Ku Koyar Da Yaranku
Ɗanɗan ’Yar’uwar Bulus—Ya Ceci Kawunsa
KA SAN cewa manzo Bulus yana da dangi da mabiyan Yesu ne?a— Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa ’yar’uwarsa da ɗanta mabiyan Yesu ne. Kuma ɗanɗan ’yar’uwarsa ɗin ne ya ceci ransa! Ba mu san sunansa ko na mahaifiyarsa ba, amma mun san abin da ya yi. Za ka so ka ji labarin?—
Bulus ya dawo kenan daga tafiyarsa ta uku ta wa’azi a ƙasashen waje kuma yana Urushalima. Ga alama, wajen shekara ta 56 A.Z. An kama Bulus kuma za a yi masa shari’a. Amma maƙiyan Bulus ba sa son a yi masa shari’a. Suna son ya mutu! Saboda haka, suka sa maza arba’in su ɓoye a hanya don su kashe Bulus.
Sai ɗanɗan ’yar’uwar Bulus ya ji wannan shirin da suke yi. Ka san abin da ya yi?— Ya tafi wajen Bulus ya gaya masa. Nan da nan, Bulus ya gaya wa wani soja: “Ka tafi da wannan sarmayi wurin sarkin yaƙi: gama yana da wani abin da za ya faɗa masa.” Sojan kuwa ya kai shi wajen sarkin yaƙi, Kuludiyas Lisiyas, kuma ya bayyana masa cewa wannan saurayin yana da wani bayani mai muhimmanci. Kuludiyas ya kira ɗanɗan ’yar’uwar Bulus gefe ɗaya, kuma ya gaya masa dukan abin da ke faruwa.
Sai Kuludiyas ya gargaɗe ɗanɗan ’yar’uwar Bulus cewa: “Kada ka faɗa ma kowane mutum ka shaida mani wannan magana.” Sai ya kira manyan sojoji guda biyu ya gaya musu su shirya mayaƙa guda ɗari biyu, barade saba’in, da masu mashi ɗari biyu kuma su yi shirin zuwa Kaisariya. Da ƙarfe tara na daren, mayaƙa guda ɗari huɗu da saba’in suka kai Bulus wurin Sarkin Roma, Filikus, a Kaisariya. A wasiƙar da ya aika wa Filikus, Kuludiyas ya gaya masa game da shirin da aka yi na kashe Bulus.
Hakan ya tilasta wa Yahudawa su je su sami Bulus a kotun shari’a a Kaisariya don su gabatar da zarginsu. Amma dai, ba su da shaidar da ta nuna cewa Bulus ya aikata abin da bai da kyau. Duk da haka, an ɗaure Bulus a kurkuku babu hujja har tsawon shekara biyu. Saboda haka, ya ɗaukaka ƙararsa zuwa ƙasar Roma, sai suka aika shi wurin.—Ayyukan Manzanni 23:16–24:27; 25:8-12.
Menene za mu iya koya daga wannan labarin na ɗanɗan ’yar’uwar Bulus?— Muna bukatar gaba gaɗi don mu faɗi gaskiya kuma idan mun yi hakan, za mu iya ceto rayuka. Har a lokacin da Yesu ya san cewa maƙiyinsa “suna nema su kashe shi,” ya ci gaba da gaya wa mutane game da Mulkin Allah. Yesu ya gaya mana mu yi hakan. Za mu yi hakan? Ƙwarai kuwa idan muna da gaba gaɗi kamar ɗanɗan ’yar’uwar Bulus.—Yohanna 7:1; 15:13; Matta 24:14; 28:18-20.
Bulus ya aririci amininsa Timothawus: “Ka maida hankali da kanka, da kuma koyarwarka. Ka lizima cikin waɗannan; gama garin yin wannan za ka ceci kanka duk da masu-jinka.” (1 Timothawus 4:16) Babu shakka, ɗanɗan ’yar’uwar Bulus ya yi amfani da irin wannan ƙarfafawar daga kawunsa. Za ka yi haka?
[Hasiya]
a Idan kana karanta wa yara, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata, ka yi musu tambayar.
Tambayoyi:
○ Su wanene wasu cikin dangin Bulus, kuma menene muka koya game da su?
○ Menene ɗanɗan ’yar’uwar Bulus ya yi don ya ceci ran Bulus?
○ Menene za mu iya yi, don yin biyayya ga Yesu, da zai iya ceto rayukan mutane a yau?