Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/1 p. 3
  • Matsalolin da Mata Suke Fuskanta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matsalolin da Mata Suke Fuskanta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Shin Allah Ya Damu da Mata Kuwa da Gaske?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Mata Suna da Mutunci A Gaban Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Mene ne Matsayin Mata a Tsarin Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/1 p. 3

Matsalolin da Mata Suke Fuskanta

ZAHRA, wata ’yar shekara 15 da aka yi ƙaulinta a mujallar GEO ta ce: “Idan na ga yadda ake wulaƙanta mata, sai in ji da ma ni ba mace ba ce.”

MAGANA da yarinyar nan ta yi da aka rubuta a gefen dama ya bayyana mummunar hali da mata suka samu kansu a ciki a ko’ina a duniya, wato, yadda ake zalunta su da kuma nuna musu wariya. Ka yi la’akari da waɗannan misalan da ke gaba.

● Wariyar jinsi. A nahiyar Asiya, yawancin iyaye sun fi son su haifi yara maza a maimakon yara mata. Wani rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar a shekara ta 2011 game da mata a nahiyar ya nuna cewa zubar da ciki da kisan jarirai da kuma rashin kula ne sanadiyyar mutuwa ko ɓacēwar mata guda miliyan 134 daga al’ummar.

● Ilimi. A faɗin duniya, mata ne kashi 67 na mutane da ba su yi shekara huɗu a makaranta ba ko kuwa ba su yi makaranta ba sam.

● Tilasta wa mata yin jima’i. Sama da biliyan 2.6 na mata suna zama ne a ƙasashen da idan mutum ya yi jima’i da matarsa da ƙarfin da yaji ba laifi ba ne.

● Kiwon lafiya. Saboda rashin isashen tanadin kiwon lafiya a ƙasashe masu tasowa, kimanin mata 720 ne suke mutuwa a kowace rana sakamakon haɗarurrukan da suka shafi juna biyu da kuma haihuwa.

● Gādo. Ko da yake, mata ne suke noman sama da kashi hamsin na amfanin gona da ake samu a dukan duniya, amma ba su da ’yancin gādan gidaje ko kuma filaye.

Me ya sa ake danne wa mata hakkinsu? A wasu wurare mutane suna bin tsarin addini da ke ƙarfafa zaluntar mata, wasu kuma sun ɗauka cewa nuna wa mata wulaƙanci ba laifi ba ne. Wata jarida a ƙasar Faransa ta yi ƙaulin wata lauya daga Indiya mai suna Chandra Rami Chopra cewa: “Dukan addinai suna goyon bayan nuna bambanci ga mata.”

Mene ne ra’ayinka game da mata? Shin, kana ganin Littafi Mai Tsarki yana goyon bayan nuna bambanci ga mata kamar yadda wasu littattafan addini suke yi ne? Wasu suna ganin cewa wasu ayoyi daga Littafi Mai Tsarki sun faɗi hakan. Amma a gaskiya, yaya Allah da ya ba mu Littafi Mai Tsarki yake ganin mata? Ko da yake mutane da yawa sun ɗauki wannan batun da zafi, binciken abin da Littafi Mai Tsarki ya ce cikin hankali da natsuwa zai taimaka mana mu san gaskiyar.

[Wuraren da Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 3]

© G.M.B. Akash/Panos Pictures

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba