Mutumin da Ya Canja Duniya
Biliyoyin mutane sun yi rayuwa kuma sun mutu a wannan duniyar. Yawancinsu ba su yi wani abin da zai sa a riƙa tunawa da su ba. Ƙalilan kuwa, sun yi tasiri a tarihi sosai, wataƙila har da rayuwarka ta yau da kullum.
KA TASHI tun da safe kuma ka yi shirin zuwa wajen aiki. Ka kunna wutan lantarki yayin da kake shiri. Ka ɗauki littafi ko jarida don ka karanta a cikin mota. Ka tuna ka ɗauki maganin da aka baka wanda ke taimaka maka wajen yaƙar wata cuta a jikinka. Ayyukanka a ranar sun riga sun soma kenan, kuma ka amfana daga tasirin wasu sanannun mutane.
Michael Faraday An haife shi a shekara ta 1791, wannan Bature manazarcin ƙarfin halittu ne ya ƙirƙiro na’urar wutan lantarki da dynamo. Binciken da ya yi da abubuwan da ya ƙirƙiro ya sa mutane suka samu ƙarin wutan lantarki.
Ts’ai Lun Babban ma’aikaci ne a daular ƙasar Sin, Ts’ai Lun ne aka ce ya ƙirƙiro yadda ake yin takarda, a wajen shekara ta 105 A.Z.
Johannes Gutenberg Wajen shekara ta 1450, wannan mutumin ɗan ƙasar Jamus ne ya ƙirƙiro na’aurar buga takardu na farko wadda ake juyawa da hannu. Wannan na’aurar ta sa buga takardu ta yi araha, kuma hakan ya sa mutane su samu bayani a ko’ina a kan batutuwa dabam-dabam.
Alexander Fleming A shekara ta 1928, wannan ɗan bincike ɗan ƙasar Scotland ne ya gano antibayotik, wato, wani maganin kashe ƙwayoyin cuta wanda ya sa wa suna penicillin. Ana yin amfani da antibayotik a dukan duniya wajen yaƙar ƙwayoyin cuta.
Babu shakka, abubuwan da wasu mutane ƙalilan suka gano kuma suka ƙirƙiro ya sa biliyoyin mutane su sami wasu gata ko su more cikakkiyar lafiya.
Amma, akwai wani mutumin da ya fita dabam daga sauran dukan mutane. Ba a san shi da gano wani abu game da kimiyya ba ko kuma magani. Maimakon haka, wannan mutumin da aka yi renonsa a cikin iyalin talaka kuma ya mutu wajen shekaru 2,000 da suka shige ya bar wani saƙo, wato, saƙo mai ƙarfi na bege da ta’aziyya. Idan aka duba yadda saƙonsa ya shafi rayukan mutane a dukan duniya, yawanci za su yarda cewa shi ne ainihin mutumin da ya canja duniya.
Yesu Kristi ne wannan mutumin. Wane saƙo ne ya yi wa’azinsa? Kuma ta yaya wannan saƙon zai iya shafan rayuwarka?