Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 8/15 p. 22
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Rahoton 2017
    Rahoton Hidima na Shaidun Jehobah a fadin duniya na 2017
  • Rahoton 2018
    Rahoton Hidima na Shaidun Jehobah a fadin duniya na 2018
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 8/15 p. 22

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Yaya za mu fahimci adadin rahoton hidima na shekara-shekara?

Kowace shekara muna ɗokin karanta rahoto na aikin wa’azi da aka wallafa a cikin Yearbook da kuma Hidimarmu Ta Mulki ta Fabrairu. Muna farin cikin karanta abin da mutanen Jehobah suka cim ma a dukan duniya a aikin wa’azin Mulkin Allah da kuma koya wa mutane game da ita. Amma don a fahimci ainihin abin da rahoton yake nufi, muna bukatar bayyana ma’anar wasu laƙabi da adadi. Ga wasu misalai.

Shekarar hidima. Shekarar hidima tana somawa daga watan Satumba kuma tana ƙarewa a Agusta. Rahoton da ake sakawa cikin Hidimarmu Ta Mulki tana ɗaukan rahoton shekarar da ta wuce. Alal misali, Hidimarmu Ta Mulki ta Fabrairu, 2011 tana ɗauke da rahoton shekarar hidima ta 1 ga Satumba 2009, zuwa 31 ga Agusta, 2010.

Ƙoli da kuma abirejin masu shela. Masu shela su ne Shaidu da suka yi baftisma da kuma wasu da aka amince cewa su riƙa yin wa’azin bishara ta Mulki. Ana ɗauko adadin “ƙolin masu shela” daga wata na shekarar hidimar da rahoton ya fi yawa. Adadin zai iya haɗa da wasu rahotanni da suka makara. “Abirejin masu shela” yana nufin adadin masu shela da suke ba da rahoton sa’o’in da suka yi a aikin wa’azi kowanne wata.

Jimillar sa’o’i. Hidimarmu Ta Mulki ta 2011 ta nuna cewa Shaidun Jehobah sun yi wa’azi na fiye da sa’o’i biliyan ɗaya da rabi. Amma wannan jimillar ba ta haɗa da dukan sa’o’in da muka yi muna bauta wa Jehobah ba. Alal misali, bai haɗa da sa’o’in da dattawa suka yi amfani da su suna ƙarfafa ’yan’uwa a cikin ikilisiya ba. Bai kuma haɗa da lokacin da muke amfani da shi don halartar tarurruka don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kan abin da muka koya ba.

Kuɗin da aka kashe. A shekarar hidima ta 2010, Shaidun Jehobah sun kashe fiye da dala miliyan 155 wajen kula da majagaba na musamman da masu wa’azi a ƙasashen waje da kuma masu kula masu ziyara a wuraren aikinsu na hidimar fage. Amma wannan bai haɗa da kuɗaɗen da ake kashewa don wallafa Littafi Mai Tsarki da littattafai da kuma mujallu ba. Kuma bai haɗa da kuɗaɗen da ake kashewa don kula da ’yan’uwa fiye da 20,000 da suke aiki a gidajen Bethel a dukan duniya ba.

Masu cin isharar. Wannan adadin dukan Shaidu ne da suka yi baftisma da suke cin gurasa da kuma shan ruwan inabi a lokacin da ake Tuna Mutuwar Yesu. Amma wannan adadin ba daidai adadin shafaffu da suke duniya ba. Alal misali, wasu suna iya kasancewa da ra’ayin da bai dace ba game da zuwan sama domin abin da suka yi imaninsa a dā ko kuma domin sun ɗan taɓu. Saboda haka, ba zai yiwu ba mu san ainihin adadin shafaffu da ke duniya kuma ba ma bukatar mu san su ba. Hukumar Mulki ba ta ajiye tsarin sunayen dukan mutanen da suke cin gurasa da shan ruwan inabi a lokacin Tuna Mutuwar Yesu ba.a

Abin da muka sani shi ne cewa wasu cikin shafaffu “bayin Allahnmu” za su kasance a duniya sa’ad da ƙunci mai girma ya soma. (R. Yoh. 7:1-3) Yayin da suke duniya shafaffu suna aiki tuƙuru a wa’azi da kuma koyarwa. Rahoto na shekara-shekara ya nuna mana abin da mutanen Jehobah a dukan duniya suke yi a wannan aiki mafi muhimmanci a tarihin ’yan Adam.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Wakili Mai Aminci da Hukumarsa ta Mulki,” a cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Yuni, 2009, shafi na 24.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba