Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 7/1 pp. 8-9
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Dā Ni Mugu Ne da Kuma Mai Son Yin Fada
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Shaidun Jehobah Suna Raba Aure Ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 7/1 pp. 8-9

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“A Dā, Na So In Zama Firist”

Roberto Pacheco ne ya ba da labarin

  • SHEKARAR HAIHUWA: 1957

  • ƘASAR HAIHUWA: MEZIKO

  • TARIHI: ƊALIBIN MAKARANTAR KOYAR DA ADDINI, MAI SAURIN FUSHI

RAYUWATA A DĀ:

An haife ni ne a wani ƙaramin gari da ake kira Texcoco. A lokacin, ba a yi kwalta a hanyoyin da ke garin ba saboda haka, suna da ƙura sosai. Mutane daga ƙauyukan da ke kusa da mu suna yawan zuwa garinmu da kayayyakin sayarwa a kan jakuna. Iyalinmu matalauta ne sosai kuma ni ne na bakwai cikin ’ya’ya tara. Sana’ar da mahaifina ya yi don ya ciyar da iyalinmu ita ce gyaran takalmi. Amma ya mutu sa’ad da nake ɗan shekara bakwai. Daga lokacin ne mahaifiyata ta ɗauki ɗawainiyar ciyar da iyalinmu.

Kakana yana buga wani abin kiɗa kamar goge kuma shi ne shugaban mawaƙa da suka ƙware a waƙoƙin addini. Kusan kowa a cikin iyalinmu yana buga wani kayan kiɗa. Mahaifiyata tana cikin rukunin mawaƙa a coci kuma kawuna yana rera waƙoƙi a inda ake wasannin kwaikwayo. Mu masu bin addinin Katolika ne sau da kafa kuma ina yi wa firist hidima a cikin coci. Buri na shi ne in zama ɗan mishan. Amma ni mai yawan kallon fina-finan karet ne. Kuma hakan ya sa na koyi rashin imani.

Na shiga wata makarantar koyar da malaman addinin Kirista a birnin Puebla. Ina son in zama firist. Amma sa’ad da na kusan sauke karatu, wasu abubuwa da ke faruwa a cikin Cocin Katolika sun sa ni sanyin gwiwa. Wata budurwa mai-zaman zuhudu ta so in kwana da ita. Ko da yake ban yarda ba, amma al’amarin ya sa na soma sha’awar yin aure. Ƙari ga haka, na lura cewa firistoci da yawa ba sa rayuwa bisa abin da suke koyarwa. Da shigewar lokaci, na yi watsi da ƙudurin da na yi na zama firist.

A matsayin mai yi wa firist hidima, na so in zama ɗan mishan na Cocin Katolika, amma ina yawan kallon fina-finan karet kuma hakan ya sa na koyi rashin imani

Daga baya na soma koyan kiɗa a wata makarantar da ake kira National Conservatory of Music a Mexico City. Sa’ad da na sauke karatu, sai na yi aure, kuma ba da daɗewa ba matata ta haifa mana yara huɗu. Na yi waƙoƙi sa’ad da ake cin jibi a Cocin Katolika kuma da wannan sana’ar ce na ciyar da iyalina.

Tun farkon aurenmu mun fuskanci matsaloli. Ni da matata mukan yi faɗa sosai, kuma a yawancin lokaci kishi ne ke sa mu yin hakan. Da farko, muna yawan zagin juna ne kawai, amma daga baya, sai muka shiga dambe. Bayan shekara 13, muka yanke shawarar rabuwa kuma a ƙarshe muka kashe auren.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Na soma haɗuwa ne da Shaidun Jehobah kafin in rabu da matata. A lokacin, Shaidun Jehobah guda biyu sun zo gidanmu kuma suka tattauna Littafi Mai Tsarki da ni. Da yake ina ganin na san abubuwa da yawa game da addini, na yi ƙuduri cewa sai na ƙaryata su. Sai na soma yi musu tambayoyi masu wuya da na ɗauka cewa ba za su iya ba da amsoshin ba. Amma da suka ba da amsoshi masu ƙayatarwa daga Littafi Mai Tsarki, hakan ya ba ni mamaki. A nan ne na gane cewa ban san kome ba. Amma kuma, matata tana yawan yi wa Shaidun rashin hankali, ƙari ga haka, ba na samun lokacin tattaunawa da su, saboda haka, suka daina zuwa.

Shekara biyar bayan haka, sa’ad da na fara zama da wata mata mai suna Elvira, na sake haɗuwa da Shaidun Jehobah. Elvira ba ta yi sūkar Shaidun ba, kuma hakan ya sa na sami zarafin yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai. Duk da haka, na yi shekaru da dama kafin in canja halaye na.

Na fahimci cewa idan ina son bauta wa Jehobah da dukan zuciyata, wajibi ne in yi gagaruman canje-canje a rayuwata. Na farko, ina bukata in daina sana’ata ta yin waƙoƙi a lokacin cin jibi a Cocin Katolika kuma in soma wata sana’a dabam. (Ru’ya ta Yohanna 18:4) Ƙari ga haka, ina kuma bukatar in yi rajistar aurena da Elvira.

A cikin canje-canjen da na yi, mafi wuya shi ne shawo kan saurin fushi da nake yawan yi. Ayoyin Littafi Mai Tsarki guda biyu da suka taimaka mini su ne Zabura 11:5, wadda ta nuna cewa Jehobah ya tsane zalunci, da kuma 1 Bitrus 3:7, inda na koyi cewa idan ina son Jehobah ya ji addu’ata, wajibi ne in riƙa mutunta matata. Sa’ad da na yi bimbini a kan waɗannan ayoyin kuma na roƙi Jehobah cikin addu’a ya taimake ni, da sannu-sannu, na shawo kan yawan saurin fushi da nake yi.

A cikin Littafi Mai Tsarki, na koyi cewa idan ina son Jehobah ya ji addu’ata, wajibi ne in riƙa mutunta matata

YADDA NA AMFANA:

A yanzu, ni da iyalina muna farin ciki. Ina ƙoƙarin kyautata dangantakata da ’ya’yan da na samu a auren farko da na yi kuma ina taimaka wa iyalina na yanzu su kasance da bangaskiya sosai.

Sa’ad da nake ƙarami na so in zama firist kuma in riƙa taimaka wa mutane. Yanzu na tabbata cewa rayuwata tana da ma’ana sosai. Ina ciyar da iyalina ta wajen koya wa mutane waƙa. Ina matuƙar godiya ga Jehobah don yadda ya yi haƙuri da ni da kuma yadda ya ba ni zarafin canja halayena don in zama mutumin kirki!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba