“Mai Kula Mai Kyau da Kuma Aboki Ƙaunatacce”
JOHN (JACK) BARR, wanda ya yi hidima a matsayin ɗaya cikin Hukumar Mulki na Shaidun Jehobah ya gama hidimarsa na duniya a safiyar ranar Asabar, 4 ga Disamba, 2010. Yana da shekaru 97 da haihuwa. An kwatanta shi a matsayin “Mai kula mai kyau da kuma aboki ƙaunatacce.”
An haifi Ɗan’uwa John Barr a birnin Aberdeen da ke ƙasar Scotland, shi ne auta cikin yara uku. Iyayensa shafaffu ne. Ɗan’uwa Barr yana magana cikin farin cikin sau da yawa game da yadda rayuwar iyalinsa ta soma; ya nuna godiya sosai game da fitacciyar misalin da iyayensa ƙaunatattu suka kafa masa.
Da ya fara balaga, ya yi wa matashi John wuya ya yi magana da baƙi. Amma dai, ya yi ƙoƙari sosai don ya shawo kan matsalar, kuma da yake ɗan shekara 14, a wata ranar Lahadi da rana a shekara ta 1927, ya sanar wa mahaifinsa cewa yana shirye ya fita wa’azi na gida gida tare da shi. Somawar hidimarsa ga Jehobah na shekaru da yawa ke nan. Daga wannan ranar har mutuwarsa, Ɗan’uwa Barr ya kasance mai wa’azin bishara da ƙwazo.
Wani mummunar hatsari da ya kusan kashe mahaifiyarsa ya sa matashi John ya yi tunani sosai game da ma’anar rayuwa, kuma a shekara ta 1929 ya keɓe kansa ga Jehobah, ya nuna hakan ta wurin yin baftisma a shekara ta 1934. Sa’annan a shekara ta 1939, ya zama ɗaya daga cikin iyalin Bethel da ke Landan, a ƙasar Ingila. Da haka ne ya soma hidima ta cikakken lokaci da ya kai shekaru 71.
Sa’ad da ya auri Mildred Willett, a ranar 29 ga Oktoba a shekara ta 1960, wadda ta daɗe tana hidimar majagaba da ƙwazo da kuma wa’azi a ƙasar waje, Ɗan’uwa Barr ya shiga abin da ya kira “dangantaka na musamman mai tamani.” An san Ɗan’uwa da ’Yar’uwa Barr a matsayin ma’aurata da abin koyi ne da kuma masu ibada, kuma sun kasance hakan har watan Oktoba, na shekara ta 2004 sa’ad da Mildred ta kammala hidimarta na duniya. Ɗan’uwa da ’Yar’uwa Barr suna karanta Littafi Mai Tsarki tare kowace rana a matsayinsu na ma’aurata.
Waɗanda suka san John Barr za su riƙa tunawa da mutumi mai ba da shawara mai kyau, a ko yaushe yana nuna daidaici da alheri da kuma ba da gargaɗi bisa Nassi. Shi mai aiki tuƙuru ne da mai yin la’akari da mai kula mai ƙauna da kuma aboki amintacce. Kalamansa da jawabansa da kuma addu’o’insa sun nuna cewa shi mai ruhaniya ne sosai kuma yana da dangantaka na kud da kud da Jehobah.
Ko da yake mun yi rashin Ɗan’uwa Barr, mun yi farin ciki da ya sami gatar da yake ɗokin samu kuma sau da yawa yana magana game da shi, wato, kyautar rai marar mutuwa. Duk abin da yake son samu ke nan.—1 Kor. 15:53, 54.a
[Hasiya]
a Don samun labarin John E. Barr, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga watan Yuli, 1987, shafuffuka na 26 zuwa 31 na Turanci.