Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 8/15 p. 17
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Annabce-annabce Game da Almasihu Sun Nuna Cewa Yesu Ne Almasihu Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Annabci Game da Almasihu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ta Hanyar Almasihu Ne Allah Zai Kawo Ceto
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Sun Jira Zuwan Almasihu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 8/15 p. 17

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Shin zai yiwu a faɗi daidai yawan annabce-annabce da aka yi game da Almasihu da suke cikin Nassosin Ibrananci?

Yin nazarin Nassosin Ibrananci sosai ya sa mu san annabce-annabce da yawa da suka cika game da Yesu Kristi. Waɗannan annabce-annabcen sun faɗi dalla-dalla game da tasowar Almasihu da lokacin da zai soma hidimarsa da abubuwan da zai yi da yadda za a bi da shi da kuma matsayinsa a shirin Jehobah Allah. Haɗa dukan waɗannan bayanan za su taimaka mana mu san cewa Yesu ne Almasihun da aka yi alkawarinsa. Amma dai, ya kamata a mai da hankali idan ana neman sanin daidai yawan annabce-annabcen da aka yi game da Almasihu da suke cikin Nassosin Ibrananci.

Ba kowa ba ne ya amince da annabcin da aka ce ya cika a Almasihu ko wanda bai cika a kan Almasihu ba. Alfred Edersheim ya faɗi a cikin littafin nan da ya wallafa The Life and Times of Jesus the Messiah cewa littattafan Yahudawa na dā sun ware shafuffuka na furuci 456 a Nassosin Ibrananci cewa suna magana game da Almasihu, ko da yake da yawa cikinsu ba su ambata Almasihu ba. Bincika waɗannan shafuffuka na furucin 456 sun sa an yi tambaya ko wasu cikinsu annabci ne game da Yesu Kristi. Alal misali, Edersheim ya ce Yahudawa sun ɗauki Farawa 8:11 a matsayin annabci game da Almasihu. Sun fahimci cewa “ganyen da kurciyar nan ta kawo daga Dutsen Almasihu ne.” Mawallafin ya kuma ambata Fitowa 12:42. Da yake bayyana yadda Yahudawa ba su fahimci wannan annabci ba, ya ce: “Kamar yadda Musa ya fito daga hamada, haka kuma Almasihun zai fito daga Roma.” Babu shakka, zai kasance wa ɗalibai da yawa da wasu mutane wuya su fahimci waɗannan ayoyi biyu da kuma bayanin da ba daidai ba da aka yi a kan Yesu Kristi.

Ko da mun mai da hankalinmu ga annabce-annabcen da suka cika a kan Yesu Kristi, yana kasancewa da wuya mu gaskata cewa suna da ainihin adadi. Alal misali, Ishaya sura ta 53 tana ɗauke da annabce-annabce da dama game da Almasihu. Ishaya 53:2-7 ya annabta: “Ba shi da wani fasali . . . Abin reni ne, yasashe ne a wurin mutane . . . Da kayan cutarmu ya nawaita . . . Sabili da laifofinmu ne aka yi masa rauni . . . Kamar ɗan rago da a ke kai wurin yanka.” Shin za a iya ɗaukan duk wannan furucin da aka yi a Ishaya sura ta 53 a matsayin annabci guda, ko kuwa kowanne cikin waɗannan annabci game da Almasihu a matsayin annabce-annabce dabam-dabam?

Ka yi la’akari ma da abin da Ishaya 11:1 ya ce: “Daga cikin tsutsugen Jesse toho za ya fito, reshe kuma daga cikin sauyoyinsa za ya bada ’ya’ya.” Wannan annabcin ya sake bayyana da kalamai iri ɗaya a aya ta 10. Shin ya kamata mu ɗauki waɗannan ayoyi biyu a matsayin annabce-annabce dabam-dabam guda biyu ne ko kuwa annabci ɗaya da aka maimaita? Yadda aka fahimci Ishaya sura 53 da kuma Ishaya sura 11 zai shafi adadin annabce-annabcen da suka yi magana game da Almasihu sosai.

Saboda haka, zai dace mu guji faɗin ainihin adadin annabce-annabcen da suka yi magana game da Almasihu da ke Nassosin Ibrananci. Ƙungiyar Jehobah ta wallafa littattafai da yawa da suke ɗauke da annabce-annabce da yawa da suka yi magana game da Yesu da kuma yadda suka cika.a Waɗannan littattafan za su taimaka mana kuma za su ƙarfafa mu sa’ad da muke yin nazari na kanmu da nazari na iyalinmu da kuma sa’ad da muke hidimar fage. Ƙari ga haka, annabce-annabce game da Almasihu da yawa da aka yi ko nawa ne adadinsu, suna ba mu tabbaci sosai cewa Yesu ne Kristi ko kuma Almasihu.

[Hasiya]

a Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shafi na 200.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba