Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/15 p. 32
  • Ka Keɓe Lokaci Domin Nazarin Littafi Mai Tsarki Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Keɓe Lokaci Domin Nazarin Littafi Mai Tsarki Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Taimako ga Iyalai
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • “Ku Yi Shiri” A Matsayin Iyalan Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/15 p. 32

Ka Keɓe Lokaci Domin Nazarin Littafi Mai Tsarki Kuwa?

ASHEKARAR da ta shige, Hukumar Mulki ta sanar da cewa an yi gyara a tsarin taron ikilisiya don a samu ƙarin lokaci don nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma tattaunawa a matsayin iyali. Idan kai shugaban iyali ne, ka tabbata cewa kana gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali a kai a kai da zai amfani matarka da yaranka. Ma’aurata da ba su da yara za su yi amfani da wannan lokacin su yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare. ’Yan’uwa maza da mata marasa aure da ba su da hakkin iyali za su yi amfani da wannan lokacin da kyau don nazarin Littafi Mai Tsarki na kansu.

Mutane da yawa sun furta godiyarsu don wannan shiri na Bauta ta Iyali da yamma. Alal misali, Kevin, wani dattijo, ya rubuta: “Kalmomin nan ‘mun gode’ ba za su ishe mu mu nuna yadda mu da ke cikin ikilisiya muka ji ba. A matsayin dattawa, mun tattauna yadda muke amfani da yamma da babu taro mu yi ainihin yadda Hukumar Mulki ta ce mu yi, wato, mu yi nazari da iyalanmu.”

Jodi, wadda mijinta dattijo ne, ta rubuta: “Muna da yara mata uku, masu shekaru 15, 11, da kuma 2. Ba da daɗewa ba mun ƙaura zuwa wata ikilisiyar da ake yaren kurame. Yana ɗaukan lokaci da ƙoƙarce-ƙoƙarce sosai don mu shirya dukan taron. Yanzu, da wannan gyaran, muna da ƙarin yamma da za ta ba mu damar mai da hankali ga bauta ta iyali!”

John da JoAnn, ma’aurata da suke hidimar majagaba na kullum, sun rubuta: “Sau da yawa ba ma yin nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali a kai a kai domin muna haɗa shi da ayyukan ikilisiya dabam-dabam. Wannan sabon tsari kyauta ce daga Jehobah da ke wartsake mu a ruhaniya, idan muka yi amfani da lokacin yadda ya kamata mu yi.”

Tony, wani ɗan’uwa matashi da bai yi aure ba ya keɓe ranar Talata da yamma don ya yi nazari. Yana amfani da sauran lokatai cikin makon don ya shirya taron ikilisiya. Amma, Tony ya ce, “Ina ɗokin ranar Talata.” Me ya sa? “Wannan yamman, lokaci na ne na musamman da Jehobah.” Tony, ya bayyana: “A cikin kusan awa biyu, ina yin nazarin batutuwa da ke ƙarfafa dangantaka ta da Jehobah. Samun ƙarin lokaci don nazari na sa na yi bimbini a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki da na karanta.” Menene sakamakon? “Shawarar da Jehobah ya ba da tana shiga zuciyata sosai fiye da dā.” Yana da wani misali ne? “A cikin littafin nan Insight, na karanta game da abotar da ke tsakanin Dauda da Jonathan. Na koyi abubuwa da yawa daga halin Jonathan na rashin son kai. Misalinsa ya taimaka mini na ƙara fahimtar abin da kasancewa aboki na ƙwarai yake nufi. Ina ɗokin gano abubuwa da yawa masu tamani kamar haka a ranar Talata da yamma!”

Babu shakka, dukan bayin Jehobah za su amfana sosai ta wajen yin amfani sosai da ƙarin lokacin da suke da shi yanzu don yin nazarin Littafi Mai Tsarki mai ma’ana da kuma bauta ta iyali.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba