Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 7/1 p. 5
  • “Su Ba na Duniya Ba Ne”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Su Ba na Duniya Ba Ne”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Ya Faru da Shaidun Jehobah a Holocaust​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Karin Batutuwa
  • Me ya sa Ake Kisan Kare Dangi? Me ya sa Allah ya Kyale hakan ya Faru?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • “Ba na Duniya Su Ke Ba”
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Tsakatsaki Na Kirista A Kwanaki Na Ƙarshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 7/1 p. 5

“Su Ba na Duniya Ba Ne”

“Duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne.”​—YOHANNA 17:14.

Abin da Hakan Yake Nufi: Babu ruwan Yesu da siyasa da kuma rikicin da mutane ke yi a zamaninsa, domin shi ba na duniya ba ne. Yesu ya ce, ‘da mulkina na wannan duniya ne, da ma’aikatana za su yi yaƙi, domin kada a bashe ni cikin hannun Yahudawa, amma yanzu mulkina ba daga nan yake ba.’ (Yohanna 18:36) Ya kuma umurci mabiyansa su guji halaye da maganganun da Kalmar Allah ta yi tir da su.—Matta 20:25-27.

Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: Jonathan Dymond, marubucin batutuwan da suka shafi addini, ya ce Kiristoci a ƙarni na farko sun “ƙi yin [yaƙi]; ko da hakan zai sa a kunyata su, a jefa su kurkuku, ko kuma a kashe su.” Sun gwammace su sha wahala da su yi yaƙi. Ɗabi’arsu ta kuma bambanta su da sauran mutane. An gaya wa Kiristoci: “Wannan kuwa suna maishe shi abin mamaki da ba ku yi gudu tare da su zuwa cikin haukar lalata irin tasu, suna aibatanku.” (1 Bitrus 4:4) Will Durant wani ɗan tarihi ya rubuta cewa “arna masu hauƙan son annashuwa suna jin haushin [Kiristoci] domin suna yin nagarta kuma suna da tsoron Allah.”

Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? Game da tsaka-tsakanci na Kirista, littafin nan New Catholic Encyclopedia ya ce: “Ƙin ɗaukan makami laifi ne.” Wani talifi a cikin jaridar Reformierte Presse ya ambata cewa rahoton da aka samo daga Hakkin ’Yan Afirka, wadda ƙungiya ce ta kāre hakkin ’yan Adam, ta tabbatar da cewa dukan coci ne suke da hannu a kisan ƙare-dangi da aka yi Ruwanda a shekara ta 1994, amma “ban da Shaidun Jehobah.”

Sa’ad da yake tattauna kisan ƙare-dangi da Nazi ta yi wa Yahudawa, malamin wata babbar makaranta ya koka cewa “babu wani rukuni ko ƙungiyar mutanen da ta fito ta yi Allah-wadai da irin ƙarya da rashin imani da kuma ayyukan masha’a da aka tabka.” Amma bayan ya tuntuɓi Gidan Tuna Tarihin Kisan Ƙare Dangi da ke Amirka, malamin ya rubuta cewa: “Na samu amsar tambayata.” Ya samu labarin cewa Shaidun Jehobah sun riƙe imaninsu duk da wahalar da suka sha.

Ɗabi’arsu a matsayin Kiristoci kuma fa? Jaridar nan U.S. Catholic ta ce: “Yawancin matasan da ke Katolika ba su amince ba da koyarwar cocinsu wadda ta ce laifi ne mutum ya yi jima’i kafin ya yi aure da kuma zama tare tsakanin mace da namiji ba tare da sun yi aure ba.” Ya yi kaulin wani dikon da ya ce: “Fiye da kashi 50 daga cikin mutanen da suka zo don a ɗaura musu aure, suna zama ne tare kafin a ɗaura musu aure.” Littafin nan The New Encyclopædia Britannica ya lura cewa Shaidun Jehobah “ba sa sakaci da batun kasancewa da ɗabi’a mai kyau.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba