Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 9/15 p. 32
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Yin Magana A Harsuna Dabam-dabam Ya Fito Ne Daga Wurin Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 9/15 p. 32

Tambayoyi Daga Masu Karatu

A wasiƙarsa ga Ibraniyawa, manzo Bulus ya yi maganar “ɗibiyar hannuwa.” Yana nufin naɗa dattawa ne ko kuma wani abu dabam?—Ibran. 6:2.

Bulus yana nufin ɗibiya hannuwa don a ba da kyautar ruhu.

Littafi Mai Tsarki ya yi maganar ɗibiya hannuwa sa’ad da ake naɗi na tsarin Allah. Musa ya ‘ɗibiya hannuwansa’ a kan Joshua sa’ad da ya naɗa shi ya zama magajinsa. (K. Sha 34:9) A ikilisiyar Kirista a dā, ana ɗibiya hannuwa a kan wasu maza sa’ad da ake son a naɗa su. (A. M. 6:6; 1 Tim. 4:14) Bulus ya ce kada a yi garaje wajen ɗora wa mutum hannu.—1 Tim. 5:22.

Amma, Bulus ya gargaɗi Kiristoci Ibraniyawa su ‘ci gaba har zuwa kammala’ tun da sun bar ‘ka’idodin farko.’ Sai ya lissafa “tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah, da kuma na koyarwa kan wanke-wanke, da ɗora hannu.” (Ibran. 6:1, 2; LMT) Ya kamata naɗa dattawa ya zama abu na farko ne da Kiristoci za su ci gaba da biɗa? A’a. Zama dattijo na ikilisiya makasudi ne da ya kamata kowane ɗan’uwa ya biɗa kuma ya daraja shi.—1 Tim. 3:1.

Amma ɗora hannuwa yana da wata manufa. A ƙarni na farko, Jehobah ya ƙi Isra’ila ta jiki a matsayin mutanensa ya ɗauki Isra’ila ta ruhaniya, wato, ikilisiyar shafaffu na Kirista kuma ya ba ta albarkarsa. (Mat. 21:43; A. M. 15:14; Gal. 6:16) Kyautar ruhu ta mu’ujiza kamar magana a harsuna ya ba da tabbacin wannan canji. (1 Kor. 12:4-11) Sa’ad da Karniliyus da iyalinsa suka zama masu bi, waɗannan sababbin sun yi “magana da harsuna” hakan ya nuna cewa sun sami ruhu mai tsarki.—A. M. 10:44-46.

Wani lokaci, ana ba da kyautar mu’ujiza ta wajen ɗora wa mutum hannu a kai. Sa’ad da Fillibi ya yi wa’azin bishara a Samariya, mutane da yawa sun yi baftisma. Hukumar mulki ta aiki manzo Bitrus da Yohanna zuwa wajen. Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’annan [waɗannan biyu] suka ɗibiya masu hannuwa, suka karɓi Ruhu Mai-tsarki.” Wannan yana nufin cewa sun samu kyautar ruhu, kuma mutane sun ga hakan ya faru. Mun san hakan domin Simon, wanda a dā yana ayyukan sihiri ya ga yadda ruhun yake aiki kuma ya yi ƙoƙari ya sayi ikon ɗora hannunsa a kan mutane su sami ruhu mai tsarki kuma su sami ikon yin mu’ujiza. (A. M. 8:5-20) Daga baya an yi wa mutane 12 baftisma a Afisa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’anda Bulus ya ɗibiya masu hannuwansa, Ruhu Mai-tsarki ya abko masu; suka yi magana da harsuna, suka yi annabci.”—A. M. 19:6; gwada da 2 Tim. 1:6.

Saboda haka, a Ibraniyawa 6:2 Bulus yana maganar ɗora hannu don ya idar da kyautar ruhu ga masu bi sababbi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba