‘Ka Kiyaye Zuciyarka!’
Taron Gunduma Na Shaidun Jehobah
JIGON RANAR JUMMA’A
‘Jehobah Yana Duba Zuciya’—1 SAMA’ILA 16:7.
JIGON RANAR ASABAR
“Daga Cikin Yalwar Zuciya Baki Ya Kan Yi Magana”—MATTA 12:34.
JIGON RANAR LAHADI
‘Ka Bauta Wa Jehobah da Sahihiyar Zuciya’—1 LABARBARU 28:9.
An ambata zuciya kusan sau dubu a cikin Littafi Mai Tsarki. A yawancin lokaci, Nassi yana magana ne game da zuciya ta alama ba zuciyar mutum ta zahiri ba. Mece ce zuciya ta alama? Wannan kalmar tana nufin halin mutum, wato, abin da mutum yake tunani da yadda yake ji da kuma abin da yake sha’awa.
Me ya sa ya kamata mu kiyaye zuciyarmu ta alama? Allah ya hure Sarki Sulemanu ya rubuta: “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa: gama daga cikinta mafitan rai su ke.” (Misalai 4:23) Ingancin rayuwarmu ta yanzu da kuma begen kasancewa a raye har abada a nan gaba ta dangana ne ga yanayin zuciyarmu ta alama. Me ya sa? Domin Allah ya san abin da ke zuciyarmu. (1 Sama’ila 16:7) Abin da ke zuciyarmu, wato, “ɓoyayyen mutum na zuciya,” shi ne zai nuna yadda Allah ya ɗauke mu.—1 Bitrus 3:4.
Ta yaya za mu kiyaye zuciyarmu? Za a amsa wannan tambayar dalla-dalla a taron gunduma na Shaidun Jehobah wanda za a fara a faɗin duniya daga wannan watan Mayu. Muna gayyatar ka ka halarci dukan ranaku uku na taron.a Abin da za ka koya zai taimaka maka ka yi abubuwan da za su faranta wa Allah rai.—Misalai 27:11.
[Hasiya]
a Domin ka san inda za a yi taron gunduma da ke kusa da kai, don Allah ka duba Yanar gizo na www.jw.org. Kuma kana iya tuntuɓar Shaidun Jehobah a yankinku ko kuma ka aika wasiƙa ga waɗanda suka wallafa wannan mujallar.
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 32]
Photo on right: Aus dem Fundus der MÜNCHNER OLYMPIAPARK GMBH, München