Ku Koyar Da Yaranku
Shem Ya ga Muguntar Zamanu Biyu
SHEM, ɗan Nuhu ya tsira daga zamani guda, kuma ya ci gaba da rayuwa a wani zamanin. Ka san abin da ya sa aka halaka zamani na farko da Shem yake ciki da kuma yadda shi da iyalinsa suka tsira zuwa zamani na biyu?—a Bari mu tattauna game da hakan.
Sa’ad da Shem yake matashi, Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa “muguntar mutum ta yi yawa.” Dukan abin da mutane suke tunani “mugunta ce kaɗai kullayaumi.” Ka san abin da Allah ya yi?— Ya sa ambaliyar ruwa ta halaka wannan mugun zamanin. Manzo Bitrus ya rubuta: “Duniya wanda take a sa’an nan, yayinda [ambaliyar ruwa] ya sha kanta, ta halaka.”—Farawa 6:5; 2 Bitrus 3:6.
Ka fahimci dalilin da ya sa Allah ya halaka wannan duniyar?— Mutanen mugaye ne, kuma sukan yi tunanin ‘mugunta kullayaumi.’ Yesu ya yi magana game da hakan. “A cikin kwanakin da ke gaban ruwan Rigyawa,” ya ce, mutane suna yin annashuwa “suna ci, suna sha” suna kuma “aure, suna auraswa.” Yesu ya daɗa: ‘Ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka.’—Matta 24:37-39.
Menene mutanen suka ƙi mai da wa hankali?— Mahaifin Shem, Nuhu, “mai-shelan adalci” ne, amma mutanen sun ƙi su saurari abin da yake cewa. Nuhu ya saurari Allah kuma ya gina jirgin ruwa, wanda zai ɗauki shi da iyalinsa har a gama Ambaliyar ruwan. Nuhu, da matarsa, yayansu—Shem, Ham, da Japheth—da matansu ne kaɗai suka mai da hankalinsu ga abin da Allah ya ke son su yi. Sauran sun yi abin da suke son su yi ne kawai, shi ya sa Ambaliyar ruwan ya halaka su.—2 Bitrus 2:5; 1 Bitrus 3:20.
Kusan shekara ɗaya da soma Ruwan, Shem da iyalinsa sun fito daga jirgin zuwa kan ƙasa busasshiya. Dukan miyagun mutane sun halaka, amma hakan ya canja ba da daɗewa ba. Ka’anan, yaron ɗan’uwan Shem, wato, Ham, ya yi wani mummunar abu da ta sa Nuhu ya ce: “Kan’ana shi zama la’antace.” Nimrod, jikan Ham, shi ma mugu ne. Ya yi tsayayya da Allah na gaskiya, Jehobah, kuma ya gaya wa mutane su gina hasumiya mai tsawo sosai mai suna Babel don su yi wa kansu suna. Ya kake ganin hakan zai sa Shem da babansa su ji?—Farawa 9:25; 10:6-10; 11:4, 5.
Sun yi baƙin ciki, Jehobah ma haka. Ka san abin da Jehobah ya yi?— Ya rikitar da harshensu hakan ya sa ba su fahimci junansu ba. Sai mutanen suka daina ginin suka tafi wurare dabam-dabam tare da waɗanda suke irin yarensu. (Farawa 11:6-9) Amma Allah bai canja yaren Shem da iyalinsa ba. Hakan ya sa sun kasance tare da junansu kuma sun taimaka wa junansu su bauta wa Allah. Ka san tsawon lokacin da Shem ya yi yana bauta wa Jehobah kuwa?—
Shem ya rayu har tsawon shekaru 600. Ya yi shekaru 98 kafin Ruwan kuma ya yi shekaru 502 bayan hakan. Muna da tabbaci cewa ya taimaka wa Nuhu wajen gina jirgin ruwan kuma ya yi wa mutane gargaɗi game da Ambaliyar ruwa da ke tafe. Amma menene kake ganin Shem ya yi a cikin waɗannan shekaru fiye da 500 da ya yi bayan Ambaliyar ruwan?— Nuhu ya kira Jehobah “Allah na Shem.” Babu shakka, Shem ya ci gaba da bauta wa Jehobah kuma ya taimaka wa iyalinsa su yi hakan. Daga baya, iyalin Shem sun haɗa da Ibrahim, Saratu, da Ishaƙu.—Farawa 9:26; 11:10-31; 21:1-3.
A yanzu, ka yi tunani game da duniya ta yau, wadda mugunta take ta ƙaruwa tun bayan zamanin Shem. Menene zai faru da ita?— Littafi Mai Tsarki ya ce tana “wucewa.” Amma ka lura da alkawarin nan: “Wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” Saboda haka, idan muka yi nufin Allah, muna iya kasancewa cikin waɗanda za su tsira zuwa cikin sabuwar duniya ta Allah. A lokacin, da taimakon Allah za mu iya rayuwa har abada cikin farin ciki a duniya!—1 Yohanna 2:17; Zabura 37:29; Ishaya 65:17.
[Hasiya]
a Idan kana karatun ne da yaro ko yarinya, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata kuma ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.
Tambayoyi:
○ A wane zamani ne Shem ya fara rayuwa a ciki, kuma don waɗanne dalilai biyu ne Allah ya halaka zamanin?
○ Shekaru nawa ne Shem ya yi, kuma wane irin mutumi ne shi?
○ Menene zai faru da duniyar nan ba da daɗewa ba?
○ Menene wajibi za mu yi don mu tsira daga ƙarshen zamanin nan?