Nassosin Yini Don Shekara Ta 2008
Watan Satumba
1. A cikin yawan wusuwasi da ke cikina ta’aziyyanka suna ji ma raina daɗi.—Zab. 94:19. w-HA 8/1/07 3: 12-14
2. Ku miƙa jikunanku hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karɓa ga Allah, bautarku mai-ruhaniya ke nan. . . . ku gwada ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.—Rom. 12:1, 2. w-HA 7/1/07 3: 3-5
3. Waɗanda an dasa cikin gidan Ubangiji za su yi yabanya cikin harabun Allahnmu. Za su yi ta ’ya’ya da tsufa a kai.—Zab. 92:13, 14. w-HA 6/1/07 3: 2, 3
4. Ga ɗanki, yana da rai.—1 Sar. 17:23. w-HA 6/1/07 3: 2, 3
5. Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, . . . matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.—Afis. 5:22, 33. w-HA 5/1/07 4: 13-15
6. Mala’ikan Ubangiji yana kafa sansani a kewaye da masu-tsoronsa, yana tseradda su kuma.—Zab. 34:7. w-HA 3/1/07 4: 16, 17
7. Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.—Mat. 28:19, 20. w-HA 2/1/07 2: 1-3
8. Mutane dayawa a cikin almajiran [Yesu] suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba.—Yoh. 6:66. w-HA 5/1/07 2: 14-16
9. Ya bada kyautai ga mutane.—Afis. 4:8. w-HA 4/1/07 4: 5, 6
10. Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji.—Afis. 5:22. w-HA 3/1/07 5: 1-3
11. Ubangiji, ka koya mana yin addu’a.—Luka 11:1. w-HA 1/1/07 3: 3-5
12. Ina misalin darajar tunaninka zuwa gareni, ya Allah! Ina misalin yawan jimlassu!—Zab. 139:17. w-HA 2/1/07 4: 2, 3
13. Ubangiji yana binciken dukan zukata, ya kuma gāne dukan siffofin tunani.—1 Laba. 28:9. w-HA 6/1/07 3: 16, 17
14. Bayarwa ta fi karɓa albarka.—A. M. 20:35. w-HA 5/1/07 5: 20, 21
15. Ka zauna da farinciki tare da mace wadda ka ke ƙaunatta.—M. Wa. 9:9. w-HA 10/1/06 2: 9, 10
16. Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.—Mat. 22:39. w-HA 12/1/06 4: 1-3
17. Kada ka rena koyaswar Ubangiji: Kada ka yi kasala kuma da tsautawassa: Gama wanda Ubangiji ya ke ƙauna shi ya ke tsauta ma.—Mis. 3:11, 12. w-HA 12/1/06 2: 1, 2
18. Ko kuna ci fa, ko kuna sha, ko kuwa iyakar abin da ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah.—1 Kor. 10:31. w-HA 11/1/06 2: 3, 4
19. Idan fa idonka sosai ne, dukan jikinka za ya zama da haske.—Mat. 6:22. w-HA 10/1/06 5: 15, 16
20. Yana da bishara ta har abada wadda za ya yi shelarta ga mazaunan duniya.—R. Yoh. 14:6. w-HA 4/1/07 3: 15, 16
21. Maganarka fitila ce ga sawayena, haske ne kuma a tafarkina.—Zab. 119:105. w-HA 5/1/07 3: 11
22. Matattu ba su san komi ba.—M. Wa. 9:5. w-HA 1/1/07 4: 1-3
23. Da kai da Yahudawa kuna da nufin tayaswa.—Neh. 6:6. w-HA 7/1/07 3: 14
24. [Yesu] ya ƙanƙantadda kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa, i, har mutuwa ta giciye.—Filib. 2:8. w-HA 7/1/07 2: 16, 17
25. Mu da kanmu muna fahariya domin ku cikin ikilisiyai na Allah.—2 Tas. 1:4. w-HA 5/1/07 1: 13, 14
26. Ku fito da ’ya’ya fa masu-isa tuba.—Luka 3:8. w-HA 8/1/07 1: 18, 19
27. Addu’ar mai-adalci tana da iko dayawa cikin aikinta.—Yaƙ. 5:16. w-HA 6/1/07 4: 14, 15
28. Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.—1 Yoh. 5:19. w-HA 6/1/07 1: 8
29. Ƙauna ta Allah ce . . . Wanda ba ya yin ƙauna ba, ba ya san Allah ba; gama Allah ƙauna ne.—1 Yoh. 4:7, 8. w-HA 10/1/06 4: 4, 5
30. Suka jejjefe Istifanus, yana kira, yana cewa, Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna. Ya durƙusa ya tada murya da ƙarfi, Ubangiji, kada ka lissafta wannan zunubi a garesu.—A. M. 7:59, 60. w-HA 7/1/07 4: 11