Yadda Aka Magance Wata Matsala
MATASA uku a Afirka ta Tsakiya suna so su je taron gunduma a ƙasarsu. Yaya za su isa wajen? Wajen kusan mil 60 ne kuma hanyar ba ta da kyau, kuma ba su da kuɗin mota. Sun tsai da shawara su ari kekuna uku, amma ba su samu masu kyau ba.
Wani dattijo a ikilisiyarsu ya ga matsalar da suke ciki sai ya ba su tsohon kekensa mai aiki da kyau. Ya gaya musu irin shirin da shi da wasu suke yi a dā don su halarci taron gunduma. Dattijon ya shawarce su su yi amfani da keke guda. Shawara ce mai kyau amma tana bukatar shiri mai kyau. Ta yaya hakan zai yiwu?
Don su guje wa zafin rana, ’yan’uwan suka haɗu da sassafe suka shirya kayansu a bisa keken. Na farkon ya tuka keken, sauran suka taka da kafa. Bayan mil ɗaya, mai tukin ya tsaya kuma ya jingina keken a wata itace. Babu shakka, ya ajiye keken a inda ’yan’uwa biyun za su iya gani don kada a “sace.” Sai wanda ya fara tuka keken ya ci gaba da tafiya da kafa.
Idan ’yan’uwa biyun suka kai wajen keken, ɗaya daga cikin su zai tuka sai sauran su ci gaba da tafiya na kusan mil ɗaya kafin wani ya hau. Da shiri mai kyau da kuma nacewa, matasa ukun suka rage tafiyarsu daga mil 60 zuwa kusan mil 40. Kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Sun haɗu da ’yan’uwansu Kiristoci a taron gunduma kuma suka more abinci na ruhaniya. (K. Sha 31:12) Wannan shekara, za ka yi iya ƙoƙarinka ka halarci taron gunduma a ƙasarka?