Sun Yi Shelar Kalmar Allah da Gaba Gaɗi!
Ana bukatar gaba gaɗi sa’ad da ake fuskantar hamayya. Kiristoci na gaskiya sun nuna wannan halin. Kamar ’yan’uwanmu Kiristoci a ƙarni na farko, muna addu’a ga Jehobah don ya ba mu ruhunsa kuma ya taimaka mana mu yi maganar kalmarsa da gaba gaɗi.—A. M. 4:23-31.
Wani ɗan’uwa ya rubuta game da aikinmu na wa’azi a lokacin yaƙin duniya na ɗaya, kuma ya ce: “Bayin Allah da ƙwazo sun rarraba littafi na bakwai na Studies in the Scriptures, mai jigo The Finished Mystery. Ban da Littafi Mai Tsarki, babu littafin da aka fi rarrabawa kamar wannan littafin a lokacin. An fito da warƙar Kingdom News na 1 a shekara ta 1918. Bayan haka, aka fito da warƙar Kingdom News na 2, wadda ta bayyana dalilin da ya sa hukuma ta hana rarraba littafin nan The Finished Mystery. Bayan wannan an fito da warƙar Kingdom News na 3. Rukunin shafaffu masu aminci sun rarraba waɗannan littattafan sosai. Ana bukatar bangaskiya da gaba gaɗi don a rarraba warƙar Kingdom News.”
A yau, ana koya wa sababbi masu shelar Mulki yadda ake wa’azi, amma ba a ko da yaushe aka yi hakan a dā ba. Da yake tunani a kan abin da ya shaida a lokaci na farko da ya fita yin wa’azi a shekara ta 1922, wani ɗan’uwa ɗan ƙasar Poland da ke zama a Amirka ya rubuta: “Da yake ban san yadda zan gabatar da littattafan ba kuma ban iya Turanci sosai ba, sai na tsaya ni kaɗai a gaban ofishin wani likita kuma na ƙwanƙwasa ƙofarsa. Sai wata nas ta buɗe ƙofa. Ban zan taɓa manta abin da ya faru ba, domin ina da ƙwazo kuma ina jin tsoro. Yayin da nake buɗe jakata, dukan littattafai da suke cikin jakar suka zube a ƙafar nas ɗin. Ban san abin da na faɗa ba, amma na ba ta littafi. Sa’ad da na bar wajen, na samu gaba gaɗi kuma na ji cewa Jehobah ya albarkace ni. Na ba da ƙasidu da yawa a ranar a wannan wurin sana’a.”
“A misalin shekara ta 1933, ’yan’uwa da yawa sun yi amfani da motoci masu lasifika don su yaɗa saƙon Mulki,” in ji wata ’yar’uwa. A wani lokaci, da ita da wasu ma’aurata Shaidu suna wa’azi a wani yanki mai tudu na jihar California, Amirka. Ta ce, “ɗan’uwan ya kai mota mai lasifika a can saman tudun, kuma mun tsaya a ƙasa a cikin garin. Sa’ad da ya saka saƙon da aka ɗauka a tef, aka ji kamar muryar tana fitowa daga cikin sama. Mutanen garin sun yi ƙoƙari su gan ɗan’uwan, amma hakan bai yiwu ba. Bayan da saƙon ya ƙare, muka tara mutanen kuma muka yi musu wa’azi. Na yi hidima tare da wasu motoci biyu masu lasifika kuma yawancin mutane ba sa son su ji saƙon. Amma dole ne su ji saƙon sarai a gidajensu tun da yake saƙon yana fitowa daga motoci masu lasifika. Mun ga cewa Jehobah a ko da yaushe yana sa a yi amfani da hanyar da ta dace don a yaɗa saƙon a lokacin da ya dace. Wannan hanyar yaɗa bishara tana bukatar mutum ya kasance da gaba gaɗi sosai, amma ta cim ma manufarta kuma an ɗaukaka sunan Jehobah.”
A tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1949 mun yi amfani da garmaho da jawaban Littafi Mai Tsarki da aka ɗauka a faifai a hidimarmu. Wata ’yar’uwa Kirista ta faɗa abin da ya faru a lokacin: “Akwai wata rana da wata matashiya take hidimar ƙofa ƙofa da garmaho. Bayan da ta buga faifan a wata ƙofa, maigidan ya yi fushi sosai har ya yi kwallo da garmaho ɗin. Amma babu faifai guda da ya karye. Maza uku da suke cin abincin rana a cikin wata babbar mota sun ga abin da ya faru, sai suka gayyaci ’yar’uwar ta saka musu saƙon su saurara, kuma suka karɓi littattafai daga hannunta. Wannan ya sa ba ta damu da wulakanci da aka mata ba.” Ana bukatar ƙarfin zuciya don a jimre da irin waɗannan gwaje-gwaje.
’Yar’uwar ta daɗa: “Na tuna lokacin da muka soma ba da mujallu a kan titi a shekara ta 1940. Da farko za a yi sanarwa cewa za a yi hakan. ’Yan’uwa maza da mata za su kasance cikin layi guda su riƙa tafiya a gefen hanya suna ɗauke da alamu da aka rubuta ‘Religion Is a Snare and a Racket’ [Addini Tarko ne da kuma Hayaniya] da kuma ‘Serve God and Christ the King’ [Ku Bauta wa Allah da kuma Kristi Sarki.] Kuma ana rarraba wa mutane warƙoƙi kyauta. Ana bukatar gaba gaɗi don a saka hannu cikin waɗannan fannoni na wa’azi, amma sun cim ma manufarsu na sa mutane su san game da sunan Jehobah da kuma mutanensa.”
“Ba da mujallu a kan titi a ƙananan ƙauyuka yana da wuya sosai,” in ji wata ’yar’uwa. “Hakan gaskiya ne sa’ad da ake tsananta wa Shaidu sosai. . . . Ana bukatar gaba gaɗi sosai don a tsaya a gefen hanya riƙe da mujallu kuma ana faɗin kalmomi da aka ce mu riƙa amfani da su. Amma duk da haka, da ƙyar mu fasa fita yin wa’azi a ranar Asabar guda. Wasu lokatai, mutane sukan yi fara’a. A wasu lokatai kuma, rukunin mutane masu fushi sukan taru mana, kuma a jifa jifa mukan bar wajen don mu guji wulakanci daga wurin wannan rukunin.”
Shaidun Jehobah sun cika hidimarsu da gaba gaɗi duk da tsanantawa da suka fuskanta a lokacin Yaƙin Duniya na biyu. A kamfen da aka yi cikin kwanaki 43, daga ranar 1 ga Disamba, 1940 zuwa 12 ga Janairu, 1941, kusan masu shela 50,000 a Amirka sun rarraba ƙasidu kusan miliyan takwas a lokacin da aka kira “Courage” Testimony Period. (Zamanin Yin Wa’azi da Gaba Gaɗi).
Tsofaffi da yawa a cikin ƙungiyar Allah sun tuna da ƙalubalen da suka fuskanta a dā da suke bukata su kasance da gaba gaɗi sosai. Wasu sun tuna cewa cikin shekaru da yawa, sun maimaita kalami da ya nuna halinsu na gaba gaɗi, Bari mu ci gaba da wa’azi da ƙwazo har ƙarshe! Ba a san har yawan yadda za a yi wa’azi da Allah ya ce mu yi ba kafin ƙarshen wannan mugun zamanin. Amma da taimakon Allah, za mu ci gaba da shelar kalmar Jehobah da bangaskiya da kuma gaba gaɗi.
[Bayanin da ke shafi na 9]
Ana bukatar gaba gaɗi don a yi aikin wa’azin Mulki