Nassosin Yini Don Shekara Ta 2008
Watan Nuwamba
1. Macijin kuwa ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriya tata.—R. Yoh. 12:17. w-HA 7/1/07 4:17, 18
2. Sa’anda waɗannan al’amura sun soma faruwa, ku duba bisa, ku tada kanku; gama fansarku ta kusa.—Luk 21:28. w-HA 10/1/06 5:20, 21
3. Ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji kuma; za ya kuwa biya maka muradin zuciyarka.—Zab. 37:4. w-HA 6/1/07 4:20
4. Kada ku kamantu bisa ga kamar wannan zamani kuma: amma ku juyu bisa ga sabontar azancinku, da za ku gwada ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.—Rom. 12:2. w-HA 6/1/07 2:16, 17
5. Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai; domin cigabanka ya bayyanu ga kowa.—1 Tim. 4:15. w-HA 5/1/07 5:12, 13
6. Cikin bangaskiyarku kuma ku kawo . . . haƙuri.—2 Bit. 1:5, 6. w-HA 8/1/07 3:1-4
7. Ku sansance waɗannan da ke . . . shugabannai ne a gareku cikin Ubangiji, suna kuma faronku.—1 Tas. 5:12. w-HA 4/1/07 4:10-14
8. Ku yi ƙyamar abin da ke mugu; ku lizimci abin da ke nagari.—Rom. 12:9. w-HA 7/1/07 3:8, 9
9. Ta wurinsa fa [Yesu] bari mu miƙa hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi, watau, ’ya’yan leɓunan da su ke shaida sunansa.—Ibran. 13:15. w-HA 5/1/07 1:18, 19
10. Kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.—1 Kor. 11:3. w-HA 3/1/07 2:8, 9
11. Ka fita daga ƙasarka, daga danginka kuma, da gidan ubanka, zuwa ƙasa da zan nuna maka.—Far. 12:1. w-HA 6/1/07 4:5, 6
12. Mala’iku kuma waɗanda ba su riƙe matsayi nasu ba, amma suka rabu da nasu wurin zama, ya tsare su cikin madawaman sarƙoƙi a cikin dufu zuwa hukuncin babbar ranar.—Yahu. 6. w-HA 4/1/07 2:4-6
13. ’Yan’uwa, ko an iske mutum a cikin kowane laifi, ku da ku ke masu-ruhaniya, cikin ruhun tawali’u ku komo da irin wannan; kana lura da kanka, kada ya zama kai kuma ka jarabtu.—Gal. 6:1. w-HA 8/1/07 2:21, 22
14. Shaidar Ubangiji tabbataciya ce, tana sa marar-sani ya zama mai-hikima.—Zab. 19:7. w-HA 5/1/07 3:17, 18
15. Kada ku ji tsoro . . . , ku tuna da Ubangiji, wanda shi ke mai-girma, mai-ban razana.—Neh. 4:14. w-HA 7/1/07 4:9
16. Ina misalin darajar tunaninka zuwa gareni, ya Allah! Ina misalin yawan jimlassu!—Zab. 139:17. w-HA 7/1/07 1:12, 13
17. Fa ne shi, aikinsa cikakke ne.—K. Sha 32:4. w-HA 6/1/07 1:10-12
18. Ka kiyaye kwatancin sahihiyan kalmomi waɗanda ka ji daga gareni.—2 Tim. 1:13. w-HA 6/1/07 3:9
19. Dole bishop shi kasance . . . mai-gāran bāƙi, mai-son nagarta, mai-hankali, mai-adalci, mai-tsarki, mai-kamewa.—Tit. 1:7, 8. w-HA 8/1/07 5:23, 24
20. Idan ku fa da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?—Luk 11:13. w-HA 1/1/07 2:10-13
21. Suka fāɗa ma wuyan Bulus, suna sumbatasa, yawancin baƙinzuciya da su ke yi domin . . . ba za su ƙara ganin fuskatasa ba.—A. M. 20:37, 38. w-HA 10/1/06 4:9, 10
22. Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.—Lev. 19:18. w-HA 12/1/06 4:8-10
23. Waɗanda su ke biɗan Ubangiji ba za su rasa kowane abu mai-kyau ba.—Zab. 34:10. w-HA 3/1/06 5:4, 5
24. Idan maƙiyinka yana jin yunwa, ka cishe shi; idan yana ƙishi, ka ba shi sha; gama garin yin haka, za ka tara masa garwashin wuta a kansa.—Rom. 12:20. w-HA 7/1/07 3:16-18
25. Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah; sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa.—Zab. 19:1. w-HA 7/1/07 1:18, 19
26. Ubangiji Allahnka za ya albarkace ka . . . za ka fa cika da murna sarai.—K. Sha 16:15. w-HA 8/1/07 2:9, 10
27. Tun kana jariri fa ka san littattafai masu-tsarki.—2 Tim. 3:15. w-HA 5/1/07 5:3-5
28. Dukan waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.—2 Tim. 3:12. w-HA 2/1/07 2:8, 9
29. Ku tuba, ku juyo wajen Allah, ku yi ayyuka waɗanda sun cancanta tubarku.—A. M. 26:20. w-HA 12/1/06 2:9-11
30. Mai-albarka ne mutum wanda ya ke dogara ga Ubangiji, wanda Ubangiji ne begensa.—Irm. 17:7. w-HA 10/1/06 5:17-19