Tambayoyi Daga Masu Karatu
Shin abin da Yesu ya faɗa a Matta 19:10-12 yana nufin cewa waɗanda suka zaɓi su kasance marasa aure sun samu baiwa na yin hakan ta hanyar mu’ujiza ce?
▪ Ka yi la’akari da yanayin da ya sa Yesu ya yi wannan maganar. Yesu ya bayyana ƙa’idodin Jehobah sarai a kan aure sa’ad da Farisawa suka yi masa tambaya game da kashe aure. Ko da yake Dokar ta ce mutum ya kashe aure idan ya gano “abin da ba daidai ba” a wurin matarsa, amma hakan ba asalin nufin Allah ba ne. (K. Sha 24:1, 20) Yesu ya ce: “Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci ba, ya kuwa auri wata, zina ya ke yi: shi kuma wanda ya auri sakakkiyar, zina ya ke yi.”—Mat. 19:3-9.
Sa’ad da almajiransa suka ji wannan, sai suka ce: “Idan zancen namiji da matatasa haka ya ke, ba ya dace a yi aure ba.” Yesu ya amsa ya ce: “Ba dukan mutane sun iya su karɓi wannan magana ba, sai waɗannan da an ba su. Gama akwai babani waɗanda aka haife su haka tun daga cikin uwassu; akwai kuma babani waɗanda aka maishe su babani da hannun mutane; akwai kuma babani waɗanda suka maida kansu babani sabili da mulkin sama. Wanda ya ke da iko shi karɓi wannan shi karɓa.”—Mat. 19:10-12.
Wasu sun zama bābānni domin an haife su hakan, wasu kuma don hatsari ko kuma domin sun naƙasa. Amma, wasu sun zaɓi su zama bābānni. Ko da sun isa yin aure, sun kame kansu ba su yi hakan ba “sabili da mulkin sama.” Kamar Yesu, sun ƙi yin aure domin su ba da kansu ga hidimar Mulki. Ba a haife su da wannan baiwa na zama marasa aure ba kuma ba a ba su ta mu’ujiza ba. Da gangan ne suka zaɓa wannan baiwar.
Sa’ad da manzo Bulus yake magana game da abin da Yesu ya ce, ya bayyana cewa dukan Kiristoci, da masu aure da marasa aure za su iya bauta wa Allah sosai. Amma ya ce, marasa aure waɗanda suka ‘tsaya sosai a kan shawarar zuciyarsu’ game da yanayinsu sun yi “abin da ya fi kyau.” Ta yaya suka yi hakan? Waɗanda suka yi aure suna raba lokacinsu da kuzarinsu don su faranta wa abokan aurensu rai kuma su kula da su. A wani ɓangare kuma, waɗanda ba su yi aure ba suna iya ba da kansu sosai ga hidimar Ubangiji ba tare da yin hakan ba. Suna ɗaukan yanayinsu a matsayin ‘baiwa’ daga Allah.—1 Kor. 7:7, 32-38.
Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Kirista ba ya samun baiwa na zama marar aure ta hanyar mu’ujiza. Maimakon haka, yana ƙin yin aure domin kada hankalinsa ya rabu biyu sa’ad da yake al’amura na Mulki. Mutane da yawa a yau sun tsai da shawara cewa ba za su yi aure ba don wannan dalilin, kuma yana da kyau mu riƙa ƙarfafa su.