Nassosin Yini Don Shekara Ta 2008
Watan Oktoba
1. Dukan abin da mutum yake da shi, ya bayar a bakin ransa.—Ayu. 2:4. w-HA 6/1/07 2: 14, 15
2. Ku mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta; hakanan ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu.—Afis. 5:25, 28. w-HA 5/1/07 4: 6, 7
3. Ikilisiyar Allah mai-rai ke nan, jigon gaskiya da ƙarfinta.—1 Tim. 3:15. w-HA 5/1/07 2: 17, 18
4. Na cikin ƙasa mai-kyau, su ne waɗanda sun ji magana cikin zuciya mai-gaskiya mai-kyau, daga baya su kan riƙe ta, da haƙuri kuma suna bada amfani.—Luka 8:15. w-HA 2/1/07 2: 4, 5
5. Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa: Gama babu rashi ga masu-tsoronsa.—Zab. 34:9. w-HA 3/1/07 5: 1, 3
6. Kowane zunubi ko saɓo za a gafarta ma mutane su; amma saɓon da a ke yi a kan Ruhun ba za a yi gafarassa ba.—Mat. 12:31. w-HA 8/1/07 1: 2, 3
7. Biyayya ta fi hadaya.—1 Sam. 15:22. w-HA 7/1/07 2: 3-5
8. Ka tuna da kwanakin dā, Ka lura da shekarun tsara zuwa tsara; Ka tambayi ubanka, ya kuwa gwada maka; Manyanka kuma, su a faɗa maka.—K. Sha 32:7. w-HA 6/1/07 4: 18
9. Kada rana ta faɗi kuna kan fushinku.—Afis. 4:26. w-HA 5/1/07 4: 17, 18
10. Ya ɓāta [Sanballat da Tobiah] zuciya ƙwarai, da shi ke [Nehemiya] ya zo mai-biɗan lafiyar ’ya’yan Isra’ila.—Neh. 2:10. w-HA 7/1/07 4: 3, 4
11. Wataƙila a ɓoye ku a cikin ranar fushin Ubangiji.—Zeph. 2:3. w-HA 4/1/07 1: 17-19
12. Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne . . . ga kwaɓewa.—2 Tim. 3:16. w-HA 6/1/07 1: 8, 9
13. Kowane ɗaya am ba da bayanuwar Ruhu garin amfani.—1 Kor. 12:7. w-HA 5/1/07 1: 15, 16
14. Ku da ke yara, ku yi biyayya da dattiɓai.—1 Bit. 5:5. w-HA 4/1/07 4: 7-9
15. Mace wadda ta ke da miji a ɗaure ta ke ga mijin bisa ga shari’a.—Rom. 7:2. w-HA 3/1/07 2: 5-7
16. Ina gode maka, ya Uba, . . . da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.—Luka 10:21. w-HA 2/1/07 4: 4, 5
17. Za mu zauna har abada tare da Ubangiji.—1 Tas. 4:17. w-HA 1/1/07 5: 4, 5
18. Ku tāda idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.—Yoh. 4:35. w-HA 5/1/07 3: 14, 15
19. Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.—A. M. 5:29. w-HA 7/1/07 2: 18, 19
20. Magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.—1 Bit. 5:8. w-HA 1/1/07 2: 9, 10
21. A bada wannan irin mutum ga Shaiɗan garin a hallaka jiki, domin ruhu shi tsira.—1 Kor. 5:5. w-HA 12/1/06 2: 4-6
22. In kawo su wurin dutsena mai-tsarki, in faranta zuciyassu a cikin gidana na addu’a.—Isha. 56:7. w-HA 11/1/06 4: 1, 4
23. Macijin kuwa ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriya tata.—R. Yoh. 12:17. w-HA 10/1/06 4: 11, 12
24. Wannan abin karɓa ne, idan sabili da lamiri zuwa ga Allah mutum ya jimre baƙinzuciya, yana shan zalunci.—1 Bit. 2:19. w-HA 7/1/07 4: 8
25. Ya mai-jin addu’a, a gareka dukan masu-rai za su zo.—Zab. 65:2. w-HA 8/1/07 3: 16, 17
26. Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu.—Ibran. 10:24, 25. w-HA 6/1/07 3: 5, 6
27. Wa ke yin, Wai yo? . . . Wa ke da jajjayen idanu? Sai waɗanda su kan daɗe wurin shan ruwan anab.—Mis. 23:29, 30. w-HA 11/1/06 2: 4, 5
28. Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa.—Mis. 4:23. w-HA 10/1/06 2: 4, 6
29. Yanayina ba a ɓoye ya ke a gareka ba, Sa’anda aka yi ni a fakaice, Sa’anda aka sifanta ni da gwaninta daga cikin zurfafan duniya.—Zab. 139:15. w-HA 7/1/07 1: 5, 7, 8
30. Fuskatasa, sai ka ce fuskar malaika.—A. M. 6:15. w-HA 8/1/07 3: 18-20
31. Na cika umurnin Ubangiji.—1 Sam. 15:13. w-HA 7/1/07 2: 9, 10