Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
MENE ne ya motsa wani tsohon sojan tawaye kuma ɓarawo ya canja irin rayuwar da yake yi? Me ya sa wata zakarar karati ta canja makasudanta a rayuwa? Ta yaya ne imanin da wani uba yake da shi a ɗansa ya samu sakamako mai kyau? Ka karanta waɗannan labaran don samun amsoshin.
“Ina farin ciki, duk da munanan abubuwan da na aikata a dā.”—GARRY P. AMBROCIO
SHEKARU: 47
ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: PHILIPPINES
TARIHI: SOJAN TAWAYE
TARIHI NA NA DĀ: Na girma ne a wani ɗan ƙaramin gari mai suna Vintar. Babban kwarin da muke zaune yana kewaye ne da manyan koren duwatsu, rafuka masu tsabta, da iska mai daɗi. Duk da cewa wuri ne mai kyau, rayuwa ba ta da sauƙi. Mutane suna satar dabbobinmu kuma su shiga gidanmu su yi sata.
Sa’ad da nake matashi, ina mugun shan giya tare da abokaina, ina shan taba sigari, kuma ina yin sata don na biya bukatuna na mugun abin da nake yi. Akwai lokacin da na saci lu’ulu’un kakata. Sojoji sun yi zargin cewa ina cikin wani rukunin ’yan tawaye mai suna New People’s Army (NPA) wato, (Sojojin Sababbin Mutane) kuma sun sha yi mini bugun kawo wuƙa. A sakamakon haka, na yanke shawarar shiga rukunin ’yan tawayen. Na yi shekaru biyar cikin manyan duwatsu tare da sojojin NPA. Rayuwar tana da wuya. Mun kasa zama waje guda, domin muna guduwa daga sojojin. Daga baya, na gaji da ɓoyewa a cikin manyan duwatsu, kuma na miƙa kaina ga gwamnan Ilocos Norte. Ya bi da ni yadda ya kamata, har ma ya taimaka mini na samu aiki mai kyau. Duk da haka, ban ƙyale mugayen halaye na na dā ba, ina shiga gidajen mutane in yi sata kuma in ci mutane da burga.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWANA: Akwai wata mata a wajen aikina mai suna Loida wadda ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah ce. Ta haɗa ni da Jovencio, kuma ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Amma rayuwar da nake yi a dā ta zama jinina. A lokacin da Jovencio yake nazarin Littafi Mai Tsark da ni ne kawai ba na shan taba, kuma har ila ina yin haramtattun ayyuka. A ƙarshe, ’yan sanda suka kama ni ina karya doka, kuma na yi watanni 11 a cikin kurkuku. A wannan lokacin, na yi addu’a ga Jehobah, na nemi taimakonsa. Na roƙe shi ya gafarta mini kuma ruhunsa mai tsarki ya yi mini ja-gora kuma ya ƙarfafa ni.
Bayan wani lokaci, wani daga cikin Shaidun Jehobah ya ziyarce ni a kurkuku kuma ya kawo mini Littafi Mai Tsarki. Na karanta shi kuma na koyi cewa Jehobah mai rahama ne mai ƙauna kuma yana gafarta zunubai. Na fahimci cewa Jehobah yana nuna mini rahama kuma ya ba ni zarafin koyan hanyoyinsa. Na roƙe shi ya ba ni ƙarfin daina halaye na marar kyau. Abin da na karanta a Misalai 27:11 ya shafe ni sosai. Na ɗauki ayar nan kamar Jehobah ne yake yi mini magana kai tsaye. Ayar ta ce: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.”
Bayan na fito daga kurkuku, na sake soma nazarin Littafi Mai Tsarki da nake yi da Shaidu, na soma halartan taronsu, kuma na soma amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki a rayuwana. Daga baya, da taimakon Jehobah, na daina dukan mugun halayen da nike yi a dā kuma na keɓe rai na ga Jehobah Allah.
YADDA NA AMFANA: Duk da munanan abubuwan da na aikata a dā, a yanzu ina farin ciki. Ko da yake a dā ni bawa ne ga munanan halaye, a yanzu na zama sabon mutum. (Kolosiyawa 3:9, 10) A yau, daraja ne a gare ni in yi tarayya da mutanen Jehobah masu tsabta kuma in taimaka wa mutane su san Allahnmu maɗaukaki, Jehobah.
“Na so in waƙilci ƙasar Brazil.”—JULIANA APARECIDA SANTANA ESCUDEIRO
SHEKARU: 31
ƘASAR DA AKA HAIFE TA: BRAZIL
TARIHI: ƘWARARRIYAR ’YAR KARATI
TARIHI NA NA DĀ: Na girma ne a garin Londrina. Ko da yake yawancin mutanen da ke zaune a garin talakawa ne, garin yana da tsabta ga kuma kwanciyar hankali. Sa’ad da na kai ’yar shekara goma, wā na ya ƙarfafa ni in riƙa binsa muna wasan tsalle-tsalle na karati tare, wato, “yin wasa da hannuwa da ƙafafu.” Baba baya son in koyi wannan wasan amma daga baya ya ƙyale ni.
Na horar da kaina sosai kuma sau da yawa na zama zakarar wasan karati a jihar Parana. Daga baya, na zama zakarar ƙasa sau da yawa, kuma a shekara ta 1993, an naɗa ni zakarar ƙasar Brazil. Na so na shiga manyan wasanni na ƙasashe. Amma, iyalinmu talakawa ne kuma ba su da kuɗin aika ni ƙasar waje.
Fata na shi ne cewa za a saka wasan karati a wasannin Olampik, kuma abin da ya faru ke nan. Ina son in wakilci ƙasar Brazil a Wasannin Olampik, saboda haka na horar da kaina sosai kuma na samu ɗaukan nauyin da ya sa na shiga gasa a ƙasar Faransa, Vietnam, Koriya ta Kudu, da Japan, da kuma Wasannin Amirka ta Kudu. Buri na na gaba shi ne shiga wasannin nan mai suna Pan American Games, kuma na yi ƙoƙari sosai har aka zaɓe ni in kasance ɗaya daga cikin mutane uku da za su yi gasa a wannan wasan a Santo Domingo, a Jamhuriyar Dominikan, a shekara ta 2003.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: A shekara ta 2001, ni da saurayi na mun haɗu da Shaidun Jehobah, kuma suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mu. Da farko, ba na damuwa da nazarin sosai. Ba na samun zarafin saurarawa saboda yawan gajiya kuma barci yakan ɗauke ni a lokacin nazarin. Duk da haka, abin da nake koya ya shiga zuciyata, kuma hakan zai bayyana a babban gasa da zan yi nan gaba.
Domin an zaɓe ni in kasance cikin ’yan wasan Pan American Games, masu horar da ’yan wasan karati sun sa na shiga gasan da ake yi kafin babban wasa. Sa’ad da lokaci ya yi da zan shiga in yi faɗa, na tsaya cik, na kasa motsi. Farat ɗaya, na fahimci cewa bai kamata Kirista ya yi faɗa da wasu ba, har da inda ake yin wasa! Dokar da ke cikin Littafi Mai Tsarki na “ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka” ta faɗo zuciyata. (Matta 19:19) Sai kawai na juya kuma na fice daga fagen wasan ba tare da nadamar yin hakan ba. Mutane suka buɗe baki suna kallona.
Sa’ad da na isa gida, na zauna kuma na soma tunanin abin da zan yi da rayuwata. Na ɗauki wata mujallar da Shaidu suka wallafa wadda ta tattauna abin da Allah yake bukata daga gare mu. A cikinta na ga inda aka yi nuni ga Zabura 11:5, wadda ta ce game da Jehobah: “Mai-mugunta da mai-son zalunci ransa yana ƙinsu.” Waɗannan kalaman na mai zabura sun shiga zuciyata, kuma na yanke shawarar daina yin wasan karati.
Masu horar da ni a wasan karati ba su yi farin ciki ba. Sun yi ƙoƙarin sa in canja zuciyata ta wajen gaya mini cewa ni ce zakarar ƙasar gaba ɗaya kuma na kusan kai ga yin gasa a Wasannin Olampik. Amma na riga na yanke shawara.
A wannan lokacin, ni da saurayi na mun riga mun yi aure. Ya riga ya soma bin Shaidu zuwa aikin wa’azin da suke yi. Yana dawowa gida cike da farin ciki kuma ya gaya mini dukan tattaunawar da ya yi da mutane. Na san cewa idan ina so in samu irin wannan gatan, dole ne in yi canje-canje a rayuwata. Na yi murabus daga addinina na dā kuma daga baya na cancanta na zama Mashaidiyar da ta yi baftisma.
YADDA NA AMFANA: Ni da mijina muna farin ciki sosai kuma kanmu a haɗe domin muna ƙoƙarin yin amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki a aurenmu. Ina jin daɗin tallafa masa a kulawar da yake yi wa ikilisiyar da muke. Zan iya ƙoƙartawa in ci zinari a Wasannin Olampik kuma in yi suna. Amma na ga cewa babu wani abin da wannan duniyar marar adalci za ta iya ba da wa da za a iya kwatantawa da gatan bauta wa Jehobah Allah.
“Mahaifina bai taɓa fid da rai a kaina ba.”—INGO ZIMMERMANN
SHEKARU: 44
ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: JAMUS
TARIHI: MAI TSARO A GIDAN RAWA
TARIHI NA NA DĀ: An haife ni a cikin iyalin da ba kowa ba ne ke bauta wa Jehobah ba a wani gari mai suna Gelsenkirchen, inda ake haƙar kwal. Babana Mashaidin Jehobah ne. Amma Mama tana hamayya da ƙoƙarce-ƙoƙarcensa na yin renon ni, wa na, da yayye na mata biyu bisa ga imanin addininsa. Yana aikin tuƙa manyan motoci har tsawon awa goma ko fiye da haka a kowace rana. A yawancin lokaci, yana soma aiki ne da ƙarfe biyu ko uku na dare. Duk da haka, yana koyar da mu a kowane lokaci don mu kafa dangantaka da Jehobah. Amma na yi watsi da duk ƙoƙarce-ƙoƙarcensa.
Sa’ad da na kai ɗan shekara 15, sai na soma jin cewa duk na bi na gaji da taron addinin da yake kai ni, sai na yi tawaye. Bayan shekara ɗaya, na shiga ƙungiyar ’yan dambe. Cikin shekaru biyun da suka bi bayan hakan, na yi abubuwan da suka ta da wa babana hankali sosai. Na tashi daga gidanmu sa’ad da na kai ɗan shekara 18.
Ina bala’in son wasanni kuma ina horar da kaina har sau shida a kowane sati wajen yin dambe da kuma ɗaga ƙarfe mai nauyi. A ƙarshen kowane mako, ni da abokaina muna zuwa gidajen rawa. Akwai lokacin da na yi faɗa da wani mugun mutum a gidan rawa kuma na ba shi kashin tsiya. Sa’ad da mutumin da ke da gidan rawan ya ga abin da ya faru, nan da nan ya ce zai ɗauke ni aiki a matsayin mai tsaro. Da na ga cewa kuɗin da zai ba ni yana da tsoka, sai na karɓi aikin.
A ƙarshen kowane mako, ina tsayawa a bakin ƙofar shiga gidan rawan kuma in yanke shawarar wanda zai shiga da wanda ba zai shiga ba. Gidan rawan yana ɗaukan mutane wajen 1,000 kuma hakan ya sa ni yin aiki gadan-gadan. Yin faɗa ya zama ruwan dare. An sha yi mani barazana da bindigogi da fasassun kwalabe. Wasu daga cikin waɗanda na hana shiga gidan rawan ko waɗanda na fid da waje sukan jira ni a waje don su ɗauki fansa. Shekaru na 20 a lokacin kuma ji nake babu wanda zai iya bugu na. Hakika, ni gagararre ne a lokacin, mamugunci, mai fahariya, dogon buri, ga rashin jin magana.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWANA: Babana bai taɓa fid da rai a kaina ba. Ya sa a riƙa aika mini mujallar Hasumiyar Tsaro da Awake!a a inda nake da zama. Sun taru a ɗakina ba tare da na karanta su ba. Wata rana, na yanke shawarar duba shafuffukan wasu daga cikinsu. Talifofin da na karanta a kan yadda tsarin siyasa, arziki, da addinai za su zo ƙarshe ya motsa ni in kira yaya ta. Ita da mijinta Shaidun Jehobah ne. Sun ce za su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni, kuma na amince da hakan.
Mizanin da ke Galatiyawa 6:7 ya motsa ni in yi canje-canje a rayuwata. Daga abubuwan da na gani a rayuwa, na san cewa duk wani abin da na yi, ko na ce, ko na yanke shawarar yi a yau zai shafi rayuwata gobe. Na samu ƙarfafawa daga gayyatar da ke Ishaya 1:18, wadda ta ce: “Mu zo yanzu, mu yi bincike tare, in ji Ubangiji: ko da zunubanku sun yi baƙi kamar mulufi, za su yi fari kamar kankara: ko da suna ja wur kamar garura, za su zama fari kamar auduga.” Tun daga lokacin da na soma nazari, wannan nassin ya taimaka mini in kawar da tunanin rashin cancanta ko kuma in ji cewa na riga na yi nisa.
Cikin watanni shida, na yi canje-canje masu yawan gaske a rayuwata amma hakan bai zo da sauƙi ba. Ina bukatar in ƙyale mugun yankin da nake zaune da kuma abokan banzan da na kewaye kaina da su. Na soma gaya wa abokaina cewa ina nazarin Littafi Mai Tsarki kuma na gaya musu abin da nake koya. Sai suka soma guduna suna kira na firist. Da taimakon yayata, na samu wani aikin yi mafi kyau.
Na soma halartan taro a Majami’ar Mulkin da yaya ta da mijinta suke halartan taro, duk da cewa yana da nisan mil 19 (kilomita 30). Akwai Majami’ar Mulki a kusa da gidana, amma ina jin tsoron haɗuwa da mutanen da suka san ni tun ina yaro. Ina kuma jin tsoron bi gida-gida ina wa’azi a wurin da nake zaune a dā. To, idan na haɗu da wani da na jefa waje daga gidan rawa kwanan nan fa, ko kuma wanda na sayar wa ƙwaya? Amma, na yi amfani da darasin da na koya daga horar da kaina da nake yi, wato, horar wa da suka fi wuya su ne mafi muhimmanci. Sa’ad da na cancanta, na soma wa’azi gadan-gadan.
Ina kuma da wani ƙalubalen da nake bukatar magancewa—ba na son yin karatu ko nazari. Amma na san cewa idan ina son in kasance da bangaskiya mai ƙarfi, ina bukatar in horar da kaina in yi nazari mai zurfi na gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Na fahimci cewa kamar ɗaga ƙarfe mai nauyi, mutum na bukatar ya ƙoƙarta sosai idan kana son ka samu ƙarfi.
YADDA NA AMFANA: Ina raye! Har yanzu ina mai da hankali sosai don kada in koma ga kasawana na dā. Amma ina more rayuwar iyali mai kyau da matata, wadda take da hali mai kyau na Kirista. A cikin Shaidun Jehobah, ina da abokan kirki waɗanda nike da cikakken tabbaci a cikinsu. Babana ya rasu shekaru biyar da suka shige, amma kafin rasuwarsa, ya shaida farin cikin marabtar ɗansa.
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.