Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 3/15 p. 32
  • “Don Allah Ka Ɗauke Mu Hoto”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Don Allah Ka Ɗauke Mu Hoto”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 3/15 p. 32

“Don Allah Ka Ɗauke Mu Hoto”

Bayan rana ta biyu na taron gunduma, wani ɗan’uwa mai suna Josué, da ke hidima a Bethel da ke ƙasar Meziko ya fita yawan buɗe ido a birnin Querétaro. Sai wasu ma’aurata Javier da matarsa Maru da suka fita yawon buɗe ido ma, suka ce Josué ya ɗauke su hoto. Da yake shi da abokinsa sun yi ado mai kyau kuma sun saka bajon su na taron gunduma, sai ma’auratan suka tambaye su ko suna dawowa ne daga sauke karatu ko kuma wani biki. Sai Josué ya bayyana cewa sun halarci taron gunduma na Shaidun Jehobah kuma ya gayyace su su halarci taron a ranar Lahadi.

Ma’auratan suka ji cewa za su ji kunya da yake ba su yi ado mai kyau ba da ya dace da irin wannan taron. Amma duk da haka, Josué ya gaya musu sunansa da kuma lambar wayar ofishin reshen da yake hidima.

Josué ya yi mamaki sosai sa’ad da Javier ya kira shi bayan wata huɗu. Ma’auratan sun halarci taron gundumar kuma suna son Shaidun Jehobah su ziyarce su a gidansu a Birnin Meziko. Ba da daɗewa ba, aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Javier da matarsa Maru, kuma suka soma halartar tarurruka. Watanni goma bayan wannan lokacin, suka zama masu shela da ba su yi baftisma ba. Ko da yake ma’auratan sun ƙaura zuwa birnin Toronto, a Kanada, suka ci gaba da samun ci gaba kuma suka yi baftisma.

Daga baya, Javier ya rubuta wa Josué wasiƙa yana bayyana masa dalilin da ya sa ya soma bauta wa Jehobah. “Jim kaɗan kafin mu halarci taron gundumar, ni da matata mun tattauna yadda za mu soma kyautata dangantakarmu da Allah. Sa’ad da muka ga yadda kuka yi ado mai kyau, mun yi zato cewa kun je wani biki na musamman ne. Yadda ka ba mu wurin zama a taron gundumar da taimaka mana mu buɗe namu Littafi Mai Tsarki da kuma halin waɗanda suka hallara ya burge mu sosai. Ba su yi ƙyamarmu ba da yake ba mu yi ado mai kyau ba.”

Kalamin Sarki Sulemanu mai hikima ya kasance gaskiya ga Josué. Sulemanu ya rubuta: “Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka; gama ba ka san wanda za ya yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuwa duk za su yi kyau baki ɗaya.” (M. Wa. 11:6) Shin za ka iya shuka iri ta wajen gayyatar mutane zuwa taron gunduma ko kuma su saurari jawabi ga jama’a? Kamar yadda Jehobah ya yi amfani da Josué da abokinsa don jawo Javier da matarsa Maru su soma bauta wa Jehobah, zai iya yin amfani da kai ma don taimaka wa waɗanda suke son su bauta wa Jehobah.—Isha. 55:1.

[Hoto a shafi na 32]

Daga hagu zuwa dama: Alejandro Voeguelin da Maru Pineda da Alejandro Pineda da Javier Pineda da kuma Josué Ramírez a ofishin reshen da ke ƙasar Meziko

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba