Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .
Shaidun Jehobah suna yin mu’ujiyar warkarwa ne?
▪ Shaidun Jehobah ba su taɓa yin warkarwa ba. Kamar Yesu, sun gaskata cewa ainihin aikin su shi ne yin wa’azin bishara game da Mulkin Allah. Sun kuma gaskata cewa ana gane Kiristoci na gaskiya ne ta wajen wani abu mai muhimmanci sosai, ba ta hanyar warkarwa ba.
Gaskiyar ita ce, warkar da marasa lafiya a ƙarni na farko A.Z. da Yesu Kristi ya yi yana da muhimmanci sosai ga dukanmu. Ta hakan, ya tabbatar da cewa a ƙarƙashin sarautarsa a matsayin Sarkin Mulkin Allah, ba ‘wanda ya ke zaune a ciki da zai ce, Ina ciwo ba.’—Ishaya 33:24.
Yau kuma fa? Masu warkarwa a Kiristendom da wasu addinan da ba na Kirista ba suna da’awar cewa suna warkarwa ne ta hanyar mu’ujiza. Duk da haka, Yesu da kansa ya yi gargaɗi sosai a kan mutanen da za su yi da’awar cewa sun yi “ayuka dayawa masu-iko” da sunansa. Zai ce musu: “Ban taɓa saninku ba daɗai: rabu da ni, ku masu-aika mugunta.” (Matta 7:22, 23) Saboda haka, waɗannan mu’ujizai da masu warkarwa ta zamani suke da’awar yi suna nuna amincewar Allah ne ko albarkarsa?
Ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da warkarwar da Yesu ya yi. Ta wajen gwada wannan labarin da ke rubuce a cikin Nassi da kuma hanyoyin da masu warkarwa ta zamani suke amfani da ita, za mu iya sanin ko warkarwa na zamani ya fito ne daga Allah.
Yesu bai taɓa yin amfani da warkarwa don samun mabiya ko manyan taro ba. Akasin haka, ya yi warkarwa da dama ba tare da mutane sun sani ba. Sau da yawa ya gaya wa mutanen da ya warkar cewa kada su bayyana mu’ujizar ga kowa.—Luka 5:13, 14.
Yesu bai taɓa cewa a biya shi kuɗi domin mu’ujizan da ya yi ba. (Matta 10:8) Kuma yana yin nasara a dukan lokaci. Dukan marasa lafiya da suka je wurinsa sun warke daram, kuma warkarwar ba ta dangana a kan bangaskiyar mutumin ba. (Luka 6:19; Yohanna 5:5-9, 13) Kai, Yesu ya ta da matattu!—Luka 7:11-17; 8:40-56; Yohanna 11:38-44.
Ko da yake ya yi mu’ujizai, ainihin wa’azin da Yesu yake yi bai mai da hankali a kan tara mabiya ta hanyar aikin mu’ujiza ba. A maimakon hakan, ainihin aikinsa shi ne faɗin bisharar Mulkin Allah. Yesu ya shirya mabiyansa su zama masu almajirantarwa, waɗanda za su koyar da wasu game da begen samun kamiltacciyar lafiyar jiki a ƙarƙashin Mulkin Allah.—Matta 28:19, 20.
Hakika, wasu daga cikin mabiyan Yesu a ƙarni na farko suna da kyauta ta musamman na warkarwa, amma za su ƙare. (1 Korintiyawa 12:29, 30; 13:8, 13) Ana gane Kiristoci na gaskiya a yau ta wajen gamin ƙauna ta sadaukarwa da ke tsakaninsu, ba ta hanyar warkarwa ba. (Yohanna 13:35) Warkarwa ta zamani ba ta kafa iyalin Kiristoci na gaskiya ba daga dukan ƙasashe da ƙabilu, waɗanda irin wannan ƙaunar ta haɗa kansu.
Amma, akwai wani rukunin Kiristoci waɗanda gamin ƙaunar da ta haɗa su tana da ƙarfi sosai har suka ƙi su cuci junansu, ko kuma wani, har ma a lokacin da ake mugun faɗa. Su wane ne su? Shaidun Jehobah ne. A faɗin duniya, an san su da nuna irin ƙaunar Kristi. Haɗa kan mutane dabam-dabam, daga ƙasashe dabam-dabam, al’adu dabam-dabam, da kuma al’umma dabam-dabam mu’ujiza ce, kuma ruhu mai tsarki na Allah ne ya sa hakan ya yiwu. Kana iya halartan ɗaya daga cikin taronsu don gano wa idonka.
[Hoton da ke shafi na 27]
Masu warkarwa ta zamani (da aka nuna a dama) suna samun goyon baya daga Allah kuwa?