“Wannan Bishara Kuwa ta Mulki Za a Yi Wa’azinta”
“Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—MATTA 24:14.
Abin da Hakan Yake Nufi: Luka, marubucin Linjila ya ba da rahoto cewa Yesu “ya yi ta yawo a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azi, yana kawo bishara ta mulkin Allah.” (Luka 8:1) Yesu da kansa ya ce: “Dole in kai bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luka 4:43) Ya tura almajiransa su kai bishara zuwa garuruwa da ƙauyuka kuma daga baya ya umurce su: ‘Za ku zama shaiduna cikin iyakan duniya.’—Ayyukan Manzanni 1:8; Luka 10:1.
Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: Almajiran Yesu ba su ɓata lokaci ba wajen yin abin da Yesu ya gaya musu su yi. “Kowace rana fa, cikin haikali da cikin gida, ba su fāsa koyarwa da yin wa’azi kuma Yesu Kristi ne.” (Ayyukan Manzanni 5:42) Babu wanda ke cikin ikilisiya da bai yi wa’azi ba. Ɗan tarihi mai suna Neander ya lura cewa “Celsus wanda shi ne marubuci na farko da ya yi sūkar Kiristanci, ya yi ba’a domin mutanen da suka yi wa’azin linjila da himma sun haɗa da masu yin saka, masu gyaran takalma, dukawa, tare da jahilai.” A cikin littafinsa The Early Centuries of the Church, Jean Bernardi ya rubuta: Ya kamata “[Kiristoci] su riƙa yin wa’azi ga dukan mutane a ko’ina. A tituna da birane da gidaje. Suna yin wa’azin ne ko an saurare su ko a’a. . . . A duk faɗin duniya.”
Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? “Mutane da yawa a yau ba sa sha’awar bauta wa Allah domin coci-coci ba su ɗauki yin wa’azi da koyarwa da muhimmanci ba,” in ji firist ɗin cocin Anglican, David Watson. A cikin littafin da ya rubuta Why Are the Catholics Leaving?, José Luis Pérez Guadalupe ya yi rubutu a kan ayyukan ’yan cocin Evangelical da Adventist da dai sauran su kuma ya lura cewa “ba sa wa’azi gida-gida.” Amma ya rubuta game da Shaidun Jehobah, cewa: “Suna wa’azi gida-gida bisa tsari.”
Wani bayani mai muhimmanci kuma na gaskiya wanda Jonathan Turley wanda ke rubuce a littafin nan Cato Supreme Court Review, 2001-2002 ya ce: “Da zarar ka ambata Shaidun Jehobah, abin da zai zo zuciyar yawancin mutane shi ne masu wa’azi da suke zuwa gidajenmu a lokacin da ba ma so. Ga Shaidun Jehobah, yin wa’azi ƙofa-ƙofa don su rinjayi mutane su dawo addininsu ba batun ƙara yawan mabiya ba ne ba kawai, amma yin hakan yana da muhimmanci ga bangaskiyarsu.”
[Akwati a shafi na 9]
Su Wane Ne Suke da Alamun a Yau?
Daga ƙa’idodin Nassi da aka tattauna a jerin talifofin nan, a ganinka, su wa suke da alamun Kiristanci na gaskiya a yau? Ko da yake akwai dubban rukunoni da dariku da suke da’awar cewa su Kiristoci ne, kada ka mance abin da Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Ba dukan mai-ce mani, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aikata nufin Ubana wanda ke cikin sama.” (Matta 7:21) Sanin waɗanda suke yin nufin Allah, wato, waɗanda suke da alamun Kiristanci na gaskiya, da kuma yin tarayya da su zai kai ga samun albarka na har abada a Mulkin Allah. Don Allah ka tuntuɓi Shaidun Jehobah da suka kawo maka wannan mujallar, don ka samu ƙarin bayani game da Mulkin Allah da albarkar da zai kawo.—Luka 4:43.