Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 7/1 pp. 26-27
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Amfani da Sunan Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Amfani da Sunan Allah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne Sunan Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Ka San Sunan Allah Kuma Kana Amfani da Shi Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Daraja Suna Mai Girma Na Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ma’anar Sunan Allah da Yadda Ake Amfani da Shi
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 7/1 pp. 26-27

Ka Koya Daga Kalmar Allah

Me Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Amfani da Sunan Allah?

Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.

1. Me ya sa Allah ya ba kansa suna?

Babu shakka, za ka so a kira ka da sunanka maimakon da laƙabi irin su “malam,” “malama,” “uwargida.” Suna yana sa a gane mutum. Ana kiran Allah da laƙabi kamar su “Ubangiji Mamallaki,” “Allah Mai Iko Duka,” da kuma “Mahalicci.” (Farawa 15:2; 17:1, NW; Mai-Wa’azi 12:1) Amma ya ba kansa sunan da zai taimaka mana mu ƙulla dangantaka da shi. Sunan Allah shi ne Jehobah ko Yahweh.—Karanta Fitowa 6:3.

Ko da yake yawancin mafassarin Littafi Mai Tsarki sun sauya sunan Allah da lakabi kamar su “Allah” da “Ubangiji,” wannan sunan ya bayyana kusan sau 7,000 a rubutu na dā na Littafi Mai Tsarki a Ibrananci. A bayyane yake cewa Allah yana son a san sunansa.—Karanta Ishaya 12:4.

2. Me ya sa sanin sunan Allah yake da muhimmanci?

Sanin sunan Allah yana nufin fiye da sanin yadda ake furta sunan kawai. Sanin sunan Allah yana nufin ƙulla dangantaka da shi. Sunan nan Jehobah yana nufin “Yana sa Ya Kasance.” Hakan tabbaci ne cewa Allah zai iya kasancewa duk wani abin da ake bukata don ya cika nufinsa. Saboda haka, sanin sunan Allah yana nufin gaskata cewa Allah zai cika alkawuran da ya yi. (Zabura 9:10) Bangaskiyar mutanen da suka san sunan Allah kuma suna amfani da shi tana sa su dogara ga Allah kuma su sa shi farko a rayuwarsu. Jehobah Allah zai kiyaye irin waɗannan mutanen.—Karanta Zabura 91:14, Littafi Mai Tsarki.

3. Me ya sa Allah yake so a sanar da sunansa?

Allah yana son mutane su san sunansa don hakan zai amfane su. Wannan zai sa su zama abokan Allah kuma su kasance da begen yin rayuwa har abada. Shi ya sa Jehobah yake son mu sanar da sunansa!—Karanta Yohanna 17:3; Romawa 10:13, 14.

Yesu ya sanar da sunan Allah ta wurin koya wa mutane hanyoyin Allah da dokokinsa da kuma alkawuransa. A yau, mabiyan Yesu suna ci gaba da gaya wa dukan al’umma sunan Allah. Suna yin hakan cikin haɗin kai a matsayin ‘jama’a domin sunan [Allah].’—Karanta Ayyukan Manzanni 15:14; Yohanna 17:26.

4. Ta yaya Allah zai ɗaukaka sunansa?

Jehobah Allah yana son ya ɗaukaka sunansa domin an ɓata sunan. Alal misali, wasu mutane sun ce ba ma bukatar mu yi masa biyayya domin ba shi ba ne ya halicci rai. Wasu kuma sun ce ba ya kula da mu kuma shi ne ya jawo wahalar da muke sha. Irin waɗannan mutanen suna ɓata sunan Allah. Amma ba za su ci gaba da yin hakan har abada ba. Allah zai halaka waɗanda suke ɓata sunansa.—Karanta Zabura 83:17, 18.

Jehobah zai ɗaukaka sunansa a lokacin da Mulkinsa zai kawar da sarautar ’yan Adam kuma zai kawo salama da kwanciyar rai ga ’yan Adam. (Daniyel 2:44) Ba da daɗewa ba, kowa zai san cewa Jehobah ne Allah na gaskiya.—Karanta Ezekiyel 36:23; Matta 6:9.

Mene ne ya kamata ka yi? Ka kusaci Allah ta wurin koyan Kalmarsa da kuma yin tarayya da mutanen da suke ƙaunarsa. A lokacin da Jehobah zai ɗaukaka sunansa, zai tuna da bayinsa masu aminci.—Malachi 3:16.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 1 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Hoto a shafi na 26]

Sunan Allah a rubutun dā na Littafi Mai Tsarki a Ibrananci

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba