Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 7/1 pp. 5-6
  • 2. Ka Karanta Shi Da Zuciya Ɗaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 2. Ka Karanta Shi Da Zuciya Ɗaya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Ka ƙaru wajen Samun Cikakken Sani Da “Yardar Rai Sarai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Kiristoci Ku Nuna Ɗaukakar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ka Amfana Sosai Daga Karatun Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ka Bi Tafarkin Sarakuna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 7/1 pp. 5-6

Yadda Za Ka Fahimci Littafi Mai Tsarki

2. Ka Karanta Shi Da Zuciya Ɗaya

Abokinka ya taɓa gaya maka wani abu marar kyau game da wani da ba ka taɓa gani ba? Amma sa’ad da ka sadu da wannan mutumin, abin da abokinka ya gaya maka ya hana ka ganin halayensa da baiwarsa masu kyau? Irin wannan abu zai iya faruwa idan ya zo ga batun Littafi Mai Tsarki.

MANZO Bulus ya yi gargaɗi game da abin da zai iya faruwa idan muka ƙi karanta Littafi Mai Tsarki da zuciya ɗaya. Game da wasu Yahudawa na zamaninsa, Bulus ya rubuta: “Ina shaidassu suna da himma domin Allah, amma ba bisa ga sani ba.”—Romawa 10:2.

Wasu daga cikin waɗannan Yahudawa na ƙarni na farko sun ƙi amincewa da gaskiyar da Nassosin Ibraniyawa ya bayyana dalla-dalla, wato, bayyanuwar Almasihu. Yesu ɗan Nazarat ya yi daidai da duk kwatancin da aka yi a Nassosi kuma ya cika dukan annabcin da aka yi game da shi. Duk da haka, ra’ayin da yawancin Yahudawan suke da shi tun da daɗewa ne ya hana su su fahimci Kalmar Allah.

Menene za mu iya koya daga wannan labarin? Yana da muhimmanci mu karanta Littafi Mai Tsarki da zuciya ɗaya. Nuna bambanci ko kuma ra’ayi marar kyau zai iya hana mai karatu ya fahimci gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Alal misali, wani farfesa na karatun addini a Arewancin Carolina, a Amirka, ya bayyana cewa Littafi Mai Tsarki “littafin da ’yan adam suka wallafa ne, da ya ƙunshi tunanin ’yan adam, wanda yawancin littattafan sun bambanta da juna kuma babu wani daga cikinsu da ya ba da tabbatacciyar shawara game da yadda za a yi rayuwa.” Idan mutum ya ɗauki Littafi Mai Tsarki a matsayin “littafin da ’yan adam suka wallafa,” zai yi watsi da ƙa’idodin da ba ya so, ko ba haka ba?

Akasin haka, Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafamu mu yi nazarinsa sosai. Game da Biriyawa a zamanin Bulus, Nassosi ya ce: ‘Sun karɓi magana da yardar rai sarai, suna bin cikin littattafai kowace rana, su gani ko waɗannan al’amura haka suke.’ (Ayyukan Manzanni 17:11) Kamar Biriyawa, wataƙila kana bukatan ka kawar da duk wani ra’ayi marar kyau ko nuna bambanci da kake da shi game da Littafi Mai Tsarki. Ka karanta Kalmar Allah da zuciya ɗaya, don ka fahimci saƙo mai ban sha’awa na Mawallafin.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba