɗan. Yahuda ya ce Allah “ya tsare [mala’iku] cikin madawwaman sarƙoƙi a cikin duhu zuwa hukuncin babbar ranar” tun da yake “ba su riƙe matsayi nasu ba, amma suka rabu da nasu wurin zama.”—Yahu. 6.

Ta yaya mala’iku suka yi rashin biyayya a zamanin Nuhu? Waɗannan mugayen mala’iku sun ɗauki siffar ’yan Adam, kafin Rigyawa, kuma Allah bai so su yi hakan ba. (Far. 6:2, 4) Ƙari ga haka, waɗannan mala’iku da suka yi jima’i da mata sun yi abin da bai dace da su ba. Allah bai halicci mala’iku su yi jima’i da mata ba. (Far. 5:2) A lokacin da ya dace, Allah zai halaka waɗannan mala’iku da suka yi rashin biyayya. Amma, an tsare su “cikin duhu” a yau, wato, suna cikin yanayi da ba za su iya yin kome ba.

A wane lokaci ne Yesu ya yi wa’azi ga waɗannan “ruhohin da ke cikin maɗaura,” kuma ta yaya ya yi hakan? Bitrus ya rubuta cewa hakan ya faru sa’ad da aka “rayar da [Yesu] cikin ruhu.” (1 Bit. 3:18, 19) Ka lura cewa Bitrus ya ce Yesu “ya yi wa’azi.” Da yake Bitrus ya yi amfani da furucin nan “ya yi,” hakan yana nufin cewa Yesu ya yi wa’azin kafin Bitrus ya rubuta wasiƙarsa ta farko. Saboda haka, kamar dai bayan Yesu ya tashi daga matattu, ya gaya wa miyagun ruhohi game da hukunci da za a yi musu. Yesu ya yi musu wa’azin hukunci ne ba na bege ba. (Yun. 1:1, 2) Da yake Yesu ya kasance da bangaskiya da aminci har mutuwa kuma aka ta da shi daga matattu, hakan ya nuna cewa Iblis ba zai iya yi wa Yesu kome ba. Shi ya sa Yesu ya yi wannan shelar hukunci.—Yoh. 14:30; 16:8-11.

A nan gaba, Yesu zai ɗaure kuma ya jefa Shaiɗan da waɗannan mala’iku cikin rami marar matuƙa. (Luk 8:30, 31; R. Yoh. 20:1-3) Kafin lokacin, waɗannan mala’ikun suna cikin yanayin da ba za su iya yin kome ba, kuma babu shakka cewa za a halaka su dindindin.—R. Yoh. 20:7-10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba