Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/1 pp. 3-4
  • Wa Zai Iya Sanin Abin da Zai Faru a Nan Gaba?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wa Zai Iya Sanin Abin da Zai Faru a Nan Gaba?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Akwai Wanda Zai Iya Sanin Gobe?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Annabci Game da Almasihu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/1 pp. 3-4

Wa Zai Iya Sanin Abin da Zai Faru a Nan Gaba?

“Gama ni ne Allah. . . , mai-bayana ƙarshe tun daga mafarin, tun zamanin dā kuma al’amuran da ba a rigaya a aika ba tukuna.”—Ishaya 46:9, 10.

AWAƊANNAN kwanaki marasa kan gado, masana siyasa da tattalin arziki da kuma zaman jama’a sun bincika tarihi da kuma yanayin da muke ciki a yau don su iya faɗin abin da zai faru a nan gaba. Wasu da suke marmarin sanin abin da za su fuskanta a nan gaba suna duba taurari ko sihiri domin su sami amsoshi. Sau da yawa irin waɗannan mutanen sun yi baƙin ciki saboda amsoshin da suka samu. Zai yiwu kuwa mu san abin da zai faru ga wannan duniyar, iyalanmu da kuma mu kanmu? Shin akwai wanda zai iya faɗin abin da zai faru kuwa a nan gaba?

A kalmominsa ga annabi Ishaya da aka yi ƙauli a baya, Maɗaukaki Allah, Jehobah, ya bayyana kwarewarsa na annabta abin da zai faru a nan gaba. Ta bakin Ishaya, Allah ya annabta cewa za a saki Isra’ila ta dā daga bauta a Babila kuma za su koma Urushalima su gina haikali. Wannan annabci ya cika a kan lokaci kuwa? Kusan shekara 200 kafin lokacin, Ishaya ya ambata sunan wanda zai ci Babila a yaƙi, wato, Cyrus. Bugu da ƙari, Ishaya ya kwatanta dabarar da Cyrus zai yi, wato zai kawar da kogin Yufiretis, wanda ke kāre birnin. Ya annabta cewa Cyrus zai sami an bar manyan ƙofofin birnin a buɗe cikin sakaci, hakan kuma zai taimake shi ya ci nasara cikin sauƙi.—Ishaya 44:24–45:7

Idan aka gwada shi da Allah, mutum ba shi da iko ya hangi gaba. Sarki mai hikima Sulemanu ya rubuta: “Kada ka yi ma kanka alwashin gobe: Gama ba ka san abin da kwana ɗaya za ya kawo ba.” (Misalai 27:1) Har ila, waɗannan kalmomin gaskiya ne. Babu ɗan adam da zai iya sanin abin da zai faru da shi a nan gaba. Amma, me ya sa Allah ya bambanta? Yana sane da dukan abubuwan da ya halitta har da halin mutum da muradinsa. Yayin da ya zaɓi ya yi hakan, Allah yana iya ganin abin da kowane mutum da al’ummai za su aikata. Ƙari ga haka, yana da iko ya daidaita sakamakon abubuwa. Sa’ad da ya annabta ta bakin annabawansa cewa wani abu zai faru, sai ya zama Wanda yake “ƙarfafa maganar bawansa, yana tabbatadda shawarar manzanninsa.” (Ishaya 44:26) Jehobah Allah ne kawai zai iya faɗin haka.

Ishaya ya rayu fiye da shekara 700 kafin Yesu, Almasihu. Duk da hakan, Ishaya ya annabta game da zuwan Almasihu. Musamman daga ƙarni na 18 zuwa kasa, ’yan sūka sun musanta gaskiyar Littafin Ishaya. Suna da’awar cewa annabcin Ishaya bai faɗi abin da zai faru a gaba ba amma an yi rubutun bayan abubuwan sun faru ne, daga baya wani marubuci ya rubuta abubuwan da suka riga sun faru. Hakan gaskiya ce kuwa? A shekara ta 1947 an sami kofi na Littafin Ishaya da wasu naɗaɗɗun littattafai na dā a wani kogo a kusa da Tekun Gishiri. Masana sun tabbata cewa an rubuta wannan kofin fiye da shekara ɗari kafin haihuwar Almasihu ko Kristi da aka annabta. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da zai faru a nan gaba!

Ishaya da sauran marubutan Littafi Mai Tsarki ba su annabta abubuwan da suka faru a gaba bisa ga hikimarsu kawai ba. Akasin haka, sun “yi magana daga wurin Allah, Ruhu Mai-tsarki ne yana motsa su.” (2 Bitrus 1:21) A talifi na gaba za mu mai da hankali a kan wasu abubuwa game da rayuwar Yesu da aka annabta ta bakin Ishaya. Sannan za mu yi la’akari da wasu abubuwa da Yesu da almajiransa suka annabta game da zamaninmu da kuma abin da zai faru a nan gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba