Ka Kusaci Allah
Da Akwai Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”?
WANENE tsakanin mu baya bukatar ƙauna? Hakika, muna ci gaba sa’ad da ’yan’uwa da abokai suna gwada mana ƙauna. Abin baƙin ciki, dangantakar ’yan adam tana da aras kuma ba ta da tabbaci. Waɗanda muke ƙauna suna iya ɓata mana rai, su yi watsi da mu, ko kuwa su ƙi mu. Duk da haka, da akwai wani wanda ƙaunarsa ba ta kasawa. An kwatanta ƙaunar da Jehobah Allah yake yi wa bayinsa da kyau a Romawa 8:38, 39.
“Na kawas da shakka,” in ji manzo Bulus. Shakkar me? Da abin da zai iya “raba mu da kamnar Allah.” Bulus ya yi wannan furci ba don kansa kaɗai ba amma domin “mu” wato, dukan mutane da suke bauta wa Allah cikin aminci. Domin ya nanata abin da yake nufi, Bulus ya jera abubuwa masu yawa da ba za su iya hana bayin Jehobah amintattu su more ƙaunarsa ba.
“Ba mutuwa, ba rai.” Ƙaunar Jehobah ga bayinsa ba ta ƙarewa yayin da suka mutu. Domin ya tabbatar da ƙaunarsa, Allah yana tunawa da su, kuma zai tada su daga matattu a sabuwar duniya ta adalci mai zuwa. (Yohanna 5:28, 29; Ruya ta Yohanna 21:3, 4) A yanzu dai, ƙaunar Allah ga bayinsa masu aminci ba ta ƙarewa ko da me za su fuskanta a wannan duniyar.
“Ba malaiku, ba sarautai.” Mutane masu iko da kuma hukumomi suna iya rinjayar ’yan adam amma ba haka yake ga Jehobah ba. Halittu na ruhu masu ƙarfi kamar mala’ika wanda ya zama Shaiɗan ba zai iya sa Allah ya daina ƙaunar bayinsa ba. (Ru’ya ta Yohanna 12:10) Gwamnatoci ma da suke yin hamayya da kiristoci na gaskiya ba za su iya canja ra’ayin Allah game da bayinsa ba.— 1Korinthiyawa 4:13.
“Ba al’amuran yanzu, ba al’amuran na zuwa.” Ƙaunar Allah bata ƙarewa da shigewar lokaci. Babu abin da bayinsa za su fuskanta yanzu ko kuma a nan gaba da zai sa Allah ya daina ƙaunarsu.
“Ba ikoki.” Bulus ya ambaci runduna ta sama da ta duniya wato, “malaiku” da “gwamnatoci” amma yanzu ya ambaci “ikoki.” Kalmar Hellenanci da aka yi amfani da ita a nan tana da ma’ana dabam dabam. Ko da mecece ainihin ma’anarta, mun tabbata da cewa: Babu wani iko a sama ko ƙasa da ya isa ya hana Jehobah ƙaunar bayinsa.
“Ba tsawo, ba zurfi.” Jehobah yana ƙaunar bayinsa ko yaya yanayinsu.
“Ba kuwa wani halittacen abu.” Da waɗannan kalmomi, Bulus yana faɗi ne da tabbaci cewa babu wani abin da ya isa ya raba bayin Jehobah amintattu daga ƙaunar da yake masu.
Ko da shike ƙaunar ’Yan adam tana koɗewa amma ƙaunar Allah ga waɗanda suka dogara da shi cikin bangaskiya ba ta fasawa; tana kasancewa har abada. Sanin haka yana sa mu mu kusaci Jehobah kuma mu yi iyaka ƙoƙarinmu mu tabbatar masa cewa muna ƙaunarsa.