Wasiƙa Daga Ghana
Ranar da Ya Ƙi Faɗan Karate
BAI yi kama da yadda na yi tsammanin ganinsa ba. Ya yafa dogon tufafi fari, a ɗaure baƙin bel mai faɗin inci biyu a ƙugunsa ya yi balas, ya ƙarfafa hannuwansa yana shirin duka, ƙafafunsa suna ware. Ya haɗa fuskarsa, yana mai da hankali. Idanunsa sun koma ciki, babu alamar tausayi a cikinsu da zai nuna raunana.
Nan da nan, sai ya matsa ya yi ihu. “Yat!’ Ya miƙa hannunsa ya yi naushi. Nan da nan sai katako ya karye ya faɗi a ƙasa. Ya juya kuma, ya yi tsalle sosai, ƙafafunsa da hannunsa suka juya tare don su kai naushi ga abokin faɗa. Da gaske wannan mutumin ne ya ce yana so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi?
Na miƙa hannu mu gaisa da shi. “Kai ne Kojo. Na ji cewa kana son a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai.” Ya riƙe hannuna ya yi murmushi, fuskarsa a sake da kuma fara’a. Fuskarsa ba abin ban tsoro ba ne kamar dā, kuma ya nuna marmari ƙwarai. Ya ce: “E, ina so sosai” yaushe za mu soma”?
Muka zauna a kan dakalin gidan da Littafi Mai Tsarkinmu da littafin da za mu yi nazari. Wajen yana da sanyi-sanyi, kuma ba surutu. Mu uku ne kawai a wajen: Da ni da Kojo da kuma ɗan birinsa. Ɗan birin yana da tsawon inci 14, yana da jar gashi a kansa, da kuma farin gemu, hakan ya sa yana da ban dariya. Yana da kyau, yana da yawan son wasa, yana zuwa duk inda ya ga dama, yana taka littattafanmu, yana kwace bironmu, yana kuma saka ’yan hannayensa a aljihun rigarmu ko zai sami abin ci. Kamar iyaye da suka saɓa da surutu da shiga da fita da ƙananan yara suke yi, Kojo ya rabu da birin ya mai da hankali ga nazarin. Tambayoyin da yawa da yake yi ya nuna mini cewa yana tunani, kuma yana son ya fahimta. Wataƙila karate ya koya masa ya mai da hankali sosai, saboda ba ya amincewa da kome sai ya ga tabbaci daga Nassosi.
Nazarinmu ya ci gaba sosai. Amma, sai na lura da wata faɗa da yake faruwa a cikin zuciyarsa. “Abin da nake so ƙwarai a wannan duniya shi ne karate” Ya gaya mini. Na lura na ga cewa yana son faɗa sosai, abin da ya koya har ya ƙware. A cikin shekara 26 a duniya, ba kawai yana son karate ba amma ya ƙware a cikinsa sosai, har ya kai matsayin mai baƙin bel, matsayin da mutane kalilan ne suka samu ko kuma za su taɓa samu.
Ban san abin da Kojo zai so ya yi ba. Na lura cewa ya fahimci cewa wanda yake yin karate, ji wa mutane rauni, ba zai jitu da halayen Kirista kamar su juyayi, ƙauna da kuma kula da mutane ba. Duk da haka, na san cewa gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta canja halayen mutane da suka fi shi taurin zuciya. Idan Kojo yana da zuciyar kirki, a hankali zai yi canji, domin ƙarfin ikon Kalmar Allah. Dole ne in jimre.
Wata rana kafin mu gama nazarinmu, sai muka karanta wata sura a cikin Littafi Mai Tsarki da ta girgiza Kojo kamar naushi mai ƙarfi daga abokin faɗa. “Ubangiji yana gwada mai-adalci: amma mai-mugunta da mai-son zalunci ransa yana ƙinsu,” ya karanta. (Zabura 11:5) Duk “Mai-mugunta,” ya sake faɗa a hankali. Nan da nan sai ya yi sanyi. Ya kalle ne sai ya yi murmushi. “Na tsai da shawara.”
Yanzu da ni da Kojo muna yin aikin da muka fi so, wato, mun ba da kanmu don muna koyar da waɗanda suke son su saurari umurni daga Littafi Mai Tsarki. Yau da safe mun shirya za mu ziyarci wani matashi mai suna Luke.
A hanyar zuwa gidansu, mun bi wata matsatsiyar hanya ta kasuwa da ke cike da mutane. Akwai shaguna da yawa kuma masu talla sun jera kayan sayarwa a kan titi, kamar su kayan miya, kuɓewa da kuma rediyo, laima, sandunan sabulu, gashin doki, abubuwan da ake dahuwa da su, da kuma gwanjon takalma da kayan sawa. ’Yan mata sun aza abinci mai ƙamshi a cikin babban kwano a kansu. Suna ƙoƙari su wuce tsakanin taron mutane, suna ja wa masu jin yunwa rai da miyarsu masu ƙamshi da aka yi da gasashen kifi, ƙaguwa da kuma dodon koɗi. Karnuka, awakai, da kuma kazuna suna yawo. Karan rediyo, motoci da kuma maganganu mutane sun sa kasuwa ta cika da surutu.
Muka bi hanyar ta fice daga wajen nan mai yawan surutu na gari muka isa wani gida mai ɗauke da wata alama da ta ɗan gogu: “Inda masu dogon tafiya suke tsayawa.” Luke wani ɗan matashi mai shekara 20 zuwa 25 ya tsaya a bakin ƙofa sai ya kira mu ciki muka shiga inuwa. Fadarsa tana cike da buhunan da akwatunan saiwa da ganye da aka ɗaura da igiya, da kuma bawon itatuwa duka na innar Luke ce, wadda take ba da maganin gargajiya. Tana haɗa magungunan ta bisa ga ilimi da ta gada, musamman ma idan aka daka kuma aka niƙa, ana ba da tabbati cewa zai warkar da kowane irin cuta. Luke yana jiranmu. Ya share dattin gefe ɗaya, kuma ya aje mana kujeran zama guda uku. Mun zauna kusa da juna, sai muka soma nazarinmu na Littafi Mai Tsarki.
Kojo ne yake nazarin da Luke. Ina zaune ina sauraron matasan guda biyu suna tattauna daga cikin Littafi Mai Tsarki abin da ya sa akwai wahala sosai a duniya. Sa’ad da Kojo ya miƙa hannusa ya taimaki Luke ya buɗe Littafi Mai Tsarki, ina kallon yadda hannunsa mai ƙarfi yake buɗe nassosi a hankali. Sai na tuna. Ba da daɗewa ba, da waɗannan hannayen yake yin faɗa. Ikon Kalmar Allah ta cire mugayen halaye da suka zama gama gari a wannan duniya marar dabi’a kuma suka mai da su zuwa masu juyayi da ƙauna. Wannan abin da aka cim ma mai muhimmanci ne.
A hanyarmu zuwa gida, mu ga wani mutum yana zaune a ƙarƙashin itacen mangwaro. Ya saurari kallo da kyau sa’ad da ya buɗe Littafi Mai Tsarki kuma ya karanta. Sa’ad da mutumin ya fahimci cewa mu Shaidun Jehobah ne, sai ya tashi tsaye. “Ba na ƙaunarku!” ya furta cikin fushi. Nan da nan sai Kojo ya hau zuciya. Sai na ga ya huce kuma ya bar wajen. Muka yi tafiyarmu.
Da muke tafiya sai Kojo ya matsa kusa da ni ya raɗa: “Zuciya ta ta tashi sa’ad da a faɗi waɗannan maganganu. Da ka sani abin da zai yi wa mutumin nan?” “Na sani” ya ce da murmushi. Shi ma ya yi murmushi muka ci gaba da tafiyarmu.