Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/1 pp. 16-18
  • Majami’a—Wurin da Yesu da Almajiransa Suka Yi Wa’azi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Majami’a—Wurin da Yesu da Almajiransa Suka Yi Wa’azi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/1 pp. 16-18

Majami’a—Wurin da Yesu da Almajiransa Suka Yi Wa’azi

“Ya yi yawo cikin dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin bishara ta mulkin.”—MATTA 4:23.

SAU da yawa a cikin Linjila, mun karanta cewa Yesu ya shiga cikin majami’a. A Nazarat, garin da aka rene shi, ko kuma a Kafarnahum, birnin da ya zauna, ko kuma a dukan garurruka da ƙauyuka da ya ziyarta a cikin shekaru uku da rabi da ya yi yana hidimarsa tuƙuru, Yesu yakan zaɓi majami’a a matsayin wurin da zai yi wa’azi kuma ya koyar game da Mulkin Allah. Hakika, sa’ad da ya duba hidimar da ya riga ya yi, Yesu ya ce: “Kullum ina koyarwa cikin majami’u duk da haikali, wurin da Yahudawa duka su kan taru.”—Yohanna 18:20.

Hakazalika, manzannin Yesu da sauran Kiristoci na farko sukan taru kuma su koyar a majami’un Yahudawa. Ta yaya Yahudawa suka soma yin bauta a Majami’u? Kuma yaya waɗannan wuraren bauta suke a zamanin Yesu? Bari mu duba mu gani.

Muhimmiyar Abu a Rayuwar Yahudawa Sau uku a shekara, Yahudawa maza za su yi tafiya zuwa Urushalima don idodin da ake yi a haikali mai tsarki da ke wurin. Amma idan ya zo ga bautarsu ta yau da kullum, suna yin amfani da majami’ar da ke yankinsu, ko da suna zama ne a Falasɗinu ko a ɗaya daga cikin ƙasashen mallaka na Yahudawa da ba sa cikin ƙasar Falasɗinu.

A wane lokaci ne aka soma amfani da majami’a? Wasu sun gaskata cewa kusan lokacin da aka kai Yahudawa bauta a Babila ne (607-537 K.Z.), lokacin da aka halaka haikalin Jehobah. Ko kuma wataƙila an yin hakan ne ba da daɗewa ba bayan Yahudawa sun dawo daga bauta, sa’ad da Ezra firist ya umurci mutanensa su samu sani sosai game da Dokar Allah.—Ezra 7:10; 8:1-8; 10:3.

A asali, kalmar nan “majami’a” tana nufin “taro” ko “ikilisiya.” An yi amfani da ita a hakan a cikin Septuagint, wato, fassarar Helenanci na Nassosin Ibrananci. Da sannu-sannu, sai aka soma kiran ginin da mutane suke taruwa don bauta da wannan kalmar. A ƙarni na farko A.Z., kusan dukan garin da Yesu ya ziyarta suna da tasu majami’a; birane suna da wasu; Urushalima kuma tana da majami’u masu yawa. Yaya waɗannan gine-ginen suke?

Madaidaicin Gidan Bauta Sa’ad da suke son su gina majami’a, Yahudawa sukan nemi wuri mai tudu kuma su shirya ginin don ƙofar (1) ya kalli Urushalima. Kamar dai irin waɗannan fasalin ba su da wuya sosai, amma ba a cim ma hakan a yawancin lokaci.

Sa’ad da aka kammala ginin, majami’ar takan kasance madaidaiciya, kayan ɗakin kuma ba su da yawa. Wani abu na musamman shi ne akwati (2), ko ma’adana, inda ake ajiye abin da ya fi tamani a yankin, wato, littattafai na Nassosi Masu Tsarki. Sa’ad da ake yin taro, ana fito da akwatin, kuma a mai da shi cikin ma’adanar bayan an tashi taron (3).

Ana ajiye kujeru a gaba da ke fuskantar ikilisiyar a kusa da akwatin (4) domin shugabannin majami’ar da duk wasu manyan baƙi. (Matta 23:5, 6) Kusa da tsakiyar majami’ar akwai dakali da kuma inda za a ɗora littafi tare da kujeran zama don mai jawabi (5). A ɓangarori ukun da suke fuskantar dakalin akwai bencuna da ikilisiyar za ta zauna a kai (6).

Ikilisiyar da ke yankin ne take tallafa da kuma tafiyar da abin da ake yi a majami’ar. Ana yin amfani da gudummawar da masu arziki da talakawa suke ba da wa da son rai, wajen gyara ginin kuma ya kasance mai kyaun gani. Yaya tarurruka suke a majami’ar?

Bauta a Cikin Majami’ar Tsarin ayyuka na bauta a majami’ar ya ƙunshi yin waƙoƙin yabo, addu’a, karanta Nassosi, tare da koyarwa da kuma yin wa’azi. Ikilisiyar takan soma ne da maimaita Shema, wato, abin da ke kai ga furta bangaskiyar Yahudawa. An samo sunan nan ne daga kalma ta fari na nassi na farko da aka maimaita: “Ka ji fa [Shema], ya Isra’ila: Ubangiji Allahnmu Ubangiji ɗaya ne.”—Kubawar Shari’a 6:4.

Bayan haka, sai a karanta da kuma bayyana Attaura, wato littattafai biyar na farko na Littafi Mai Tsarki, waɗanda Musa ya rubuta. (Ayyukan Manzanni 15:21) Bayan haka, sai a sake yin wani karatu, ta wajen yin amfani da wasu ɓangarorin rubuce-rubucen annabawa (haftarahs) da kuma bayyana su da faɗin amfanin su. A wasu lokatai, baƙi masu jawabi ne suke yin wannan sashe na tsarin ayyuka, kamar yadda Yesu ya yi a yanayin da aka kwatanta a Luka 4:16-21.

Ko da yake, naɗaɗɗen littafin da aka miƙa wa Yesu a wannan taron ba shi da surori da ayoyi kamar yadda Littafinmu Mai Tsarki na zamani yake da shi. Saboda haka za mu iya zana a zuciyarmu yadda Yesu yake buɗe littafin da hannunsa na hagu kuma yana naɗa shi da hannunsa na dama har lokacin da ya ga wurin da yake nema. Bayan karatun, sai ya sake naɗa naɗaɗɗen littafin zuwa farko.

Sau da yawa, ana yin waɗannan karatun ne a ainihin yaren Ibraniyawa kuma ana fassara su zuwa Aramaic. Akan yi amfani da Septuagint a ikilisiyoyin Helenanci.

Yana da Muhimmanci ga Rayuwa na Yau da Kullum Abu mai muhimmanci a rayuwar Yahudawa na yau da kullum shi ne majami’ar, tare da sauran gine-gine da ke haɗe da ita, ko da ke cikin gidan, waɗanda ake amfani da su wajen yin abubuwa dabam-dabam. A wasu lokatai akan yi zaman shari’a a wurin, tare da tarurruka na yankin da manyan tarurrukan da za a ci abinci a wurin cin abinci da ke majami’ar. Akan saukar da baƙi a ɗakunan kwana da ke majami’ar.

A kusan dukan garurruka, majami’ar tana da makaranta, sau da yawa a cikin ginin. Za mu iya ƙaga a zuciyarmu ɗakin da ke cike da ƙananan ɗaliban da ke koyon karanta manya baƙaƙen da malami ya rubuta akan allon dunƙulin kaki. Irin waɗannan makarantu ne ya sa Yahuduwa na dā suke da ilimi, har talakawa ma sun san Nassosi.

Amma ainihin amfanin majami’ar ita ce, don a riƙa yin bauta a kullum. Ba abin mamaki ba ne ba cewa tarurrukan Kiristoci na ƙarni na farko ya yi kama sosai da tarurrukan Yahudawa a majami’a. A tarurrukan Kiristoci, manufar ɗaya ce, wato, bauta wa Jehobah ta hanyar addu’a, waƙoƙin yabo, da kuma karanta Kalmar Allah da tattauna ta. Kamannin bai ƙare a nan ba. Akan tallafa wa wuraren bautar nan biyu ta wajen ba da gudummawa da son rai, kuma karanta da tattauna Kalmar Allah ba hakkin limamai ba ne kawai; a waɗannan wuraren biyu, dattawa da suka manyanta ne suke tsara da kuma yin ja-gora a tarurrukan.

Shaidun Jehobah a yau suna yin koyi da tafarkin da Yesu da kuma mabiyansa na ƙarni na farko suka kafa. Saboda haka, tarurrukansu a Majami’ar Mulki yana da wasu fasaloli da suka yi kama da tarurrukan da ake yi a majami’u na dā. Fiye da haka, Shaidu suna taruwa ne da irin makasudin da masu ƙaunar gaskiya suke da shi tun da daɗewa, wato, su “kusaci Allah.”—Yaƙub 4:8, Littafi Mai Tsarki.

[Hoton da ke shafi na 16, 17]

An yi wannan ginin da aka sake ne bisa ga fasalin Majami’a na Gamla na ƙarni na farko

[Hoton da ke shafi na 18]

Ana koyar da yara maza masu shekaru 6 zuwa 13 a makarantar majami’ar

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba