Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .
Shaidun Jehobah suna karɓan jinya kuwa?
▪ Yesu ya ce “lafiyayyu ba su da bukatar mai-magani, sai masu-ciwo.” (Matta 9:12) Da haka, ya nuna cewa Nassi bai hana neman jinya daga ƙwararrun masu kiwon lafiya ba. Saboda haka, Shaidun Jehobah suna karɓan magani tare da jinya cike da farin ciki. Suna son su kasance da cikakkiyar lafiya kuma su tsawaita ransu. Hakika, kamar Luka, wanda Kirista ne a ƙarni na farko, wasu a cikin Shaidun Jehoba likitoci ne.—Kolosiyawa 4:14.
Amma, Shaidun Jehobah ba sa karɓan jinyar da ta saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ba sa karɓan ƙarin jini, domin Littafi Mai Tsarki ya haramta karɓan ƙarin jini don kiyaye jiki. (Farawa 9:4; Levitikus 17:1-14; Ayyukan Manzanni 15:28, 29) Kalmar Allah ta kuma haramta hanyoyin jinyar da suka ƙunshi yin amfani da “tsafi” ko sihiri.—Ishaya 1:13, NW; Galatiyawa 5:19-21.
Ƙwararrun masu kiwon lafiya da yawa suna tanadar da magunguna da ba su saɓa wa mizanan Littafi Mai Tsarki ba. Irin waɗannan jinyar da Shaidu da yawa suke karɓa, suna da kyau sosai fiye da jinyar da suka saɓa wa abin da Allah yake bukata.
Babu shakka, akwai ra’ayoyi da yawa idan ya zo ga batutuwan lafiyar jiki. Abin da ya amfane wani wataƙila ba zai amfane wani ba. Shi ya sa, mutanen da suke biɗar cikakken gwaji da kuma magani suna iya tuntuɓar likitoci fiye da guda.—Misalai 14:15.
Kowane Mashaidi yana da nasa zaɓin game da jinya. Kalmar Allah ta ba da damar yin zaɓi bisa lamiri a tsakanin Kiristoci idan zaɓin bai saɓa wa dokar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba. (Romawa 14:2-4) Saboda haka, ya kamata kowa ya bincika duk wata shawarar da aka ba shi game da jinya kuma ya tabbata cewa hakan bai saɓa wa lamirin shi ko ita da Littafi Mai Tsarki ya koyar ba.—Galatiyawa 6:5; Ibraniyawa 5:14.
Mashaidi zai ɗauki kowace shawarar da zai tsai da kamar shi direba ne da ya kusanci inda hanyoyi suka haɗu. Idan ya bi motocin da ke gabansa kuma ya wuce mahaɗar hanyar a guje, hakan zai iya jawo mugun haɗari. Direba mai hikima zai dakata kuma ya duba hanya sosai kafin ya wuce. Hakazalika, Shaidu ba sa hanzarin yanke shawara game da jinya ko kuma su bi ra’ayin jama’a cikin jahilci. Maimakon haka, suna yin tunani sosai a kan zaɓin da suke da shi kuma su bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kafin su tsai da shawara.
Babu shakka, Shaidun Jehobah suna yaba wa masu jinya sosai saboda aiki mai wuya da ba da kai da suke yi. Suna kuma godiya saboda sauƙin da masu kiwon lafiya suke tanadarwa.