Ka Koya Daga Kalmar Allah
Me Ya Sa Kiristoci Suke Yin Baftisma?
Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Mece ce ma’anar baftismar da Kiristoci suke yi?
Yin baftisma hanya ce ta roƙon Allah ya amince mu ƙulla dangantaka mai kyau da shi. Saboda haka, ya dace Kirista ya yi baftisma sa’ad da ya koya game da Allah kuma ya zama almajirin Yesu, ba sa’ad da yake jariri ba. (Ayyukan Manzanni 8:12; 1 Bitrus 3:21) Muna zama almajiran Yesu ne sa’ad da muka koya game da shi kuma muka yi abin da ya umurce mu.—Karanta Matta 28:19, 20.
A zamanin manzannin Yesu, mutane da yawa sun ɗauki mataki nan da nan don su koya game da Allah da kuma Yesu. Alal misali, akwai wani mutumin da ya zama almajirin Yesu nan take sa’ad da ya koyi cewa mutuwar Yesu ta buɗe hanyar samun ceto. A yau ma, sahihan mutane da yawa sun zama mabiyan Yesu.—Karanta Ayyukan Manzanni 8:26-31, 35-38.
2. Me ya sa Yesu ya yi baftisma?
Yesu yana gab da kaiwa ɗan shekara 30 sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya nitsar da shi cikin ruwan Kogin Urdun. Baftismar Yesu tana wakiltar shawarar da ya yanke na yin nufin Allah. (Ibraniyawa 10:7) Hakan ya haɗa da ba da ransa a matsayin hadaya domin zunuban ’yan Adam. Yesu yana ƙaunar Ubansa, Jehobah, kuma ya yi masa biyayya tun yana sama kafin ya zo duniya.—Karanta Markus 1:9-11; Yohanna 8:29; 17:5.
3. Me ya sa ya kamata Kirista ya yi baftisma?
Yanayinmu ya bambanta da na Yesu, mu ajizai ne. Amma, hadayar da Yesu ya yi ta hanyar mutuwa ta sa mun ƙulla dangantaka mai kyau da Allah. (Romawa 5:10, 12; 12:1, 2) Hakan zai ba mu damar kasancewa cikin iyalinsa. (2 Korintiyawa 6:18) Ta yaya za mu samu wannan gatan? Za mu gaya wa Jehobah cikin addu’a cewa mun keɓe kanmu domin yin nufinsa har ƙarshen rayuwarmu. Bayan mun yi irin wannan keɓewar, za mu bayyana ta a fili ta wajen yin baftisma.—Karanta Matta 16:24; 1 Bitrus 4:2.
4. Me kake bukatar ka yi don ka cancanci yin baftisma?
Shaidun Jehobah suna koya wa dukan waɗanda suke son su kusaci Allah Littafi Mai Tsarki. Nazarin Littafi Mai Tsarki da halartan taron Kirista za su ƙarfafa ƙaunar da kake yi wa Allah da kuma bangaskiyar da kake da ita a gare shi. Za su kuma taimaka maka ka kasance da halaye masu kyau. Kasancewa da ƙauna da bangaskiya tare da halayen da suke faranta wa Allah rai zai taimake ka ka cika alkawarin da ka yi na bauta wa Jehobah har abada.—Karanta Yohanna 17:3; Ibraniyawa 10:24, 25.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 18 na wannan littafin Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.