Nassosin Yini Don Shekara Ta 2008
Watan Agusta
1. Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku cikin Ubangiji.—Afisawa 6:1. w-HA 3/1/07 13, 14, 16a
2. Ba ku da iko ku bauta ma Allah da mammon ba.—Matta 6:24. w-HA 5/1/07 17-19d
3. Ya mai-jin addu’a, a gareka dukan masu-rai za su zo.—Zabura 65:2. w-HA 12/1/06 18, 19b
4. Ka yi haƙuri . . . ka jimre sabili da sunana, ba ka gaji ba.—Ru’ya ta Yohanna 2:3. w-HA 2/1/07 17, 18c
5. Kada ku bada sanadin tuntuɓe, ko ga Yahudawa, ko ga Helenawa, ko ga ikilisiya ta Allah.—1 Korinthiyawa 10:32. w-HA 5/1/07 11a
6. Ina roƙonku misalin saukakku, baƙi masu-tafiya kuma, ku hanu daga sha’awoyi na jiki.—1 Bitrus 2:11. w-HA 1/1/07 16, 17b
7. Kuna lizima cikin addu’a.—Romawa 12:12. w-HA 1/1/07 17-19a
8. Na yi muku kwatanci.—Yohanna 13:15. w-HA 3/1/07 19, 20a
9. Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.—Kolossiyawa 4:6. w-HA 6/1/07 4, 5a
10. Ku ne shaiduna, in ji Ubangiji, barana kuma wanda na zaɓa.—Ishaya 43:10. w-HA 11/1/06 14b
11. Kowanne mutum ya jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko.—Yaƙub 1:14. w-HA 12/1/06 21, 22a
12. Ku mazaje, ku yi ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.—Kolossiyawa 3:19. w-HA 5/1/07 10, 11c
13. Ba wanda ya ke da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, mutum shi bada ransa domin abokansa.—Yohanna 15:13. w-HA 10/1/06 2, 3c
14. Da hanƙuri na yi sauraro ga Ubangiji; Ya kuwa karkata kunne gareni, ya ji kukata.—Zabura 40:1. w-HA 1/1/07 1, 2a
15. Kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.—1 Korinthiyawa 11:3. w-HA 10/1/06 19, 20a
16. Bangaskiya, in ba ta da ayuka ba, mataciya ce cikin kanta.—Yaƙub 2:17. w-HA 11/1/07 1, 2a
17. Ubangiji, ka dubi kashedinsu: ka ba bayinka kuma su faɗi maganarka da ƙarfinzuciya duka.—Ayukan Manzanni 4:29. w-HA 9/1/06 16, 17b
18. Ubangiji ya tsare ni in yi ma ubangijina wannan abu, shafaffe na Ubangiji.—1 Samuila 24:6. w-HA 8/1/06 5-7c
19. Kada ku yi karkiya marar-dacewa tare da marasa-bangaskiya.—2 Korinthiyawa 6:14. w-HA 5/1/07 9, 10b
20. Wanda ya ke maida kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi.—1 Korinthiyawa 10:12. w-HA 10/1/06 7, 8a
21. Ina ɗan wanda ubansa ba ya yi masa horo ba?—Ibraniyawa 12:7. w-HA 3/1/07 17-19a
22. Sai ta wurin wahala dayawa za mu shiga mulkin Allah.—Ayukan Manzanni 14:22. w-HA 10/1/06 7, 8c
23. Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.—Misalai 27:11. w-HA 9/1/06 5, 6a
24. Ba shi kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da bangaskiya: gama mai-zuwa wurin Allah sai shi bada gaskiya akwai shi, kuma shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.—Ibraniyawa 11:6. w-HA 9/1/06 1, 2c
25. Ku bari jimrewarku ta sanu ga dukan mutane. Ubangiji ya kusa.—Filibbiyawa 4:5. w-HA 11/1/06 4, 6a
26. Ƙaunatattu, muna da waɗannan alkawarai, bari mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazamtar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.—2 Korinthiyawa 7:1. w-HA 11/1/06 17-19b
27. Mai-albarka ne mutum wanda Ubangiji ba ya lissafta mugunta gareshi ba.—Zabura 32:2. w-HA 12/1/07 7, 8a
28. Baƙon da ke sabke a wurinku za ya zama maku kamar ɗan da aka haifa a wurinku, za ka ƙaunace shi kamar kanka.—Leviticus 19:34. w-HA 12/1/06 4-6b
29. Don me za ka jarabtu da karuwa, ya ɗana.—Misalai 5:20. w-HA 10/1/06 2, 3a
30. Amma dukan wanda ya saurara gareni za ya zauna lafiya, za ya zauna da rai a kwance, ba tsoron masifa ba.—Misalai 1:33. w-HA 10/1/06 13, 14d
31. Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu; ku yi tafiya cikin ƙauna, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunace ku, ya bada kansa kuma domin ku, abin miƙawa da hadaya ga Allah domin shesheƙi na ƙamshi mai-daɗi.—Afisawa 5:1, 2. w-HA 7/1/07 15a