Ku Koyar Da Yaranku
Waɗanda Suka Rubuta Labarin Yesu
KUNA jin daɗin karanta labarin Yesu tare kuwa?—a Wasu mutane suna mamaki cewa Yesu bai rubuta komi ba a cikin Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, marubutan Littafi Mai Tsarki guda takwas sun gaya mana abubuwa masu yawa game da shi. Waɗannan mutanen sun yi rayuwa tare da Yesu, kuma sun gaya mana abin da ya koyar. Za ka iya faɗin sunayen su takwas ɗin kuwa?— Su ne Matta, Markus, Luka, da Yohanna. Sauran huɗun su ne Bitrus, Yaƙub, Yahuda, da Bulus. Menene ka sani game da waɗannan marubutan?—
Bari mu fara yin magana game da marubuta uku waɗanda suke cikin manzannin Yesu sha biyu. Ka san sunayensu kuwa?— Bitrus, Yohanna, da Matta. Bitrus ya rubuta wasiƙu biyu zuwa ga ’yan’uwansa Kiristoci. Ya gaya musu game da abubuwan da ya san cewa Yesu ya yi da kuma waɗanda ya faɗa. Ka buɗe Littafi Mai Tsarki zuwa 2 Bitrus 1:16-18, kuma ka karanta yadda Bitrus ya bayyana cewa ya ji Jehobah Allah yana yi wa Yesu magana daga Sama.—Matta 17:5.
Manzo Yohanna ya rubuta littattafai biyar na Littafi Mai Tsarki. Shi ne ke zaune kusa da Yesu a jibi na ƙarshe da manzannin suka ci tare da Ubangijinsu. Yohanna yana kuma tare da Yesu sa’ad da Ya mutu. (Yohanna 13:23-26; 19:26) Yohanna ya rubuta ɗaya daga cikin labarai huɗu a cikin Littafi Mai Tsarki game da rayuwar Yesu, wato Linjila. Ya kuma rubuta Ru’ya da Yesu ya ba shi da kuma wasiƙu uku da ke ɗauke da sunansa a cikin Littafi Mai Tsarki. (Ru’ya ta Yohanna 1:1) Marubucin Littafi Mai Tsarki na uku da ya zama manzon Yesu shi ne Matta. Shi mai karɓan haraji ne a dā.
Sauran marubutan biyu na Littafi Mai Tsarki sun san Yesu ne a wata muhimmiyar hanya. Mahaifiyarsu ɗaya ce, kuma ’ya’yan Yusufu da Maryamu ne su. (Matta 13:55) Sa’ad da Yesu ya soma wa’azi, su ba mabiyinsa ba ne. Sun yi zaton cewa ya ɗan haukace saboda ƙwazonsa na yin wa’azi. (Markus 3:21) Su wanene waɗannan ’yan’uwansa?— Yaƙub yana ɗaya daga cikinsu. Shi ne ya rubuta littafin Yaƙub a Littafi Mai Tsarki. Na biyun kuma Yahuda ne, wanda ake kuma kiransa Yahuza. Shi ya rubuta littafin Yahuda na Littafi Mai Tsarki.—Yahuda 1.
Wasu mutane biyu kuma da suka rubuta labarin Yesu su ne Markus da Luka. Mahaifiyar Markus, Maryamu, tana da babban gida a Urushalima, inda Kiristocin zamanin dā suke taro, har da manzo Bitrus. (Ayyukan Manzanni 12:11, 12) Shekaru da suka wuce, a daren da Yesu ya yi Idin Ƙetarewa na ƙarshe da manzanninsa, wataƙila Markus ya bi su sa’ad da suka je lambun Jathsaimani. Sa’ad da aka kama Yesu, sojoji suka riƙe Markus, amma ya gudu ya bar tufafinsa.—Markus 14:51, 52.
Luka likita ne mai ilimi sosai wanda wataƙila ya zama manzo bayan mutuwar Yesu. Ya yi nazari mai kyau game da rayuwar Yesu kuma ya rubuta labarin gaskiya kuma mai sauƙi game da shi. Daga baya, Luka ya zama abokin tafiyar manzo Bulus kuma ya rubuta littafin Ayyukan Manzanni da ke cikin Littafi Mai Tsarki.—Luka 1:1-3; Ayyukan Manzanni 1:1.
Bulus shi ne na takwas cikin marubutan Littafi Mai Tsarki da ya rubuta labarin Yesu. Ya yi karatu ƙarƙashin sanannen alƙali Gamaliel. Da yake Farisiyawa ne suka rene shi kuma suka koyar da shi, Bulus, wanda ake kira Shawulu a lokacin, ya ƙi jinin mabiyan Yesu kuma ya saka hannu wajen kashe su. (Ayyukan Manzanni 7:58–8:3; 22:1-5; 26:4, 5) Ka san yadda Bulus ya koyi gaskiya game da Yesu kuwa?—
Bulus yana kan hanyar zuwa Dimashƙa don ya kama almajiran Yesu, sai farat ɗaya hasken wuta da ya sauko daga sama ya makantar da shi. Ya ji murya tana ce masa: “Shawulu, Shawulu, don me ka ke tsanantata?” Yesu ne yake magana! Ya gaya wa Bulus ya shiga cikin Dimashƙa. Sai Yesu ya ja-goranci almajirinsa Hananiya ya yi wa Bulus magana, sai Bulus ya zama almajirin Yesu. (Ayyukan Manzanni 9:1-18) Bulus ya rubuta littattafai goma sha huɗu na Littafi Mai Tsarki, farawa daga Littafin Romawa zuwa Ibraniyawa.
Ka soma karanta littattafan Littafi Mai Tsarki da suke magana game da Yesu ko kuma ka sa wani ya karanta maka su?— Wani abu mafi muhimmanci da za ka taɓa yi a rayuwarka yanzu da kake ƙuruciya shi ne ka soma koyan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu.
[Hasiya]
a Idan kana karatun da yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.
TAMBAYOYI:
▪ Waɗanne manzannin Yesu ne suka zama marubutan Littafi Mai Tsarki?
▪ Waɗanne marubutan Littafi Mai Tsarki biyu ne ’yan’uwan Yesu?
▪ Me ya sa za a iya ce Markus ya san Yesu, amma Luka bai san shi ba?
▪ Ta yaya ne Bulus ya zama almajirin Yesu?
[Hotuna da ke shafi na 25]
Yahuda
Markus
Bitrus
Matta
Bulus
Yaƙub
Luka
Yohanna