Ana Son A San Amsoshi Game da Yesu
“Kusan kowane mutum yana da nasa ra’ayi game da [Yesu]. Ko da muna da bangaskiya sosai ko a’a, mukan tambayi kanmu, ‘Wane ne wannan mutumin?’”—MAWALLAFI STAN GUTHRIE.
MUTANE sun damu da sanin ko wane ne Yesu. Littattafai da fina-finan da aka yi game da Yesu ne suka fi ciniki a duniya. Duk da haka, mutane suna ci gaba da yin tambayoyi game da Yesu. Mutane suna da ra’ayoyi dabam-dabam game da Yesu.
A cikin ’yan shekarun da suka wuce, ’yan jaridu guda biyu sun ba mutane damar amsa wannan tambayar a cikin Intane, “Wane ne Yesu?” Ga wasu cikin amsoshin da suka ba da:
● “Babu shakka, shi rabbi (malami) ne wanda ya kafa misali mai kyau wajen nuna juyayi a rayuwarsa.”
● “Shi mutum ne kamar kowa amma ya yi rayuwa ta musamman.”
● “Babu wani tabbaci cewa Yesu ya taɓa wanzuwa.”
● “Yesu Ɗan Allah ne da aka haifa a duniya, ya mutu, kuma ya tashi daga matattu domin ya cece mu daga zunubanmu. Yana raye a yau, kuma zai sake dawowa duniya.”
● “Na gaskata cewa Yesu Kristi ne kaɗai ɗan Allah, shi alla ne da kuma mutum, duk a lokaci ɗaya.”
● “Labaran da aka rubuta game da Yesu tatsuniyoyi ne.”
Hakika, ba zai yiwu dukan ra’ayoyin nan su kasance gaskiya ba. Shin, akwai inda za mu iya samun tabbataccen amsoshin tambayoyinmu game da Yesu? Mawallafan wannan mujallar sun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce kuma shi kaɗai ne kawai zai gaya mana gaskiya game da Yesu.a—2 Timotawus 3:16.
A talifi na gaba, za mu tattauna amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya bayar na wasu tambayoyin da ake yi game da Yesu. Shi da kansa ya ce “duk wanda ya gaskata da shi” zai samu ceto. (Yohanna 3:16) Muna ƙarfafa ka ka bincika waɗannan amsoshin, bayan haka, ka yanke shawara ko kana bukatar ƙara sanin Yesu da kuma yadda za ka yi imani da shi.
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani, ka duba babi na 2 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, wanda ke da jigo “Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah.” Shaidun Jehobah ne suka wallafa.