Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 4/15 p. 32
  • Ka Sani?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sani?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 4/15 p. 32

KA SANI?

Shin An Sake Gina Haikalin Urushalima Bayan Shekara ta 70 a Zamaninmu?

YESU ya annabta cewa za a halaka haikalin Jehobah. Wannan annabcin ya cika a shekara ta 70, sa’ad da Titus ya ja-goranci sojojin Roma, kuma suka halaka Urushalima. (Mat. 24:2) Daga baya, wani Sarkin Roma mai suna Julian ya yi shirin sake gina haikalin.

An kira Julian arne na ƙarshe da ya mulki Ƙasar Roma. Constantine mai Girma ne kawunsa, kuma Kiristoci na zamaninsa ne suka koyar da shi. Amma sa’ad da ya soma sarauta a shekara ta 361, sai ya ƙi bin koyarwarsu da kuma ayyukansu na ɓatanci. Littattafan tarihi sun ce shi “ɗan Ridda” ne.

Julian ya tsani waɗanda suke da’awar su Kiristoci ne. Wani dalili da ya sa ya yi hakan shi ne don ya ga yadda suka kashe mahaifinsa da kuma wasu danginsa sa’ad da yake ɗan shekara shida. ’Yan tarihi na coci sun ce Julian ya ƙarfafa Yahudawa su gina haikalinsu, don su mai da Yesu annabin ƙarya.a

Tabbas ne cewa Julian ya so ya sake gina haikalin, amma ba a san ko ya soma ginin ba. Kuma idan har ya soma da gaske, ba a tabbata ko me ya sa ya dakata ba. Amma, abin da aka sani shi ne cewa an kashe Julian kafin ya kai shekara biyu a sarauta, kuma shirinsa na sake gina haikalin ya bi ruwa.

a Yesu ya ce za a halaka haikalin a shekara ta 70, amma bai ce ba za a sake gina shi ba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba